part 75-76

831 60 1
                                    

NI DA AMINIYYA TAH
(Ja'adah da Sameerah)
*2019*

NA MARYAM S INDABAWA
MANS

HAJOW
HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S

*_(We Educate, Entertain Enlightenment and  Exhortation our readers)_*

Facebook @Maryam Sulaiman
Facebook group Indabawa Hausa Novel.
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSIndabawa

*Dedicated to my Bestie*
*Hauwa Kamilu Zimit (Ameerah)*
*Mrs Bashir*

*Bismillahi Rahamanir Rahim*

Saturday
23/February/2019
75-76


Duk motsin ta idon sa na kan ta duk dagowar da zatai sai sun hada ido. Duk sai ta kasa sakewa. Mustapha kuwa tana zaune yana kallon sarautar Allah dan ya gane cewa tabbas akwai wani abu a kasa tsakain Jawad da Ja'ada.

Ta yadda yaga Jawad din ya kafe ta da ido ko kiftawa bayayi, kuma ba wai normal kallo yake mata ba. Kalllo ne mai cike da ma'anoni daban daban.

Akwai alamun tausayi a cikin kallon da kulawa sannan abinda ya daure masa kai shine son da ya gani tsantsa a cikin idanun sa kwance wanda daga gani kasan ya jima a tare da shi.

A ta gun Ja'ada kuwa ba zai gane ko me ba dan ba wani dagowa take ba. Sai dai ya gane a takure take bai san dalili ba amman sai ya kawo haka da ko dan tana gun ne.

kadan ta iya cin abinckn ta ture sai kunun da Sameerah ta zuba mata ta samu ta sha da yawa. Maganin ta Sameerah ta dauko mata nan da nan tai raurau da idanun ta.

Sai da Sameerah ta ballo maganin ta mika mata sannan ta ga a halin da take ciki. Dan murmushi tayi ta ce
"Haba My Adar! Ki daure kisha kin san fa magani ne lafiyar ki kawai zamu nema yanzu."

Amsa tayi ta jefa bakin ta tare da daga kai dama ta rumtse idanun ta sanna ta amshi ruwan da Sameerah ta zuba mata a kofi ta sheka a bakin ta. Kirji ta dafe tana sauke a iiyar ziciya.

"Sannu!"
Sameerah ta fada.

Mustapha ma ya ce,
"Sannu!"

Kai ta iya daga musu sannan ta mikawa Sameerah cup din hannun ta tace
"Dado min ruwan kinji shi anan!"

Ta nuna wuyan ta. Dada mata ruwan tayi sai dai duk da haka tana jin kamar tsaiwar sa a gun ganin ba tafiya zai ba yasa ta mike ta hau kan gado ta kwanta kawai.

Kayan wajen Sameerah ta kawar. Sannan ta tattare dakin ta fesa roomfreshner, dakin ya dau kamshi.

Momy ce ta shigo ta kalli Sameerah ta ce,
"Ki zo ku tafi dare nayi!"

"Momy ni anan zan kwana!"
Ido Momy ta xaro ta ce,
"Ban son shashanci ki tashi ki tafi gidan ki.'

Idon ta ne ya kawo ruwa ta kalli Muhammad. Momy ya kalla ya ce,
"Momy ki bar ta, ta kwana mana!"

"Aah fa. Dady ne yace ku fito ku tafi,"
"Momy Allah ta kwana da ita!"

Ya mike yana cewa,
"Mustapha muje ko?"

Ya mike suka fice a dakin, a falo suka samu Dady. Muhammad ya durkusa ya ce,
"Abban ni zan tafi!"

"Ina ita Sameerah?"
"Anan xata kwana!"

"Ina A'ah ta zo ta wuce ku tafi gobe ta dawo Maman taku ce zata kwana da ita!"
Jawad zai Magana Dady ya hau kwadawa Sameerah kira.
"Sameerah!"

"Na'am!"
Ta Amsa  fito da sauri. Ganin su Jawad yasa gaban ta faduwa dan tasan Dady ba zai bar ta ta kwana ba.

"Gani!"
Ta fada tana dirkusawa.

Ni da Aminiyya tah (Ja'adatu da Sameerah)Où les histoires vivent. Découvrez maintenant