NI DA AMINIYYA TAH
(Ja'adah da Sameerah)
*2019*NA MARYAM S INDABAWA
MANSHAJOW
HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'SFacebook @Maryam Sulaiman
Facebook group Indabawa Hausa Novel.
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSIndabawa*Dedicated to my Bestie*
*Hauwa Kamilu Zimit (Ameerah)*
*Mrs Bashir**Bismillahi Rahamanir Rahim*
16/January/2019
31-32Karfe biyun dare agogo ya nuna. Amman Ja'ada na zaune gefen Sameerah dake ta shakar bacci.
Mikewa tayi tai alwala ta hau kan sallaya ddan ta kasa bacci ssam dai tunanin Jawad da take. Har tai kukan ta gaji.
Haka har asuba ssukai sallah suka koma amman ita sai kitchen ta shiga suka hada break.
Haka bayan sun gama ta koma tai wanka ssanna ta tada Sameerah tai wanka ssuka shirya suka je sukai break.
Duk da abincin kadan Ja'ada ta ci. Suna gamawa suka kkoma falo suna hira kamar yadda suka saba.
Sameerah ce ta kalli Ja'ada ta ce,
"My Adat, me yafi komai dadi ne a duniya?"Dariya sosai Ja'ada tayi har da rike ciki saboda sai ta ji kamar dan ita tai tambayar. Kallon Sameerah tayi, ta ce,
"Kowa ya kwana lafiya. Wato dare yayi ka kwanta lafiya ba damuwar komai da tunanin komai.""Saboda me kika ce haka?"
Murmushi tayi ta ce,
"In kin shiga irin wannan halin zaki san dalilin fadar hakan. Amman bana fata haka tafaru dake. Amman gaskiya abin ba dadi My Samee!"Daga haka kuma sai ssuka ci gaba da hirar su ta Jawad da Muhammad.
In Ja'ada zata kira sunan Jawad sai dai ta ce, Honey J. Wanna yasa Sameerah cewa
"to nima haka zan na kiran Muhammad. Honey M."Tin daga lokacin take kiran sa da Honey M.
Da dare suna kwance ita da Sameerah suna hira sai ga kiran Muhammad. Nan.
Murmushi Sameerah tayi ta ce,
"My Adat kinga dan halak!"Ta ddauki wayar.
Bayan sun gaisa ne, Muhammad ya ce,
"Sameerah kina da murya mai dadi da sa nishadi, muryar ki.na sa na manta duk damuwar ta. Sameerah ina kaunar ki."Sameerah ta lumshe ido ta ce,
"Honey M kenan kada ka zautar dani da kalaman ka fa, kai naje dadin baki kake min kawai. Dan nasan ba za a ce baka taba wata budurwa ba kuma duk ka fada mata wadan nan kalaman, ""Ya isa!"
Ya katse ta cikin fushi ya ce,
"Kina nufin baki yadda dani ba ni mayaudari ne ko?""A'ah ba haka nake nufi ba...."
Kara tsayar da ita yayi ya ce,
"To ni abinda nake fada miki har zuciya ta ne."Sameerah ranar sai da tai danasin fadar wannan abun dan yadda Muhammad ya hau sama sosai. Da kyar ta lallabashi ya yadda da abinda take nufi sannan sukai sallama.
Ido Sameearah ta lumshe ta bude ta kalli Ja'ada da ta zuba mata ido ta ce,
"Gaskiya My Adat na yadda da yadda Honey M ke so na. Na godewa Allah dan nima yadda nake son sa kamar na zauce ne."Murmushi Ja'ada tayi ta ce,
"Kkna so kice son da kikewa Honey M fiye da yadda nake son Honry J?""Eh!"
Dariya Ja'ada tayi ta ce,
"Kar ki soma baki san yadda nake tsananin son Honey J ba. Wallahi zan iya ba shi rayuwa ta. Kar ki manta tin ina yarinyar nake son sa da son sa na tashi. Ina kishin Honey J kamar me?"
![](https://img.wattpad.com/cover/172818435-288-k228203.jpg)
VOUS LISEZ
Ni da Aminiyya tah (Ja'adatu da Sameerah)
FantasyLabari akan aamintaka wacce ta ke fauke da soyayya tare da sadaukar wa tsakanin amninan biyu. Muhammad Jawad (Yaron littafin) Ja'adatu (Yarinyar littafin) Saneerah (Aminiyar Ja'adat) ku shigo ciki kuji me ke akwai wacce irin sadaukar wa haka Aka yi...