part 55-56

691 70 2
                                    

NI DA AMINIYYA TAH
(Ja'adah da Sameerah)
*2019*

NA MARYAM S INDABAWA
MANS

HAJOW
HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S

Facebook @Maryam Sulaiman
Facebook group Indabawa Hausa Novel.
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSIndabawa

*Dedicated to my Bestie*
*Hauwa Kamilu Zimit (Ameerah)*
*Mrs Bashir*

*Bismillahi Rahamanir Rahim*

Wednesday
13/February/2019
55-56

Kwance yake a kan katoton royal bed din sa.  Waya ce a hannun sa sai kiran number Ja'ada yake amman ba a daga ba.

Daman wani lokacin haka zai ta kiran ta ba a dauka ba wani lokacin ma wayar a kashe.

Momy ce ta shigo ganin sa kire da waya yana ta fama kira ba a dauka ba yasa ta ce,
"Wa kake ta kira ne haka?"

"Ja'ada ce Momy!"
Fuska Momy ta bata dan zuwa yanzu tsana da kin Ja'ada sun karai mata yawa a zzuciyar ta saboda yadda Izeedeen ke shiga damuwa akan ta.

Hatta Dad shima yanzu ya shiga damuwa akan labarin Ja'ada da dan nasa. Dan sun fuskan ci tin da ya hadu da yarinyar bai da kwanciyyar hankali kullun cikin damuwa yake. Wannan in akai aure sai tana cutar sa dan yana mata wani irin mahaukacin so ne.

Momy ta ce,
"Wai kai akan mace duk ka bi ka tada hankalin ka haba Izeedeen! Wai akan ka a ka fara soyayya ne, naga kayi soyayya da mata da yawa amman me yasa wannan ya zamo ka ke cikin wahala. Ina lura da kai tun da ka hadu da yarinyar nan ka shiga wani irin yanayi kullum baka da nutsuwa sai damuwa. To wallahi ni sam ban son yarinyar nan,"

Bai jin zai iya tan ka mata dan yadda yake jin sa da zuciyar ssa. Shi zargin sa ma akan wannan mijin kawar tata anya kuwa itama Ja'adan bata son sa.

Dad ne ya shigo dakin ganin Momy tsaye kan dan nasu tana ta fada yasa ya ce,
"Lafiya dai?"

"Ina lafiya Dad yaron nan akan wannan yarinyar duk ya takurawa kan sa. Wallahi Dad da zaku bi ta tawa da an hakura da yarinyar nan nan gaba ban san ya zata mai da shi ba ji fa Dad tin kan ai auren anya haka suka bar min dana kuwa?"

Dad ma cikin bacin rai ya kalli Izeedeen duk da son da yake masa baya jin zai iya yadda ya auri wannan yarinyar mai wahalar mai da yaro tin kan ai auren ina da kuma anyi.

"Son ka shiga hankalin ka in ba haka ba wallahi auren nan za a fasa shi gwara ma ka shiga hankalin ka."
Da sauri Izeedeen ya mike yayo gun Dad ya ce,
"Dad nifa ba akan ta ne na ke damuwa ba akwai abinda ke damuna ne kawai."

"Karya kake kaji na fada maka. In kana so na yadda da batun auren nan ka shiga hankalin ka. Kasan kwanciyar hankalin ka ita ce ta mu dan haka ka nutsu."
Dad na gama magana ya fita.

Bayan sa Momy tabi. Izeedeen ya fada kan gado yana fadin dole ya boye damuwar sa ko dan a bar shi da Ja'ada. Yanzu yaga har Dad din ma ya daina ta ta su lallai in kuwa Dad ya juya masa baya akan batun auren ya zai yi.


Ja'ada na kwance a dakin su ita da Sameerah. Dan kwanan nan jikin ta yana matsa mata daurewa kawai take yi. Sameerah ta shigo ta zauna tana kallon ta.
"Sannu da hutawa!"

"Yauwah!"
Ta fada tana mikewa zaune.

"My Adat gida na zakije ki daukon wani akwati na na hada shi tin kan na haihu kaya nane a ciki dan Allah! Sannan ki duba cikin kaya na akwai wasu takkadu da kudi ki kwason su."
"Toh!"

"Yauwah driver na waje yana jiran ki."
Mikewa tayi ta saka hijab ta dau wayar ta ta fita. Bayan ta Sameerah tabi dai dai zata fita Jawad ya shigo.

Ni da Aminiyya tah (Ja'adatu da Sameerah)Onde histórias criam vida. Descubra agora