NI DA AMINIYYA TAH
(Ja'adah da Sameerah)
*2019*NA MARYAM S INDABAWA
MANSHAJOW
HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'SFacebook @Maryam Sulaiman
Facebook group Indabawa Hausa Novel.
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSIndabawa*Dedicated to my Bestie*
*Hauwa Kamilu Zimit (Ameerah)*
*Mrs Bashir**Bismillahi Rahamanir Rahim*
8/January/2019
14-15
Jawad yana koma gida shima wanka yayi ya haye gadon sa. Bacci ne ya kauracewa idon sa dan Ja'ada kawai yake gani a idon sa da irin yadda take kallon sa. Wanda yake tada masa da hankali.
Sai kuma muryar ta wacce in tai masa shhagaba yake jjin ta har cikin jikin saa. A duniya yana son Ja'ada.
Kyan ta ilimin ta nutsuwar ta, tarbiyar ta, hankali, komai nata yana son sa. Zai iya cewa bai taba haduwa da yarinyar da ya ji ta shiga ransa kamar Ja'adatu ba.
Haka yai ta juyi daga baya ya mike ya yo alwala. Kan sallaya ya hau yana ta sallah da addu'a Allah mallaka masa Ja'adaty Allah yasa Ja'adatu matar sa ce.
Har karfe biyu idon sa biyu. Abu na farko da ya farai masa yawo akai shine ya kamata ya koma karatun sa kan lokacin Ja'adatu itama ta gama nata.
Yanzu tana JS 2 nan da four years shima ya gama degree amman abin hau shi shine yanzu an yi jamb dole sai ya bata wata shekarar.
Mai sauki ne tin da yasan ko bai da komai Dady zai masa aure bare kuma shima yanzu ya tara abinda ya tara tinda Dady ya daura shi akan companyn sa.
Da haka ya ta Allah Allah safiya tayi ya je ya ga Ja'ada. Tin asuba bai koma ba, yai wanka ya shirya cikin Bakin Wando da bakar riga mai dogon hannu.
Sai tashin turare yake, tin karfe bakwai ya fice a gidan. Gidan su Ja'ada ya nufa.
A lokacin fitowar ta daga wanka kenan tajiyo knocking. Daurin kirji ne a jikin ta sai katon hijab har kasa. soro ta nufa tana fadin
"Waye?"Jin muryar ta yasa ya ji wata nutsuwa tare da sauke ajiyar zuciya sannan ya ce,
"Nine!"Bude wa tayi ta ja baya. Shigowa yayi kallon ta ya tsaya yi ya ce,
"Beauty Nah Morning!"Murmushi tayi ta juya ta zata shige ciki hannu ta yai saurin janyowa ta fada jikin sa.
Kamshin turaren sa da kamshin sabulun da tai wanka da shi na safeguard na lemon suka hadu suka bada wani kamshi mai dadi.
Matse ta yai a jikin sa ya ce,
"Ina zaki?""Honey J ka sake ni."
"Naki."Kafa ta fara bugawa ta ce,
"Zan makara fa."Murmushi yayi ya ce,
"Baza ki makara ba.""To sake ni."
kan ta ya dago ya kura mata ido. Idanun ta da suke kallon kasa ta dago ta zuba masa.Nan da nan ya rasa nutsuwar sa. Rumgume ta ya karayi tsam a jikin sa ko zai daina jin abinda yaji yana fizgar sa.
Yar kara ta saki dan sosai ya matse ta. Sai taji zanin jikin ta na kokarin kwancewa.
"Honeyyy Jyyyy....!"Ta kira sunan sa da wata irin murya. Take idon sa ya kada yai jajir. Jikin sa yai sanyi, sakin ta yayi ta gyara zanin ta tayi cikin gida.
Tsaye ya ke ya kasa koda yafiya. Dan jikin sa ya gama yin sanyi. Yayi da na sanin kallon ta da har ta kalle shi da wannan idonun nata masu sa shi shiga wani hali.
YOU ARE READING
Ni da Aminiyya tah (Ja'adatu da Sameerah)
FantasyLabari akan aamintaka wacce ta ke fauke da soyayya tare da sadaukar wa tsakanin amninan biyu. Muhammad Jawad (Yaron littafin) Ja'adatu (Yarinyar littafin) Saneerah (Aminiyar Ja'adat) ku shigo ciki kuji me ke akwai wacce irin sadaukar wa haka Aka yi...