🏵🏵☀☀🏵🏵☀☀🏵🏵
*☀WAYE MACUCI☀*
🏵🏵☀☀🏵🏵☀☀🏵🏵
'''Suhaib koh Suhail'''***********************************
® *REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS P.M.L*💭💭💭
_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_
# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
©
'''Marubuciyar Rayuwar Sumayyah'''*SA'EEDA MUSA DAUDA😍*
'''Follow and ✅ote me on Wattpad''': *SaeedaMusaDauda*
*BESTORED TO MY LIL SIS* ''' SUMAYYAH MUSA DAUDA'''~Sorry for the errors ban samu daman yi muku editing ba saboda wasu uzuri na, manage the page cuz i don't want to keep you waiting~
1⃣0⃣
yana shawo kwanan gaban shi ne ya yanke rasssss ganin Ilu na rumgumo Aysha ita kuma tana turjewa,,
ai kuwa bai san lokacin da zuciya ta kawo shi ba a kufule yayi wurin su ya damk'o Ilu yana fidda hucin bak'in ciki ya had'a kan shi da jikin bango ya bashi wasu lafiyayyun tagwayen maruka guda biyu wanda suka sanya shi ganin taurari,,
marin ta zo ma Ilu a bazata, cikin tsananin rud'ewa da kuma jin zafin marin Ilu ya dafe kuncin shi yana zazzaro ido a tsorace dan ganin inda marin ta fito,,
Aysha da bata san abunda ke faruwa ba sai jin k'arar saukan mari tayi, ba zato ba tsammani ta tsinkayo muryar ya Abdallah yana cewa" dan uban ka wani d'an iskan ne ya baka izini ka taho k'ofar gidan nan balle kuma ka samu daman cin zarafin baiwar Allah Aysha ??
hantar cikin Ilu ne ya kad'a k'uuuuu dan ya san cewa ya Abdallah mutum ne mai tsananin zafin rai, wurgo kuturun hannun shi yayi sama kana ya d'ora a ka ya fara maganar kutare yana yi yana kai hannu hanci yace" wayyo Allah yau ni Ilu d'an gidan malam Sabo naga ta kaina,,
ya had'e dunkulallun hannayen shi yace" ni dai ka yi min rai Audu wallahi tsautsayi ce ta kawo ni wurin shatu, ya fece majiya kana ya d'ora da cewa" in zaman zamana na taso ashe da rabon zan saya bala'i da kud'i na,,
ba wannan na tambaye ka ba cewa nayi wa ya baka izinin tahowa gidan nan ??", ya Abdallah ya fad'a a tsawace,,
jiki na b'ari ya tsugunna har k'asa yana ba ma ya Abdallah hak'uri, sai da ya Abdallah ya nad'a mishi na jaki kana ya kyale shi dan ganin yanda jini ke ta b'ul b'uluwa a bakin Ilu,,
cike da marifa ya cika shi with an angry look ya rik'e kunnen shi alamar gargad'i yace" daga yau sai yau idan na ga ka sake zuwa wurin Aysha, wallahi koh a hanya ka gan ta kayi yunkurin ci mata zarafi sai na yi gunduwa gunduwa da naman jikin ka kowa ma ya huta ka dai ji na fad'a, mtssssss ya ja tsaki,,
Ilu na ganin an cika shi ya rarumi takalmin shi yana yana gudu tangal tangal kamar irin ta yara,,
sai da ya d'an yi nisa dan har ya shawo kwana kana ya juyo yana duba bayan shi da maganar kutare yace" shege d'an iska basamuden banza wallahi k'arya kake ka raba ni da shatu idan ma kishi kake kwanan nan zan gwada maka jarumta ta na d'auke shatu daga wannan bukkar taku na kawo ta gida na, yana fad'a yayi shigewar shiga rai a b'aci dan jin yanda jikin shi yayi tsami dan ba k'aramin duka ya ci ba a wurin ya Abdallah",,
bayan barin shi wurin ne ya Abdallah ya juyo kan Aysha ya da zuwa yanzu ta fara nemo sandar ta dan ta shige gida, zubo mata idanuwan shi yayi yana zallan aikin kallon ta,,
a take wani irin tausayin ta ya kama shi dan ya san cewa rashin idanuwan ta ne yasa mutum kamar Ilu yake cin zarafin ta, duk da cewa Aysha makauniya ce amma koh kad'an k'imar ta ya wuce a mai da ta tamkar kwallon k'afa kamar yan da ya ga Ilu yayi,,
kallon yananin yanda ta sunne kan ta a ka'sa tana lalumo sandar ta da hannun ta ya kuma yi kana yayi wurin da take ran shi na mishi k'una,,
hawayen bak'in ciki ne ya sub'uce mishi ganin yanda ta take yi,,
cike da tausayin ta ya durk'usa a gefen ta kad'an ya d'au sandar ta ya mik'a mata da murya mai kama da ta tsantsar tausayi yace" ga sandar taki nan k'anwa ta amsa kiyi shigewar ki gida",,
kunyar shi ce ta kama ta na ganin yananin cin zarafin da Ilu ke mata a d'an kunyace ta mik'e hannun ta zata amsa sandar a wurin shi cikin rashin sa'a garin lalib'u sandar hannun su ya had'e guri guda,,
