NI DA AMINIYYA TAH
(Ja'adah da Sameerah)
*2019*NA MARYAM S INDABAWA
MANSHAJOW
HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'SFacebook @Maryam Sulaiman
Facebook group Indabawa Hausa Novel.
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSIndabawa*Dedicated to my Bestie*
*Hauwa Kamilu Zimit (Ameerah)*
*Mrs Bashir**Bismillahi Rahamanir Rahim*
Saturday
5/January/20189-10
Yana tashi gida yayi nan ya tadda Momy na ta fadan ko break bai ba ya fice, hakuri ya bata sannan ya gaye ssama ya kwanta.
Baccin awa daya kawai yayi alarm ya tada shi. Wanka yayi ya saka wani farin wando da bakar Riga. sosai yai kyau sai daukar ido yake, ga wani kamshi me dadi da ya dinga fitar wa. yayi sallah sannan ya dauki mota sai bakin Gandu special primary school. Yana zuwa tana fitowa. Motar ya fito ya kulle ya karasa wajen ta.
Tana ganin sa ta saka dariya ta ce,
"Yaa Jawad!""Na'am yan makaranta. Ya makarantar?"
"Alhamdulilah!"Fulas din hannun ta ya amsa, haka suka tafiya suna ta hira abin su gwanin ban sha'awa duk wanda ya hango su a haka yadda ya rike hannun ta sai ya ce, wa da kanwa ne.
Haka suka karasa gida, ta shiga da sallama Mamah ta ce,
"Yan Makaranta an dawo?"Kai ta gyada ta ce,
"Tare muke da Yaa Jawad!""Shigo dashi mana."
Ta fita ta kamo hannun sa suka shiga.Kara gaisawa sukai da Mamah sannan Ja'ada ta mike ta shiga tai wanka ta fito ta shirya cikin wani brown kala, Pakistan ta yafa mayafin kayan.
Ba kwalliya sai kamshin turaren humra da takeyi. Sallah tayi sanna ta fito. A falo ta tadda Mamah ta zubawa Jawad danun shinkafa wanda yaji gyada da zogale yai kyau da shi.
Ci yake yana ta zuba santi. Zama tayi tana kallon sa. Kallon ta yayi ya ce,
"Toho muci tare."Matsawa tayi suka fara ci, cikin Mamaki da dabara sai gashi sun cinye tare har Mamah ta dado musu kuma wani ikon Allah ko amai bata yi ba.
Sosai Mamah tayi mamakin dan tasan Ja'adatu in dai taci abinci mai yawa sai ta dawo dashi amman yanzu kuma ji yadda suka ci tare da Jawad ba ma tasan ta ci ba.
Suna zaune suna ta hira har karfe biyu tayi mikewa tayi ta je ta sako uniform din ta. ta dauko jakar ta.
Jawad ya mike ya ce,
"To Mamah mu zamu tafi sai anjima.""Adawo lafiya toh!"
"Allah yasa!"Suka hada baki suka fada. Hannun ta ya kama har sai da ya kai ta kofar ajin su sannan ya juyo ya koma ya dau motar sa.
Gida ya nufa yana shiga ya yi dakin sa da yake Momy bata nan. Bacci ya kwanta yayi.
Uku da rabi ya mike ya kara wanka ya canja shiga zuwa, bluen wandon jeans sai jar riga mai ratsin blue, ya saka agogo da takalmi bakake. Alwala yayi ya nufi massalaci yai sallah.
A cikin massalaci ya zauna har karfe biyar sannan ya mike ya fito, motar sa ya dauka ya nufi layin su Ja'ada yana cikin mota har biyar da rabi tayi sannan ya fito ya tsallaka titi ya karasa makarantar su.
Tana fitowa ta ganshi ta karaso gun sa. Hannun ta ya kama suka nufi gida.
Sai da ta shiga ta sanar da Mamah sannan ya shiga. Ya samu Mamah na fito da uniform din Ja'ada na boko kala uku sai na isilamiyyar ta kala biyu.
ESTÁS LEYENDO
Ni da Aminiyya tah (Ja'adatu da Sameerah)
FantasíaLabari akan aamintaka wacce ta ke fauke da soyayya tare da sadaukar wa tsakanin amninan biyu. Muhammad Jawad (Yaron littafin) Ja'adatu (Yarinyar littafin) Saneerah (Aminiyar Ja'adat) ku shigo ciki kuji me ke akwai wacce irin sadaukar wa haka Aka yi...