91-92

633 44 0
                                    

*NI DA AMINIYYA TAH*
_(Ja'adah da Sameerah)_
       *2019*

NA *MARYAM S INDABAWA*
*MANS*

*HAJOW*
*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S*

*_(We Educate, Entertain Enlightenment and  Exhortation our readers)_*

Facebook @Maryam Sulaiman
Facebook group Indabawa Hausa Novel.
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSIndabawa

*Dedicated to my Bestie*
*Hauwa Kamilu Zimit (Ameerah)*
*Mrs Bashir*

*Bismillahi Rahamanir Rahim*

Saturday
10/March/2019
91-92

"Ja'ada kuma me ya kawo ta nan!"
"Wallahi faduwa tayi!"

"Ya salam!"
Dady ya fada yana fadin
"Muje na ganta!"

Suka nufi dakin da take tana kwace da oxygen ita ma a hancin ta. Kamar mara rai haka take.

Kai Abbah da Dady suka jin jina sannan Dady ya ce,
"Ina Doctorn da ya duba ta!"

"Yana office!"
"Muje na ganshi!"

Ya fada yana yin gaba. Suka mara masa baya.
office din Doctor suka je.

Dr Sani abokin Dr Mustpha ne, Suna zuwa ya mike yana gaishe su. Hannu Dady ya mika masa suka gaisa sannan sika zauna

Dady ne ya ce,
"Me ke samun 'Ya ata ne?"

"Gaskiya Alhaji tana cikin mawuyacin hali. Tana bukatar taimako. Ku taimaka ku bata abun da Take so. In ba haka ba zata iya rasa rayuwar ta."

"Yanzu meke damun ta?"
Dady ya fada.

"Zuciyar ta ce ta Kumbura. Ga jinin ta da yai mugun hawa"
"Inna lillahi wainna illahir rajiun!"

Wayar Izeedeen. Tayi kara ya dauka Dad din sa ne. Dauka yayi. Dad din sa ya ce
"Kana ina ne? Tin dazu nake neman ka!"

"Wallahi ina asibiti!"
"Asibiti?"
Dad ya fada cikin tashin hankali.

"Eh!"
Izeedeen ya bashi amsa.

"Me ya faru kake asibiti!"
"Dad, Ja'adatu ce ba lafiya!"

"Ya salam! Kuna wane asibitin!"
Nan ya fada masa asibitin.

"Gani nan!"
Dad ya fada.

Kallon sa su Dady suka. Izeedeen ya ce,
"Gashi nan zuwa!"

"Toh!"
Suka mike sukai wa Dr godiya suka fita kowa da tunani a cikin ran sa.

Suna zaune a dakin da Ja'ada ke kwance Dad ya kira Izeedeen ya zo.

Fita sukai shi da Buhari suka taro shi tin a hanya yake tambayar me ke damun Ja'adan har suka zo daki.

"Assalamu Alaikum!"
Yai sallama.

Abbah ne ya dagl a razane yana mai kallon Dad.

Shima Dad din ido ya zare yana nuna Abbah dashi. Abbah baki yana rawa yace,
"Yayah!"

Kowa ido ya bisu da shi. Dad kuwa da sauri ya matso ya rumgume shi. Kuka suka saka mai tsuma zuciya.

Dakin dukka yan kallo suka zama. Dad ne ya ce,
"Muhammad ina ka shiga? Muhammad ina ka tafi ka barni da neman ka. Muhammad ina ka tafi baka tunawa da ni. Eh Muhammad!"

Sai ya kara rumgume Abbah. Dadyn Sameerah ne yai gyaran murya ya ce,
"To dai ya isa. Ku zauna muyi abinda ke gaban mu yanzu!"

Dad ne ya dago ya kalli Izeedeen ya nuna Abbah ya ce
"Wannan kanina ne uwa daya uba daya!!

Ni da Aminiyya tah (Ja'adatu da Sameerah)Wo Geschichten leben. Entdecke jetzt