part 67-68

714 60 2
                                    

NI DA AMINIYYA TAH
(Ja'adah da Sameerah)
*2019*

NA MARYAM S INDABAWA
MANS

HAJOW
HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S

Facebook @Maryam Sulaiman
Facebook group Indabawa Hausa Novel.
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSIndabawa

*Dedicated to my Bestie*
*Hauwa Kamilu Zimit (Ameerah)*
*Mrs Bashir*

*Bismillahi Rahamanir Rahim*

Tuesday
19/February/2019
67-68


A bangaren Jawad ma bayan ya gama biya bukatar sa ya mike ya shiga toilet yai wanka ya fito ya fada kan gado zazzabi mai zafi ya rufe shi tini ya shige cikin bargo yana rawar sanyi.

Sameerah da bacci ya dauke ta, Juyi take tayi alamar dai ko mafarki take ko wani abun na damun ta.

Can ta mike da sauri tana salati, dakin ta kala sannan ta sauke ajiyar zuciya.

Jawad ta gani cikin bargo wannan yasa ta mike ta fada bandaki wanka tayi tai alwala sannan ta dawo kan gado tayi Addu'a ta tofa sannan ta  kwanta. Amman sam bacci yaki dauke ta.

Tana tunanin mafarkin da tayi. A ranta ta ce Allah yasamu cika da rai da imani.

Sai gab da asuba sannan bacci ya dauke ta.

Ana fara kiran sallah kuma ta mike. Jawad na cikin bargo duk da idon sa biyu ya kasa tashi. Dan haka ta mike tayo alwala sannan ta dawo gefen sa.

Bargon ta dan bude ta kalle shi ta ce,
"Honey M...."

Ganin yana rawar sanyi yasa ta daura hannun ta akan jikin sa. Wani irin xafi taji a jikin sa.

"Na shiga uku Honey M baka da lafiya?"
Ta fada tana dafa kan sa.

Wani zafi ta kara ji wannan ya sa ta kara tsora ta ta zaro ido tini mafarkin da tayi ya fado mata wai gata ta mutu.

Ta shiga uku kar dai Honay M ne xai mutu. Sai ta fashe masa da kuka.

Duk yadda yake jikin jikin sa haka ya janyo ta jikin sa yana bubbuga bayan ta a hhankali.

"Ya isa menene na kukan?"
Ya fada a hankali.

"Honey M ji fa jikin ka. Tashi mu tafi asibiti."
Kai ya girgiza ya ce,
"Bari nayo alwala ki daina kukan nan kinji."

Ya mike da kyar ya shige ban daki, da kyar yai alwala saboda sanyin ruwan.

Yana fitowa ya kalle ta cikin jarumta ya ce,
"Na tafi massalaci ki ta shi kiyi sallah."
Mikewa tayi ta bi shi har kasa ta raka shi sannan ta dawo sama.

Dakin Ja'ada ta shiga ta hange ta a cikin bargo ita ma.
"Lafiya?"

Ta fada dan tasan Ja'ada bata bacci dan tin kan ayi kiran sallah take tashi kuma bata kuma komawa amman kuma gata kwance da alamun ma bata tashi ba.

Dakin ta karasa ta bude bargon. Jin an bude ta yasa tai saurin janyo bargon. Kallon ta Ja'ada tayi da rinanun idanun ta sannan ta lumshe su.
"Kema baki da lafiyar ne?"

"A'ah zazzabi ke damu na!"
Ta fada murya na rawa.

Kirjin Sameerah ya kara buga wa tino da mafarkin da tayi dai, sai hawaye ya taru a idon ta.

Kallon ta Ja'ada tayi ta ce,
"Kuka zakiyi haba My Samee ki hari please mene abin kukan?"

Ta fada tana bude bargon jikin ta. Dan ta nunawa sameerah jikin nata da sauki.

Amman tana mikewa tsaye tayo baya da sauri Sameerah ta taro ta ta fado kan ta.
"Subhanallah!"

Ido Ja'ada ta lumshe, sannan ta kara yunkurawa zata ttashi.

Ni da Aminiyya tah (Ja'adatu da Sameerah)Donde viven las historias. Descúbrelo ahora