NI DA AMINIYYA TAH
(Ja'adah da Sameerah)
*2019*NA MARYAM S INDABAWA
MANSHAJOW
HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'SFacebook @Maryam Sulaiman
Facebook group Indabawa Hausa Novel.
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSIndabawa*Dedicated to my Bestie*
*Hauwa Kamilu Zimit (Ameerah)*
*Mrs Bashir**Bismillahi Rahamanir Rahim*
Monday
18/February/2019
65-66A bangaren Izeedeen kuwa kayan lefe ya hado na gani na fada masu kyau da tsada.
Dan kayan yawan su ma baza su littafu ba haka nan bazai ce ga kudin da ya kashe wajen hado kayan ba. Amman ko daga ido kasan kaya ne masu kyau da tsada.
Haka ya hada set din akwati uku cike da kaya nan ma dan Mamin sa ta hana amman haka ya ce sun yi kadan.
Ita dai Mami sam bata son auren nan dan ta gama fuskantar sam yarinyar ba wani son dan ta take ba ta tabbata akai aure yaron ta sai inda Allah yayi da shi.
Ita a ran ta cewa take da ma yarinyar nan ta mutu da kowa ya huta ma. Ba yadda zatai sai dai addu'a da take wa dan nata Allah ya rage masa son da yakewa yarinyar nan.
A bangaren Izeedeen ba son Ja'ada kawai yake ba shi dai baza ce ga feeling nata da yake ji ba amman yasan yana jin ta har jinin jikin sa.
Abu da yake damun sa ne idan ya kira number Ja'ada yaji ta a kashe dan ita kamar bata dau waya da mahimmanci ba sai wayar ta, ta kwanan biyu, uku har sati ma a kashe kuma bata damu ba.
In yana son jin muryar ta wani sa'8in da lucky in ya kira ta dauka nan ma ba wata hira daga gaisuwa shikenan.
Amman in kunga irin murnar da yake sai ku zata wasu dadadan kalaman tai masa.
Tin da ta koma gidan su Sameerah yake nacin yana son ya zo amman ta ce, ya bari sauran kwana nawa ai bikin.
A razane ya ce
"What My princess kina nufin kice har sai an daure aure ko time din biki zan ganki. I can't gaskiya bazan iya ba, wallahi kan time zan iya haukacewa.""To zan tsaida maka da ranar da zaka zo!"
"Da dai ya fi. Yauwah nace ba abinda kike bukata na lefen ki?""Ni bana bukatar komai!"
"Ok shikenan!""Aha sai da safe!"
Ta fada tana dauke wayar a kunnen ta.Kwanciyya tayi tana juyi tana Allah, Allah lokaci yayi yayi aiyi komai a huta ita ta huta shima Izeedern din ya huta sannan Jawad ya sakar mata mara ta yi fitsari.
Haka nan Izeedeen ya dame ta da lallai lallai shi akawo laife. Ta ce sam biki tin sati biyar za a kawo lefe ina laifin in ya rage sati biyu.
Da yaga kamar Ja'ada ba so take ba sai yai wa Dad din sa maganar kan a sanar da gidan su Ja'ada za a kawo led.
Haka akayi kuwa Abbah mahaifin Ja'ada ya fadawa su da Dadyn Sameerah inda Dadyn sameerah ya ce su kawo duk lokacin da suka shirya.
Anan suka tsaida lokaci kan sati kai zuwa zasu kawo wanda a ranar saura sati uku biki kenan.
Zaune suke a falo Ja'ada da Sameerah. Ja'ada na sanye da C-blue din net material an mata dinkin doguwar riga yai mata kyau sosai. Kalbar dake Kan ta take tsefewa, tana gamawa ta taje kan nata gashin ta ya zubo gadon bayan ta.
Sameerah dake zaune rike da Junaid tana bashi Mama ita ma tana sanye da jan material dinkin riga da siket yai mata kyau sosai sai tashin kamshi suke.
ŞİMDİ OKUDUĞUN
Ni da Aminiyya tah (Ja'adatu da Sameerah)
FantastikLabari akan aamintaka wacce ta ke fauke da soyayya tare da sadaukar wa tsakanin amninan biyu. Muhammad Jawad (Yaron littafin) Ja'adatu (Yarinyar littafin) Saneerah (Aminiyar Ja'adat) ku shigo ciki kuji me ke akwai wacce irin sadaukar wa haka Aka yi...