wani irin shock yaji da da sauri ya turo mata sandar a hannun ta, amsa tayi ta mik'e tsaye tana k'ok'arin shigewa gida,,
a sanyaye ya mik'e daga durk'ushen da yake murya a sarke yace" Aysha ki daure ki fad'a min makoma na a zuciyan ki, ki sani cewa aure shine cikar mutuncin ki zaman ki a haka zai dad'a haifar miki da wata matsalar, indan yau Allah ya bani ikon taimaka miki a yayin da wata matsala koh sharri ta taso miki wallahi Aysha ba lallai bane na iya sani balle na taimaka miki,,
kin sani cewa kasancewar mace budurwa kuma makauniya zaki fuskanci lalubale da dama kuma ba lallai ne ki iya kare kan ki ba",,
gaban ta ne ya fad'i rassss dan jin k'arshen maganar shi, zancen zuci ta kama tana cewa" Allah sarki ya Abdallah da ina da halin mallaka maka zuciya ta da nayi, ba k'in ka nake ba illa wata katanga da ta shiga tsakanina da koh wani d'a namiji wanda hakan ta sanya bana jin zan iya soyayya da koh wani d'a namiji ba,,
uhhhm ina sauraran amsa ta a game da maganar da na fad'a miki kwanakin baya, ya fad'a tare da tsare ta da idanuwan shi kamar wani tana ganin shi,,
Dan Allah ya Abdallah ka taimaken ka janye maganar nan ba tun yau ba na fad'a maka cewa ba lallai bane inna ta amince da soyayya a tsakanin mu,,
na san kana iya bakin k'ok'arin ka dan ganin ka inganta min rayuwa ta amma Allah na nan kuma shi yake saka ma duk wanda aka zalun ta, shi yasa a duk lokacin da na tuna da Allah rabin damuta raguwa yake yi dan na san yana kallon duk abubuwan da suke faruwa a kaina, a duk lokacin da yaga dama shi zai saka min",,
jiki a sanyaye ya Abdallah yace" na san da hakan amma ki sani cewa baki da kwakkwaran hujjan da zata raba alaka a tsakani na da ke so ki bar fakewa da inna dan na san hanyar da zan bi na nemo amincewar"
"hhhmmmm har yanzu baka fahimce ni ba", ta fad'a
"bazan tab'a fahimtar ki ba", ya fad'a a raunane",,
bata kuma ce mishi komai ba tayi hanyar cikin gida ta bar shi nan a tsaye, ba ta d'au lokaci ba ya bi bayan ta shima zuwa d'akin shi,,***********************************
*washe gari************************************
wata mata ce na gani wacce baza ta wuce kimanin 40years ba tana zaune a kan wata had'add'iyar kujerar da ke wani tangamemen parlour mai d'auke da kayan alatu kala kala, gefen ta kuma wani matashin saurayi ne na gani ya kwanta a kujerar da take zaune a kai tare da yin filo da cinyar ta suna hira cikin so da k'auna shikuwa sai shagwab'e mata yake yi kamar wani k'aramin yaro abun gwanin ban sha'awa dan kana ganin yanayin zu zaka fahimci cewa happy family, baka hango komai a fuskokin su sai kayatattun murmushi da ke d'auke a fuskokin su,,
a cikin hirar su ne naji matar tana cewa" wai ni kam son when last kuka making call da bros d'in ka naga nayi ta k'iran layin shi but it wasn't going ??"
da tsigar shagwaba ya mai da face d'in shi yana kallon silin yace" uummm let me think mum, if i got it right it was yesterday morning, if i was not mistaken i was the one that called him, almost 5 times na ke ta k'iran numbar shi da kyar ta shiga,,
murmushi ta sakar mishi kana ta shafo suman kan shi tace" lallai ma son shine brother d'in ka bai k'ira ni ba balle na sa ran zai aiko min da sak'on gaisuwa ?? "
afwan mum may be he was busy ne shi yasa ya tsaya kad'an before ya d'ora da cewa" he told him to greet you tsafff na manta ne ban fad'a miki ba and they are about to finish their service but he insisted him to tell me the exert time but he refused, and shi wai he wanted to surprice us",,
babu wanin nan son na san cewa kana kare d'an uwan ka ne, Suhaib da Suhail tagwayen mum soyayyar ku a jini take d'ayan ku baya tab'a son laifin d'an uwan shi, mum kenan ta fad'a fuskan ta na bayyana tsantsar farin ciki dan jin lafiyar d'an nata"
*Sa'eeda ✍🏻*
~Y'ar mutanen Dengi~
YOU ARE READING
WAYE MACUCI
Historical FictionLabari ne a kan wata mak'auniyar Allah mai suna Aysha wacce take soyayya da yayan ta amma kwatsam sai wata tsautsayi ya afka mata har hakan ya saka ta cikin bakin ciki,ba tare da ta bayyana mishi ba sai daga baya ya fahimci halin da take ciki a tsan...