Page 1 and 2

4.3K 180 2
                                    

® *REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS P.M.L*💭💭💭

_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_

# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035

🏵🏵☀☀🏵🏵☀☀🏵🏵
           ☀ *WAYE MACUCI*☀         
🏵🏵☀☀🏵🏵☀☀🏵🏵
   '''Suhaif koh Suhail'''

                      
                       ©
'''Marubuciyar Rayuwar Sumayyah'''

    *SA'EEDA MUSA DAUDA😍*

'''Follow and ✅ote me on Wattpad''': *SaeedaMusaDauda*

*Suhail* _fans ina baku hakuri a bisa jina da kuka yi shiru, ba wai na d'and'ana muku zuma a baki bane, da yardar Allah sai kun jita a bakin ku, a bisa nazari da tunani da nayi na canja sunan sabon littafin da zan rubuta muku mai suna_ *Suhail* zuwa *Waye Macuci??* '''Suhaif koh Suhail'''  _da fatan zaku bani had'in kai_.

*BESTOWED TO MY LIL SIS*: '''Sumayya Musa Dauda'''

          

                          
                  1⃣—2⃣   

  

'''Inalillahi wa'inna ilaihiraji'un''',   bawan Allah ka tausayi min dan Allah kar ka k'eta min haddi, karka yi garguwa da lalurata   ka cutar da rayuwa ta........ka dubi maraici na, ka tausayamin,  wayyo ni Aysha wai ba mutane ne a wurin........., ya Abdallah ka kawo min d'auki..., ta saki kuka mai cin rai lokaci guda tana lalil'o y'ar sandar ta domin ta kwaci kant, gogan naga kuwa koh sauraranta bai yi ba,   yayi nisa wurin sarrafa ta burin shi kawai ya kai ga cimma biyan bukatan shi. Sautin sauk'ar  numfashin shi da kuma sheshek'ar kukan Aysha ne kad'ai ke tashi a d'akin, tun da take bata tab'a tsintar kanta a irin halin da take ciki ba sai yau, bata tab'a jin rad'ad'in kasancewar ta makauni ba sai yau, ina ma da tana gani da koh ta halin yaya sai ta kwaci kan ta daga gare shi.

           Ganin yana neman raba ta da kwayan jikin ta ta kwad'a mishi cizo a yatsa da yayi sanadiyar sa shi kwad'a ihu ba shiri ya rike hannun yana yarfewa saboda zogin da kuma rad'ad'in da hanun ke mishi. Jin ya cika ta ta mik'e tsaya tana lalob'o jikin bangon d'akin tana neman k'ofan fita, cikin zafin nama ya cafko ta ya had'a ta gam da jikin shi, tare da zura harshen  sa a bakin ta, bai damu da zafin da hannun ke mishi ba, da k'arfi ya rab'a ta da kayan jikin ta ya hau aika mata da hot romancing, sai da ya d'auki tsawon lokaci a hakan kafin ya kai ga cimma burin shi a kan ta. Yana gamawa ya zira rigan jikin shi, ya mai da mata nata kafin ya fice a gidan cikin maye. Abun da bai sani ba tun lokacin da ta cije shi garin yarfe hannu zoben da ke hannun shiya fad'i a k'asa.

         Sosai take ta aikin kuka, idanuwan ta suka kad'a suka yi jajawur da su, ganin babu sarki sai da Allah da kyar ta fara lalib'o sandar ta, cikin sa'a hannun ta ya sauk'a akan zoben, da sauri ta d'auka tana tattab'awa da d'aya hannun ta, jin zobe ne yasa tayi saurin zirawa a hannun ta tare da d'auko sandar ta tafara tafiya jikin ta kaca kaca da jini, Allah ya taimake ta ma cikin dare ne da bata san  yaya zata yi da tsegumin yan anguwa ba, a daddafe ta k'araso cikin gidan tana d'aga k'afa dakyar saboda radad'in da take ji a kasan ta, cikin sa'a bata ji motsin kowa ba a gidan, da kyar ta iya jan jikin ta tana k'ok'arin shiga d'aki taji muryar inna Larai tana cewa" ke makauniya daga ina kike cikin daren nan koh da yake ba abun mamaki bane dan an saba fita yawon maula". Bata kula ta ba ta ci gaba da lalib'o bakin k'ofar d'akin ta, tana d'aga k'afa da k'yar dan kar inna Larai ta fahimci halin da take ciki. Ganin tak'i ce mata kala, cikin zafin nama inna larai tasa kafa ta buge santar Aysha ta fad'i tiiimmmmm, uwar k'ara ta saki, hawaye na bin fuskan ta d'aya bayan d'aya, haba inna Larai ta kwashe da dariyar keta har da rik'e ciki tana cewa" maganin ki shegiya kawai wallahi tir da haihuwar makauniya wanda bata iya banbance daren ta da ranar ta, balle kuma ace suffan ta, ke kam duk nakasashshen da ya aure ki ya shiga uku, dan babu wani namiji mai lafiya da zai iya auren mai lalura irin taki, tana gama fad'a tayi shigewar ta d'aki ta bar Aysha a yashe a kasa, da k'ar taja jiki ran ta na mata suya ta shige d'aki ta kwanta akan katifar ta, ta saki kuka mai cin rai, babu abun da yafi d'aga mata hankali sai yanda tana ji bata da ikon gani mutumin nan ya keta mata haddi babu d'igon tausayi a zuciyan shi. Kuka ta k'ara fashewa da shi, da k'arfi tana cewa" shikenan na rasa budurcina, ga makanta ga kuma rasa budurci wannan da me yayi kama??. Muryar mahaifiyar ta ke mata yawo a dodon kunnuwan ta a lokacin da take cewa" Aisha ba da son raina zan tafi na bar ki ba, na sani mutane da yawa zasu iya kawo mishi hari saboda kasancewar ki makauniya ba lallai bane ki iya gane su, kar ki sake son abin duniya koh shaid'an yayi sanad'iyar raba ki da mutuncin ki dan shine garkuwar ki. Wasu zafafan kwalla ne suka wanke fuskan ta d'aya bayan d'aya, daren ranar da kyar barci b'arawo ya d'auke ta.

WAYE MACUCIWhere stories live. Discover now