*NI DA AMINIYYA TAH*
_(Ja'adah da Sameerah)_
*2019*NA *MARYAM S INDABAWA*
*MANS**HAJOW*
*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S**_(We Educate, Entertain Enlightenment and Exhortation our readers)_*
Facebook @Maryam Sulaiman
Facebook group Indabawa Hausa Novel.
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSIndabawa*Dedicated to my Bestie*
*Hauwa Kamilu Zimit (Ameerah)*
*Mrs Bashir**Bismillahi Rahamanir Rahim*
Thursday
14/March/2019 @8:40pm
101-102Har washe gari Ja'ada bata tashi ba abinda ya dan kara daga hankalin iyayen nata kenan.
Duk suka shiga rudu da fargaba bama Mamah da take ganin kamar Ja'ada mutuwa zatai.Bata da aiki sai kuka da addu'a haka ma Sameerah da ka ganta zaka san bata cikin hankalin ta. Komai da take jiki a sabule. Da taje gun Jawad ya tambaye ta Ja'ada cewa tayi tana gida.
Da ya kawo mata zancen an ce bata da. Lafiya shiru tayi ganin xai gano wani abu ta ce,
"Taji sauki sun ma wuce jigawa ne.""Me zasuyi a jigawa!"
"Zata je ganin Doctor tane?""Ga Mustapha nan!"
"Ai kasan wancan doctor yasan komai akan ciwon nata ""Ina son nai waya da ita!"
"Sai dai ka bari zuwa anjima."Kallo yabi Sameerah da shi a ransa yana mai rashin yadda da abinda duk take fada masa.
Shifa jikin sa ya gama bashi Ja'ada bata da lafiya sosai amman ya yi shiru ko dan kar ya bari su Dady suga yasa damuwa Dady yace baza a sallema shi ba.
Da yamma bayan Dadyn Jawad yaje yaga Ja'ada ne ya wuce gun Doctor dake kula da ita. Yana ganin Dady ya mike cikin girmamawa ya mika masa hannu suka gaisa.
Zama Sukai Dady ya ce,
"Ya me jikin kuwa?""Alhamdulilah! Daman ina son naga daya daga cikin ku!"
"To toh da akwai wata matsala ne?"
Dady ya tambaya.Kai Doctor ya girgiza ya ce,
"Ba wata matsala bace, jiya ne mukai waya da Doctor Fauwaz nake fada masa duk halin da ake ciki shine yace ya kamata akai ta ya ganta. Abinda nake son fada muku kenan dan a yi shirye shirye kuje can ina muku fatan samun nasara acan din."Sosai Dady yaji dadi dan yana jin labarin Doctor Fauwaz kan a ganshi sai anyi blocking amman su gashi ya nemi suje su ganshi. Wannan ya sa yaji dadi ssosai ya kuma fadawa Doctor cewa a fada masa nan da kwana biyu zai gansu yanzu zai je ayi maganar shirye shiryen tafiyar tasu.
Ya fita yana mai godiya ga Doctor sannan yayi dakin Jawad. Jawad ne kadai a dakin ya zuba uban tagumi da ka ganshi zaka san yana cikin damuwa. Har Dady ya shiga da sallama ya zauna bai san ma ya shiga ba.
Mikewa Dady yayi ya dafa shi sai aa lokacin ya dago da sauri. Murmushi ya kakalo. Dady ma Ya sakar masa murmushin. Kujera ya janyo ya zauna a gaban sa ya ce,
"Muhammad fada min damuwar ka ko jikin ne?"Kai ya girgiza ya ce,
"To menene?""Dady jiki na yana bani My Ja'ada bata da lafiya, Dady ko wacce damuwa ta akan ta take, Dady ku kai ni naga My Ja'ada ganin ta shi zai ciren duk wata damuwa ta."
Ya fada yana share kwallar da ta zubo.masa a idon sa.Abbah dake tsaye a kofar dakin yana ji kuma yana kallon su take tausayin Jawad ya kamashi. Dady ya ce,
"Nace ka kwantar da hankalin ka ko?""Dadyn Jawah ya kamata a fada masa me ya ke damun Ja'ada shine mafita nasan zai zama mai tawakali da mata addu'a amman boye masa sam bazai sa ya cire damuwar sa ba."
Dady da Jawad suka daga kai suna kallon Abbah dake shigkwa dakin yana magana.
VOCÊ ESTÁ LENDO
Ni da Aminiyya tah (Ja'adatu da Sameerah)
FantasiaLabari akan aamintaka wacce ta ke fauke da soyayya tare da sadaukar wa tsakanin amninan biyu. Muhammad Jawad (Yaron littafin) Ja'adatu (Yarinyar littafin) Saneerah (Aminiyar Ja'adat) ku shigo ciki kuji me ke akwai wacce irin sadaukar wa haka Aka yi...