part 35-36

738 55 0
                                    

NI DA AMINIYYA TAH
(Ja'adah da Sameerah)
*2019*

NA MARYAM S INDABAWA
MANS

HAJOW
HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S

Facebook @Maryam Sulaiman
Facebook group Indabawa Hausa Novel.
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSIndabawa

*Dedicated to my Bestie*
*Hauwa Kamilu Zimit (Ameerah)*
*Mrs Bashir*

*Bismillahi Rahamanir Rahim*

Juma'at Kareem to all Muslim Ummah. May Allah bless us Ameen.

Friday
18/January/2019
35-36

Dad na ganin kiran ya girgiza kai ya dauki wayar. Cikin muryar shagwaba ya ce,
"Dad ya zanyi?"

"For what?"
"Akan yarinyar nan mana Dad duk abinda nasan yan mata ana musu a birgesu na mata but ita kamar bata san ina yi ba fa."

" 'yar wacce ne?"
"Wallahi Dad ba yar kowa bace, just mahaifin ta na da rufin asiri amman aikin gwamnati fa yake yi ma."

Ajiyar zuciya Dad ya sauke ya ce,
"Mamin ka ta san yarinyar da kake so?"
"Yes Dad shine take fadin wai me zanyi da ita da wasu magan ganu dai "

Dariya Dad yayi ya ce,
"To kai me kace?"

"I love her!"
"Yanzu me kake so ayi?"

"Ban sani ba Dad na rasa ya zanyi da yarinyar!"
"Son what I want u to do is to, be praying, in yarinyar nan alheri ce a gare ka Allah ya saka mata son ka in kuma ba alheri bace Allah ya cire maka son ta."

"Dad ina yi but kamar bana yi!"
"Don't worry son. Haka addu'a take Allah, yana sane dakai ka kara mikewa ga Addu'a, Kaji!"

"Tnc Dad!"
"U re welcome."

Sukai kashe waya, Ajiyar Zuciya Dad ya sauke a ransa yana fadin,
"Allah ne ya tashi jarabar su Mami da danta ga yadda su sai masu kudi suke so kuma su duk abinda suke so sai ssun samu "

Yai murmushi ya ce.
"Alhalin ba haka rayuwa take ba. Ka bi rayuwa a sannu tukkunna."

A haka Izeedeen yai ta damun Ja'ada tun bata sauraron sa har ta fara dan kula shi.

Duk da haka bata bashi damar zuwa ba duk da duk weekend yana zuwa kuma yana ganin ta.


++++++++++++++
A haka har su Ja'ada suka gama exam din su, inda yanzu take Service din ta anan cikin ckul din su.

Sosai take da fannin gogewa dan ita kwarariya ce. Sannan ta mai da hankali akan abinda take.

Duk yadda lectures ke kawo mata hari sam bata sauraron su daga gaisuwa shikenan.

Duk wanda yake cikin ckul din yasan Malama Ja'adatu dan kamun kan ta da iya daukar dressing sam bata kwalliya dan yawan cin kayan ta arebian dogayen riguna ne. Sai dai tai rolling kan ta da mayafi ko ta saka hijab kullum haka take.

Kuma ta iya koyar wa dalibai na son a basu ita sosai. Ga saukin kai da fara'a ba ruwan ta. Wannan yasa take da farin jini a cikin malamai gaba dayan su.

Karfe taran dare tana kwance ta lula duniyar tunanin Jawad din ta, karar wayar ta shi ya dawo da ita daga cikin duniyar tunanin da ta tafi.

Dauka tayi taga Izeedeen ne. Tsaki ta saki sai kuma ta tuna da abinda Mamah ta ce mata dazu.
"Ja'ada girma kike karayi dan ma baki da wasu shekaru masu yawa. Amman duk ya mace mutucin ta dakin mijin ta. Abu daya zan fada miki shine ki mika komai ga Allah. Ki cire Jawad din nan a ran ki. In Allah yayi mijin ki ne wata rana zaku hadu amman yanzu yana da kyau ki.kama dahir kema kiyi aure. In Jawad ne baki sani ba ko yai aure ko ma yana da rai dan na tabbata ba zai zauna tsawon wannan lokacin ba tare da yayi aure ba."

Ni da Aminiyya tah (Ja'adatu da Sameerah)Where stories live. Discover now