Part 23-24 (Tafiyar Honey J)

745 77 0
                                    

NI DA AMINIYYA TAH
(Ja'adah da Sameerah)
*2019*

NA MARYAM S INDABAWA
MANS

HAJOW
HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S

Facebook @Maryam Sulaiman
Facebook group Indabawa Hausa Novel.
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSIndabawa

*Dedicated to my Bestie*
*Hauwa Kamilu Zimit (Ameerah)*
*Mrs Bashir*



*Bismillahi Rahamanir Rahim*

Ayi hutun karshen mako lafiya.

Saturday
12/January/2019

23-24


Washe gari da safe daga Jawad har Ja'ada da sukai sallah asuba bacci ne ya dauke su. Sai karfe tara suka tashi.

Sosai sukai mamaki dan dukkan su ba ma'abota baccin safe bane. Jiki a mace suka mike.

Wanka Jawad ya shiga ya fito ya hada kayan da zai amfani da su sannan ya shirya cikin wani Blue din wando da yellow riga mai dogon hannu wacce akai rubutu da Yellow a gaban rigar.

Jikin sa ya bade da turare sannan ya hada duk abinda zai bukata a cikin akwati ya ajiye a falo.

Yana sauka ya tadda Momy da Dady a falo. Durkusawa yai ya gaishe da su. Sanna ya mike zai tafi.
"Jawad karfe sha biyu ne tafiyar ku fa.!"

Gaban sa ya ji ya fadi ya ce,
"To Allah nuna mana.!"

Ya ffice. Gidan su Ja'ada ya nufa. Lokacin ta mike ta shiga wanka. Ta fito ta shirya cikin wata yellow kala atamfa wacce ta ke da zanen blue da baki.

Batai kwalliya ba ta hade jikin ta da humra da kuma turarukan da Jawad yake kawo mata. Falo ta nufa ta zauna ta ce,
"Mamah, Honey J yazo ne?"

"A'ah nima tunanin da nake kenan. Abbahn kuma ya ce bai fita sai yazo sunyi sallama gashi har yanzu shi....."

"Assalamu Alaikum!"
Salamar Jawad ta katse mata maganar da ta ke.

"Wa'alaikum salam!"
Suka Amsa. Mamah ta ce,
"Yanzu muke maganar ka!"

Takalmin sa ya cire ya shiga dakin ya ce,
"Sai gani ba."

Idon sa ya sauka akan Ja'ada da ke jigine da jikin bango ta zuba tagumi.

Zama yayi ya ce,
"My Ja'ada tagumi ba kyau."

Hannun ta ta janye. Ya kalli Mamah ya ce,
"Mamah ina kwana?"

"Lafiya lo Jawad yasu Momyn taka?"
"Suna lafiya."

"Yanzu nake magana Abbah ya ce bai fita sai kazo kunyi sallama gaka shiru."

Kai ya sosai ya ce,
"Wallahi bacci ne ya dauke ni da safe sai tara na tashi "

Ya kalli agogo ya ce,
"Gashi yanzu karfe goma."

"Yau Bacci kuka sha kai da mutuniyar taka kenan. Itama yanzu ta tashi."
Ta kalli Ja'ada ta ce,
"Ja'adatu dauko muki abincin ku."

Mikewa Ja'ada tayi a hanakali ta nufi waje. Kallo Jawad ya bita dashi sannan ya dawo da kallon sa ga Mamah.

Abbah ne ya shigo ya ce,
"Jawad ka shigo kenan."

"Eh wallahi Abbah barka da safiya."
"Yauwah ka tashi lafiya?"

"Lafiya Alhamdulilah!"
"Masha Allah. Nace ai ba zan fita ba sai Jawad ya zo munyi sallama."

"Allah sarki. Sai gashi banzo da wuri ba."
"Ai ba komai."

Ni da Aminiyya tah (Ja'adatu da Sameerah)Tahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon