*NI DA AMINIYYA TAH*
_(Ja'adah da Sameerah)_
*2019*NA *MARYAM S INDABAWA*
*MANS**HAJOW*
*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S**_(We Educate, Entertain Enlightenment and Exhortation our readers)_*
Facebook @Maryam Sulaiman
Facebook group Indabawa Hausa Novel.
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSIndabawa*Dedicated to my Bestie*
*Hauwa Kamilu Zimit (Ameerah)*
*Mrs Bashir**Bismillahi Rahamanir Rahim*
Saturday
14/April/2019
109-110Bangaren Izeedeen akan wannan al amarin sam bai wani zafi sosai ba. Dan shi yasan son da yakewa Ja'ada har da na jini da suka hada shiyasa.
Farin cikin sa daya da ya bawa Ja'ada abinda take so wato Jawad dan haka ya amshi auren Nusiaba hannu bibiyu da cusa son ta tinda daman can Nusaiba bata da makusa ko daya.
Itama kyakyawa ce ga hankali nutsuwa da girmama na gaba. Dan haka ya yadda ya aminta ya amshi auren Nusaiba dari bisa dari kuma zai bata duk wata kulawa da ya dace ya bata tare da hakkin auren su.
Ga Nusaiba ma abin ma haka yake dan farin cikin ta daya itama ta sadaukar da farin cikin ta na ganin ta auri izeedeen tasan yanzu burin wadan nan masoyan zai cika.
Kuma ta samu nasiha daga bakin Abbah sosai da Momyn ta. Dan haka ta fawalawa Allah komai. Da yake Nusaiba sun saba da Izeedeen kuma daman Nusaiba akwai saurin sabo da shiga rai wannan yasa nan da nan suka dinke abinsu.
In kaga suna waya kace wasu masoya ne wanda suka dade suna soyayya. A lokaci kadan ya mika mata dukkan soyayyar sa haka nan ita ma.
Jiya suka iso garin kano a jiyan yana gun ta haka ma yanzu da dare yana gun ta dan a jibi washe garon ranar walima zasu tafi da ita a kai ta can gidan Izeedeen.
Taso yau taje gun Anty Ja'ada dan ta kara kwantar mata da hankali amman sam Izeedeen tin rana da yazo har dare yana gidan yana cika ta da barkwancin sa da kalaman soyayyar sa.masu dadi. Tini duk ta fara jin sha'awar ka sancewa da shi, duk da bai nuna mata wani abu ba sun dai zauna akan three sitter tare. Wannan yasa bata samu dama ba gashi a gobe ba lokaci.
Komai da zasu saka iri daya akai musu Ja'ada da Nusaiba da Sameerah amman Sameerah ta ce wallahi baza ta saka ba.
Suma mazajen iri daya sukayi komai.
Washe gari in kaga gidan sai kace irin daurin auren nan ne dan tin safe har an taro ana ta sha'anin biki. Karfe biyu kuwa kowa ya shirya sai amare da ake karasa shirya su.
Amaren sunyi kyau ciki wani dark blue din atamfa suka yafa manyan mayafai farare haka nan takalman su da jakunna suma farare.
Mazajen sun saka Farar shadda suka saka wacce akai mata ado da blue din zare. Sosai sukai kyau. Sai da kowa ya tafi aka zo daukar Amare tare da angwayen ssu. Mota biyu ce daya ta Izeedeen yana ciki dayar kuma Jawad.
Nusaiba ita ta fara shiga motar, Izeedeen na ganin ta ya kafe ta da ido ko matsawa ya kasa dan yadda tayi kyau ba magana.
Murmushi ta sakar masa ya janyo hannun ta ta dan fada jikin sa. Wata ajiyar zuciya ya sauke yana mai zagayawa da hannun sa ta kugunta ya kara janyonta jikin sa.
"Daga jiya da dare zuwa yanzu baki ji yadda nake kewar ki ba!"
Murmushi kawai tayi."I miss u so much my wife!"
"Miss u too husby!"
![](https://img.wattpad.com/cover/172818435-288-k228203.jpg)
DU LIEST GERADE
Ni da Aminiyya tah (Ja'adatu da Sameerah)
FantasyLabari akan aamintaka wacce ta ke fauke da soyayya tare da sadaukar wa tsakanin amninan biyu. Muhammad Jawad (Yaron littafin) Ja'adatu (Yarinyar littafin) Saneerah (Aminiyar Ja'adat) ku shigo ciki kuji me ke akwai wacce irin sadaukar wa haka Aka yi...