95-96

651 53 2
                                    

*NI DA AMINIYYA TAH*
_(Ja'adah da Sameerah)_
       *2019*

NA *MARYAM S INDABAWA*
*MANS*

*HAJOW*
*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S*

*_(We Educate, Entertain Enlightenment and  Exhortation our readers)_*

Facebook @Maryam Sulaiman
Facebook group Indabawa Hausa Novel.
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSIndabawa

*Dedicated to my Bestie*
*Hauwa Kamilu Zimit (Ameerah)*
*Mrs Bashir*

*Bismillahi Rahamanir Rahim*


Tuesday
12/March/2019
95-96



Dakin yai shiru na mintina kuwa na kuka wasu na na zuci wasu na na fili.

Dady ne yai karfin halin cewa
"To yanzu dai ya kamata ku ceto min rayuwar ya'ya na."

Dad ne ya juyo ya kalli Dady ya ce,
"Tayaya zamu taimake su."

Izeedeen ne ya ce,
"Dad, Na fada maka Ja'adatu ita ce wacce zan aura. In baza ka manta ba ina yawan kawo maka complain akan yadda Ja'adatu bata sake min da matsalar da nake fuskanta daga wajen ta."

Kai Dad ya gyada. Izeedeen ya ce,
"To Dad ashe akwai wanda sukai soyayya da dadewa tashin su daga kano shi kuma ya tafi kararu shine basu kara haduwa ba."

"Ni kuma a lokacin na hadu da ita a Jigawa. Wanda ta yadda danine dan iyayen ta dake son tai aure saboda sunyi shekaru ba ita ba Shi. To Dad yanzu maganar da ake yana kwance rai a hannu Allah Ja'ada kawai yake so. Ita ma shine ta fadi."

Yai shiru idon sa jajir dashi. Nusaiba ce ta matso gefen Izeedeen ta ce,
"Dan Allah Izeedeen ka ceci rayuwar su. Dan Allah kayi sadaukar wa."

Dad ne ya ce,
"Tabbas dole Son kayi hakuri. Dole kayi sadaukar wa."

"Dad nima na shirya yin komai dan kanwata kuma masoyiya ta."
"Allah maka albarka Son!"

Bai bada amsa ba Wayar Dadyn Sameerah ta hau ruri.

Dadyn Jawad ne. Dauka yayi yana fadin
"Kuna inane yanzu Mustapha yace min kun shigo yanzu!"

"Eh muna bayan office din sa. a wani daki no 5."
"Ok gani nan!"

Ba ajima ba sai gashi tare da Abban Nusaiba. Tana ganin su tayi gun Dady ta fada jikin sa tana sakin kuka.

Janta jikin sa Dady yayi ya ce,
"To menene na kuka. Ai jikin da sauki ko?"

"Dady ku taimaka ku aura musu junan su."
"Me yake faruwa ne?"

Dadyn Jawad ya fada. Dadyn Sameerah ne ya ce,
"Wallahi ashe Ja'adatu da tin farko naso hadasu da Muhammad ta ce min tana da wanda take so na hada su da Sameerah ashe dai shine wanda take so din."

"Ya salam!"
"Wallahi shine yanzu kagan su har da kwanciyya a gadon asibiti."

Nusaiba ce ta basu labari duk abubuwan da ya faru har da ciwon da Jawad ke fama dashi akan Ja'adan da na ita Ja'adan.

Ta ce,
"Dady har yanzu daga Uncle J har Anty Ja'ada suna fama da son junan su wanda ko basuyi aure ba to basu taba zama lafiya ko kwanciyyar hankali wallahi Dady shaidan zai iya raya musu wani abu a ran sa tunda suna sson junan su kuma wallahi Dady Izeedeen zai sha wahala akan Ja'ada dan gaba daya hankalin ta da nutsuwar ta na ga Uncle J tana kawar wa ne saboda Anty Samee. Tana jin nauyin Anty Samee baza ta iya ba dan tana son farin cikin Anty Samee ne. Amman Dady da Abba!"

Ta fada tana mai da hankalin ta ga Dadyn Samee da Abbah ta ce,
"Abba kasan Anty Ja'ada na da ciwon zuciya tin kan tazo garin nan wanda a kullum ta kwanta ciwo Dr na muku gargadi akan ciwon nata. Kasan yadda irin ciwon nan yake ko?"

Ni da Aminiyya tah (Ja'adatu da Sameerah)Donde viven las historias. Descúbrelo ahora