*NI DA AMINIYYA TAH*
_(Ja'adah da Sameerah)_
*2019*NA *MARYAM S INDABAWA*
*MANS**HAJOW*
*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S**_(We Educate, Entertain Enlightenment and Exhortation our readers)_*
Facebook @Maryam Sulaiman
Facebook group Indabawa Hausa Novel.
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSIndabawa*Dedicated to my Bestie*
*Hauwa Kamilu Zimit (Ameerah)*
*Mrs Bashir**Bismillahi Rahamanir Rahim*
Friday
12/April/2019
@9:30pm107-108
Zama tayi anan kasa gefen Mamah. Tana da magana kuma maganar ga Mamah kawai take jin zata iya yin ta.
Gane haka da Momy tayi yasa ta ce,
" 'ya ta dan Allah ki saki jikin ki, ki daure ki amshi komai da kaddarar Allah. Ki sani Allah shi ya kaddarara haka ya jarabce ki. Kiga daga baya sai ya dauke miki Jawad yanzu kuma ya baki shi a matsayin mijin aminiyar ki. Dan Allah ki dauki wannnan kadarar ki rike tta hannu bibiyu nasan Allah zai shige miki cikin lamuran ki."Kamar me jira ai kam sai ta fashe da kuka wanda tin ranar da aka ce an daura mata aure da Jawad take son ya fito amman yaki.
Kuka take sosai kuma duk wanda ya ganta a haka yasan har cikin zuciyar ta. Dan da ido zaka san tana cikin wani hali.
Magana take son yi amman sam ta kasayi. Mamin Izeedeen ce ta mike ta kamo hannun ta. Cikin bedroom din dakin da suke zaune ta shige.
A kan gado ta zaunar da Ja'adatu sannan ta zauna a gefen ta. Hannun ta ta kama ta ce,
"Na lura da Mamahn ki akwai kara da son nuna komai ba komai bane bayan tana jin abin har cikin zuciyar ta. Yanzu wajen watan ku nawa bakwa tare bayan nan kina bukatar hakan ba ma akan al amarukan da suka faru."Tayi shiru sannan ta ce,
"Kamar yadda Momyn ku ta fada ki daure ki cinye wannan kalar jarabawoyin naki da sannu Allah zai miki sauyi mafi alheri. ina son na nusar dake akan abunda wani kin sani wani baki sani ba. Amman zan fada miki nasan ko Mamahn ki da Momy ba lallai su fada miki su ba. Amman ni zan fada miki dan ni daman ya dace na fada miki.
Ina son ki sani da farko aure sunna ce mai karfi a addinin musulunci Allah (SWT) yana cewa
"Yana daga cikin ayoyin sa cewa ya halitta muku matan ku daga kanku domin ku sami nutsuwa agare su. Yana kuma sanya soyayya da jin kai a tsakanin ku"
(30: 21)Annabi Muhammad (SAW) ya ce
"Aure sunnah ta ce, duk wanda yayi shi tamkar ya sami cikar rabin addinin sa ne!
Haaka nan Abu Ayuba ya rawaito cewa Manzon Allah (SAW) ya ce,
"Abubuwa biyar suna cikin sunonin Manzanni. Yawan kunya, da yawan sa turare da goge hakora da kuma aure!"
A takaice aure hanya ce ta jada zuri'ah ta gari da salihar rayuwa da samar da tarbiyyan tafiyar al umma.
Aure ne yake samar da iyali da dangi da kabila. Aure ke sanya soyayya da tausayi da jin kai a tsakanin al umma. Saboda haka wajibi ne ma'aurata su kiyaye hakkin aure domin ibada ce babba mai matukar mahimmanci a rayuwa.
A aure abu na farko da ake so mace ta gane ta fahimce shi shine hakkin mijin ya akanta. Ta gane cewa mijin shine shugaban ta. Ta rika jin hakan a ranta.
Saboda Allah Madukakin sarki yana fadin
"Maza masu tsayuwa ne da shugabanci akan mata. Kuma maza sune suke da fifiko wajen girma da daraja akan mata."
Wadan nan dalilai su za su sa mace ta dinga jin cewa namiji fa shugaba ne kuma ta dinga jin haka a jikin ta. Kuma ya san yyana da hakki a kanta domin ta san ba za ta fita ba sai da izzinin sa.
Manzon Allah (SAW) yana fadin "Saboda girman hakkin miji akan matar sa. Da za'a umarci wani yayi sujjada ga wani da an umarci mace tayiwa mijin ta sujjada, ko da miji zai bukaci amfani da matarsa ita kuma tana kan siradim rakumi to kada ta hana.
A wata ruwayar Bukhari ya ce
"Manzon Allah (SAW) ya ce, indan miji ya kirawo matar sa zuwa ga shimfidarsa ita kuma ta ki har ya kwana yana fushi da ita to mala'iku zasuyi ta tsine mata haf sai an wayu gari.
A wata ruwayar kuma manzon. allah (SAW) ya ce idan mace ta wayi gari tana kauracewa shimfidar mijin ta za suyi ta tsine mata har sai ta dawo.
Idan mace ta gane Hakkin mijin ta a kan ta kuma tayi masa da'a a kan abin da ba sabon Allah bane to hakan zai taimaka kwarai wajen gyaran zuciyar ta.
Abu na biyu shine amana ana so mace ta zamo me amana. kada ta ha'intar ciki abun da ya shafi dukiyar sa kuma ba ta ha'ince shi ba kan karan kan ta
Ha'intar miji wajen dukiyar sa shine daukar wani abun sa ba tare da izinin sa ba. Ha'intar miiji a karan kanta kuwa shine taba da kanta ta ga wani namiji ko kuma ta yi kawance da mijin da ba nata ba. da matar kirki baza tai Haka ba, to macen kirki ita ce wacce bata ha'intar mijin daga dukiyar sa ko kuma da kanta. Salihar mata masu da'a ne ga mazajen su masu tsare mutuncin. Su da dukiyoyin mazajen su. Basu ha'intar mazajen su a lokacin da basa nan.
Manzon Allah (SWA) ya ce,
"Babu yanda za ayi mace ta dauki. Wani abu a dakin mijin ta kyautar da shi ba taare da izinin mijin ta ba to hakan bai hallata ba.
sai sahabai suka tambayi manzon Allah ko da abinci ne, sai Manzon Allah ya ce wadan nan shine mafi daraja a cikin dukiyoyin mu. Ba'a a yadda mace ta dauki abincin Tai kyauta da shi ba. Sai dai ko dafafe in tayi gudun kada ya lalace sai ta sadaukar da shi shima in kmiji ya dawo sai ki sanar da shi. Ko gidan ku zaki kai sai kisanar da shi bare bawa wani can daban yana cikin cin amanar miji."
![](https://img.wattpad.com/cover/172818435-288-k228203.jpg)
BINABASA MO ANG
Ni da Aminiyya tah (Ja'adatu da Sameerah)
FantasyLabari akan aamintaka wacce ta ke fauke da soyayya tare da sadaukar wa tsakanin amninan biyu. Muhammad Jawad (Yaron littafin) Ja'adatu (Yarinyar littafin) Saneerah (Aminiyar Ja'adat) ku shigo ciki kuji me ke akwai wacce irin sadaukar wa haka Aka yi...