*NI DA AMINIYYA TAH*
_(Ja'adah da Sameerah)_
*2019*NA *MARYAM S INDABAWA*
*MANS**HAJOW*
*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S**_(We Educate, Entertain Enlightenment and Exhortation our readers)_*
Facebook @Maryam Sulaiman
Facebook group Indabawa Hausa Novel.
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSIndabawa*Dedicated to my Bestie*
*Hauwa Kamilu Zimit (Ameerah)*
*Mrs Bashir**Bismillahi Rahamanir Rahim*
Friday
1/March/2019
87-88Ranar alhamis kamu. Har gida aka dauko mai kwalliyya tazo ta dan dasawa Ja'adatu kwalliyya yadda tai kyau ma abin ba a magana.
Wasu golding din material ta saka akai mata nadi da golding head da mayafi da takalmi har jaka duk golding kala.
Gaskiya Ja'adatu tayi kyau. Ankon lemon green din material suka sa green head dukkan su sunyi kyau.
Kafin karfe hudu kowa ya shirya sai da sukai sallah la'asar sannan suka wuce gun da za ai taron.
Wajen kan sa abin kalla ne an mata ado dark green da adon lemon green an tanadi gun amarya da ango.
A wajen suka hadu da ango aka jera masu anko dan shiga da su.
Ango ma yayi kwalluya cikin Golding kalar shadda yar ciki da babbar riga. A tsare aka shiga dasu suna tafiya ana musu liki da fesa musu wani abu mai kyale. Har suka kkarasa wajen zaman su ana musu vedio da hotuna. A tare suka zauna gaba dayan su.
Nan ma mai aikin hoto nayi mai yin vedio nayi daga nan aka fara gudanar da taro. Suna zaune aka dauki amarya aka koma can gefe wani dan daki da ke cikin wajen akai mata kamu. Sai da aka kamata sannan ta dawo gun zaman ta.
Suna zaune aka fara rabon abinci yan mata kuma suna gefen amare wasu na daukar hoto wasu na yin rawa.
A haka aka fito da amarya da ango fili Sameerah ita ta fara bade su da kudi tana musu liki. Sai Nusaiba wacce ta karasa gun Ja'ada.
A kunnen ta ta farai mata magana
"Please Anty ki saki jikin ki kuma kina mmurmushi!"Murmushi da ya zame mata dole shi ta sakar mata dan murmushi ne wanda zafi gare shi amman ga mutane kyan sa suke gani gareta kuwa zafi da radadi yake mata.
Haka aka kira dangin ango sukai.musu liki da kannen sa. Sai dagin amarya nan Momy ta hau ruwan kudi ita da kawayen ta da Kawayen Mamah da suka zo gun.
Da suka gaji aka ce amarya. Da Ango su koma su zauna. Suna zama Izeedeen ya rangwafo da kan sa ya ce,
"My Princess ya naganki duk kinyi sanyi ne?"
"Ido ta dan lumshe tana murmushi ta ce,
"Ba komai!""Ko jikin ne?"
"Eh toh kai...."Marzuk ne ya karaso wannan yasa tayi shiru murmushi ya fara yana fadin
"Amaryar mu! Amaryar mu!"Murmushi tayi ta kawai Ya ce,
"Ya taro?""Alhamdulilah!"
ta fada tana yin kasa da kan ta.Yar rada yayi wa Izeedeen sannan ya bar wajen.
Kallon ta Izeedeen ya tsaya yi kan ta a kasa sai daukar su pics ake. Hannun sa ya daura akan nata da sauri ta dago sukai ido hudu.
Nan ma masu hpto sai yi suke kuma sun yi bala'in kyau. Ido ta lumshe ta zare hannun ta.
YOU ARE READING
Ni da Aminiyya tah (Ja'adatu da Sameerah)
FantasyLabari akan aamintaka wacce ta ke fauke da soyayya tare da sadaukar wa tsakanin amninan biyu. Muhammad Jawad (Yaron littafin) Ja'adatu (Yarinyar littafin) Saneerah (Aminiyar Ja'adat) ku shigo ciki kuji me ke akwai wacce irin sadaukar wa haka Aka yi...