137-138 END

1.1K 46 1
                                    

*NI DA AMINIYYA TAH*
_(Ja'adah da Sameerah)_
*2019*

NA *MARYAM S INDABAWA*
*MANS*

*HAJOW*
*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S*

*_(We Educate, Entertain Enlightenment and Exhortation our readers)_*

Facebook @Maryam Sulaiman
Facebook group Indabawa Hausa Novel.
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSIndabawa

*Dedicated to my Bestie*
*Hauwa Kamilu Zimit (Ameerah)*
*Mrs Bashir*

*Bismillahi Rahamanir Rahim*

Friday
26/April/2019
137-138


"Inna lillahi wainna illahir rajiun Abbahn Ja'adah, Kawu ne fa. Mukai shi asibiti dan Allah!"
Sauka saka shi a mota sukai AKTH dashi da sauri emergency aka amshe shi dan bugewa yayi da yake kuma jikin yana da rashi sai ya jara kafkewa dan daga tufafin jikin sa zaka san ba shi da karfi sosai.

An masa komai ya kamata suka bashi daki kan sai ya farfado an ga menene koma kan a sallame shi. haka ta zauna tana ta tunani me ya mai da kawu haka duk da ada yafi haka arziki da rufin asiri.

Sai bayan la'asar ya farka yana tozali da Mamah ya mike zaune yana fadin
"Shin mafarki nake ko ido biyu nake. Yau ke nake gani Amina."

Sai hawaye. Ya fara magana
"Dan Allah ko mafarki nake Amina kice kin yafe min dan Allah. Na cutar dake duk gadon ki na cinye miki daga baya na kore ki banyi tunanin inda zaki dosa ba. Dan Allah ki yafe min dan Allah. Naga rayuwa."
Shi kuka Mamah kuka.

Abbah ne ya ce,
"Ya isa toh! Ba mafarki kake ba sai ka godewa Allah yau ga ka ga ta nan da ran ka ita ma haka duk sai a yafi juna."

Kai kawu ya dago yana kallon ya ce,
"Muhammad kai ne? Ashe har yanzu kana nan da amanar Amina daman kai ka aure ta. Alhamdulilah! Dan Allah ku yafe min wallahi tin da Amina ta bar gida na tin lokacin komai ya fara canjawa karayar arziki na ya'yan da muke nuna wa so duk suka guje mu, rayuwa ta juyan baya da kyar nake samun wanda zamu sa abakin salati. Nayi neman Amina nayi amman ba labari har na hakura na koma amman kullum cikin neman yafiyar ta da addu'a nake Allah ya nuna kin ita. Yau nafi kowa farin ciki da ya nuna min ke."

Sai kuka.
"Ka daina kuka kawu komai ya wuce ai. Kuma gani na dawo gare ku. Nima ina cike da kewar ku. Ga Abbahn Ja'adat nan muyi neman ku amman bamu same ku ba da muka je gidan ku aka ce kun siyar wannan yasa na hakura sai kuma muka bar garin ma."

"Ikon Allah yanzu ba kwa garin kenan?"
"Wallahi dubiya muka zo shine wannan alamarin ya faru. Ashe da rabon zan ganka ne ashe da rabon Ja'adatu zata gana da wani dangin nawa ne. Kai Alhamdulilah. Da mun zata rayuwa ta juya mana baya sai gashi yanzu rayuwa keyi da mu ta dawo.mana da duk dagin mu Alhamdulilah!"

Anan Doctor yaxo ya duba shi daga nan ya bashi sallama suka dauke dan kai shi gidan shi.

A kofar gidan su ka tadda Gwaggo matar sa tsaye ana ta watso kayan su dan basu biya kudin haya ba har na shekara biyu.

Abbah ne ya nufi wajen mai gidan da yake tsaye yana fadin
"Ku fito da kayan dukka!"

Abbah ne yayi masa sallama sannan ya mika masa hannu sukai musabaha. Cikin girmamawa mutumin ya gaida Abbah bama da ya ganshi babban mutum wanda daga kallo kasan kudin sun zauna masa ga kamshin turare da kasa ba karamin kudi ke da shi ba.

"Malam lafiya naga kuna fito musu da kaya!"
"Kyale ni da mutumin nan, shekara biyu da wata biyar fa bai bani kudin haya ba tin ina hakuri har na daina shekara biyu ai ba wasa bane bayan da shi nake rike gida na!"

Ni da Aminiyya tah (Ja'adatu da Sameerah)Tempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang