*NI DA AMINIYYA TAH*
_(Ja'adah da Sameerah)_
*2019*NA *MARYAM S INDABAWA*
*MANS**HAJOW*
*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S**_(We Educate, Entertain Enlightenment and Exhortation our readers)_*
Facebook @Maryam Sulaiman
Facebook group Indabawa Hausa Novel.
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSIndabawa*Dedicated to my Bestie*
*Hauwa Kamilu Zimit (Ameerah)*
*Mrs Bashir**Bismillahi Rahamanir Rahim*
Thursday
25/April/2019135-136
Tin da tayi arbain suke zuba ido da kunne na ganin ta dawo ko ace a zo a dauke ta amman shiru.
Momy kuwa shirya ta tayi ta ce, taje gidan Momy tayi sati daya in ta dawo akai ta jigawa tayi sati biyu kan ta dawo.
Ai kam haka taje gidan Momy tayi sati daya nan ma taga kulawa da gata daga Momy har Dady daga nan kuma ta koma gida.
Washe gari aka daga da ita jigawa. Da kaya masu uban yawa da Momy ta bayar akai.
Acan ma gata ta samu sosai daga ita har Babyn ta ba abinda take daga bacci sai ci ko wankan Baby yi mata ake a gyara mata daki.Hutu sosai ya zauna a jikin ta inda acan kano kuma da Jawad yaje yaji ta tafi jigawa zuciya yayi ya bar gidan ma dan tin da taje gidan Momy yake rokar da ta dawo ta dawo dakin ta Amman Momy shine zata tura jigawa in ta dawo tafi abuja kuma wai wata daya zatai wallahi shi baya son haka.
Haka ya fita yana ta kumbure kumbure momy ta ce,
"Kai tayi sai ta huta wallahi. So kake ta dawo kai ta takura ta. Yarinya mai hakuri nasan tana hakuri da kai wallahi."Sunyi waya da shi ya ce mata ta dawo a cikin satin, bata so ba dan satin ta biyu da zuwa bayan har garin iyayen ta suka so suje a ganta. Dole su Mamah suka ce ta tafi in ta dawo sa je ita ma taga dagin mahaifan nata. Haka suka hada mata kaya masu yawa da su da na su Sameerah da su Sirikan nata.
Momy bata tsamanin ganin ta ba sai jin tayi ana shigo da kayan ta. Kallon ta ta tsaya yi tana shigowa hannun ta dauke da Baby Jawahir da ta kara girma.
Mikewa tayi ta amshi babyn tana fadin
"Ya kuka dawo?"Zama Ja'ada tayi ta ce,
"Wallahi Momy mun same ku lafiya!""Lafiya lou! Ya hanya da su Mamahn taku!"
"Suna lafiya duk suna gaishe ku!"Kallon ta tayi ta ce,
"Ince Jawad ne ya dawo dake ko?"Kai ta girgiza,
"Ki fadan gaskiya shi yace ku dawo ko?""A'ah Momy!"
"Ai shikenan tashi kije ki yi wanka ki sauko kici abinci!"Ta mike tayi sama wanka tayi ta shirya ta saka wasu kayan sanna ta sauko ta hau cin abinci.
Momy ta sama zaune tai wa Baby Jawahir Wanka sai bacci take a hannun ta. Sai da ta gama cin abincin sannan ta saka aka shigo wa da su Momy kayan tsarabar su. Nono ne da kwan zabi da kaji haka ta aika da nasu Momy da nasu gida.
Jawad yana gida aka aika da kayan ya ji dadi dan yasan Ja'ada ta dawo kenan yana son zuwa to amman yasan in yaje zai samu fadan Momy shiyasa ya zauna dan yanzu ta hannun Dady zai bi.
Sai da ya barta tayi kwana biyu bai ga dawowar ta ba sannan yaje har office ya samu Dady. Bayan sun gaisa ne Jawad ya ce,
"Dady ni dai Momy ta rike min mata wajen wata biyu taki ta bar ta, ta dawo gidan ta,"
YOU ARE READING
Ni da Aminiyya tah (Ja'adatu da Sameerah)
FantasyLabari akan aamintaka wacce ta ke fauke da soyayya tare da sadaukar wa tsakanin amninan biyu. Muhammad Jawad (Yaron littafin) Ja'adatu (Yarinyar littafin) Saneerah (Aminiyar Ja'adat) ku shigo ciki kuji me ke akwai wacce irin sadaukar wa haka Aka yi...