part 33-34

809 71 0
                                    

NI DA AMINIYYA TAH
(Ja'adah da Sameerah)
*2019*

NA MARYAM S INDABAWA
MANS

HAJOW
HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S

Facebook @Maryam Sulaiman
Facebook group Indabawa Hausa Novel.
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSIndabawa

*Dedicated to my Bestie*
*Hauwa Kamilu Zimit (Ameerah)*
*Mrs Bashir*

*Bismillahi Rahamanir Rahim*

Thursday
17/January/2019
33-34

Sai bayan tayi magariba tai isha'i sannan ta fito. Mamah ta sama a falo. Karasawa tayi ta ce,
"Mamah sannu da hutawa!"

"Yauwah Ja'ada, me kike a dakin ne?"
"Ba komai!"

"To ya kukai da Yaron da yazo."
Shiru, Ja'ada tayi sannan ta ce,
"Wai sona yake!"

"Mene na sa Wai din, son ki yake, me kika ce masa?"
"Ba komai ya amshi number ne kawai."

"Ja'ada ki hakura da Jawad din nan!"
Abbah da ke shigowa ya ce,
"Akan me?"

"Abbah yanzu ina taga Jawad shekara kusan bakwai shida fa, a ina zata ga Jawad!"
Zama Abbah yayi sannan ya ce,
"A'ah Baki san kaddarar Allah ba in Allah yayi Ja'ada matar Jawad ce duk shekarun da zasu basa tare sai kiga sun hadu nan gaba anyi aure, dan haka kina mata addu'a kawai. Amman dai Ja'ada in kin samu wanda ya kwanta miki ki saurare shi. Mutum baya auren matar wani kinji."

Kai ta gyada ta ce,
"Sannu da zuwa Abbah!"

"Yauwah ya school din?"
"Alhamdulilah Abbah sauran sati uku mu fara final exam wallahi abu duk sun min yawa ga project din nan."

"Ai kina kokari ma. Allah ya bada sa'a!"
"Ameen Abbah!"

Sun jima suna hira sannan suka ci abinci kkowa yai dakin sa. A daki Ja'ada duk ta shiga damuwa tana zaune Izzedeen ya kira wayar.

Ganin sabuwar number yasa ta ki dauka. Haka akai ta kira daga baya ma ta kashe wayar.

Izzedeen da duk ya kasa komai dan ba karamin so ne ya shige shi ba na Ja'adatu ranar ko bacci bai ba.

Washe gari da safe Mamin sa na ganin sa ta rude,
"Son lafiyar ka?"

Kai ya gyada mata kawai ya hhau dining. Duk yadda yake son cin abinci dan abinda yake so Mami ta dafa masa amman ya kasa ci.

Falo ya koma suna gamawa Mami da Dady suka rufa masa baya. Dukkan su a gaba suka saka shi suna tambayar me ke damun sa amman yai shiru daga baya sai ya saka musu kuka.

Take hankalin su ya kuma tashi. Sai da ya sha kukan sa ya ce,
"Mami ban taba zaton akwai abinda zan nema na rasa a duniya ba."

Mami ta ce,
"Ai son babu abun nan."

Kai ya girgiza ya ce,
"Mami ki daina fadar haka dan yanzu na tabbata akwai abin. Mamai duk kyau na kudi na mulki na amman Mami yau ni naje gun yarinya ta ki karbar soyayya ta daga baya ma wayar ta, ta kashe wanda hakan ba karamin tashin hankali ga rayuwa ta bane! Mami jiya ko bacci ban yi ba. duk na rasa nutsuwa ta."

Mikewa yayi. Mami tankamo shi ta ce,
"Ina zaka?"

"Jigawa zan tafi Mami jigawa zani bazan iya jure rashin ganin ta ko jin muryar ta ba."
"Inna lillahi wainna illahir rajiun!"
Mami ta fada tana dafa kai.

Dad ne yai gyaran murya ya ce,
"Zo nan my son!"

Matsawa yayi gun Dad. Dad ya ce,
"Yanzu ka tabbata ba komai mutun ke samu a duniya ba. Mahaifiyar ka ta daura ka akan duk abinda kake so zaka sama. to ka sani ba komai ne kudi ke siya ba. Abu daya zan fada maka shine ka dage da addu'a kawai. In Allah yayi Yarinyar matar ka ce zata zama rabon ka in kuwa ba matar ka bace zaka iya mutuwa in kace zaka kawo mata cikas a al amarin ta kabi komai a hanalkali."

Ni da Aminiyya tah (Ja'adatu da Sameerah)Tempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang