Page 42

627 46 0
                                    

🏵🏵☀☀🏵🏵☀☀🏵🏵
          *☀WAYE MACUCI☀*         
🏵🏵☀☀🏵🏵☀☀🏵🏵
        '''Suhaib koh Suhail'''

***********************************

® *REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS P.M.L*💭💭💭

_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_

# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
      
          
                       ©
'''Marubuciyar Rayuwar Sumayyah'''

    *SA'EEDA MUSA DAUDA😍*

'''Follow and ✅ote me on Wattpad''': *eedatou*

*BESTORED TO MY LIL SIS* ''' SUMAYYAH MUSA DAUDA'''

*Harfsart (ummu twin)* '''insha Allah'''
*Ramab*
*Ummu Rumaysa*
*MOMYN SADIQ*
*Ameena mmn Nafi*
*Limaballe*
*Hafsat Sale*
*Ummin Zaarah*

       _Duk na ga sharhin ku da ma wanda ban fad'a ba na gode gaskiya saboda sun min dad'i matuk'a Allah ya bar zumunci, ku yi min afuwa masu comments kar ku ga ban rubuta sunanan ku ba duk matsayi guda kuke a wuri na ina mugun yin ku kuma insha Allah na tanadar muku pages na musamman a gaba da zaku rubuta sunayen ku duk da dai na san ba zai iske ku duka ba._

                        4⃣2⃣

*Note edited*

'''Alhamdulillah'''  cikin ikon Allah su dad suka garin Madina cikin k'oshin lafiya, jirgin su na saukowa suka fara taka matakalan jirgin suna fitowa, dad ne ya fara fitowa sannan kuma sai mum da Aysha da suke biye da shi, wani irin tsassanyar   ni'imtaccen iska suka shak'a ba shiri suka numshe ido su suna masu yin hamdala ma sarkin da bai da tamka Allahussamad,,
    D'auko musu bags d'in su wani mutum yayi ya nemo musu motar da zai kai su masaukin su da already suka booked daga nan kuma suka doshi masaukin su.
     Ba su wani yin tafiya mai nisa sosai ba sai ga su sun iso suka fito su duka suka nufi cikin gidan yayin da drivern ya shigar musu da bags d'in su. 
     Babban gida ne mai d'auke da d'akuna biyu sai kuma wani tangamemen parlour mai d'auke da kayan alatu masu matuk'ar kyan gaske, komai na gidan cassssss abun shi dan kayan da aka tanadar ma gidan ta dace da tsaruwan gidan, a parlourn na ga su dad sun zauna kowannen su yana fidda numfashi sama sama sai da suka huta gajiya kana dad ya shige wani d'akin da nake kyautata zaton na su ne shi da mum, mum kuwa kamo hannun Aysha ta yi zuwa d'ayan d'akin tare da had'a mata ruwan wanka ta taimaka mata da dukkan abunda zata bukata da na ci da na amfani kana ta ma mata sallama kasancewar yamma lissss suka iso ta tafi saboda washe gari suke sa ran ganin doctor.
    Da daddare dad na gani a kan bed kunnen shi manne da waya yana magana yayin da mum take kwance a gefen shi ta rumgumo shi ta baya, a cikin wayan tashi ce naji yana cewa" son kenan very soon zamu b'ata da kai a kan daughter ban da haka yaushe isowan amma duk ka bi ka addabe ni a bata waya ku gaisa habbbaa ai ka bar ta ta huta mana".
    Daga d'aya b'angaren Suhail ya shagwab'e fuska kamar yana ganin mahaifin na shi yace" oohhhhh shiiitttt dad how many hours na d'auka ban sanya ta a idanuna ba sannan kunnuwa na basu ji muryar ta ba ai na yi k'ok'ari gaskiya, ni wallahi na k'osa a yi aikin nan ta samu lafiya ayi maganar aure dan na gaji da yangan da dad ke min a kan daughter d'in shi".
     Murmushi dad yayi yace" ka ji ni da ja'irin yaro wato koh kunya na ma baka ji kake wani sako magana koh ? toh na ga uban da zai baka daughter ai tunda y'a dai tawa ce hmmmmmm", ya k'are maganar tare da jan kwafa mai k'arfi, mum kuwa sai dariyan su take yi.
    B'ata rai Suhail yayi dan sai da dad ya gano hakan kana yace" wayyo dad so kake k'aunar daughter d'in ka ya haukata ni, rashin daughter d'in ka a rayuwa na tamk'ar an yanka min ticket na barin duniya ne, sai kuma ya kwantar da muryar ya ce" i'm serious dad so nake da kun dawo ku mana aure kawai mu bar muku gida dan na gaji da cin girkin mum cuz yanzu hannun ta ya fara gajiya",,
    mum na jiyo abunda yace tayi saurin k'arb'an wayan tace" oohhh haka ma kace son tammmm zamu gamu da kai ai daga yau nayi girki ban k'ara sa maka",,
     Cike da tsokana Suhail yace" ohhhhoo dai sai na sa dad ya k'aro aure amaryar shi ta din ga bani, yarinyar sharrrrrr zan nemo ma dad".
     Saurin mik'a ma dad wayan mum ta tare da juyowa da jikin ta ta d'aya b'angaren bata kuma bi ta kan su ba, ganin haka dad yace" tund ka b'ata ma matata rai sai dai ka kwanta kayi barci zuwa gobe ku yi waya or else ka apologizing ",
     da yake a hands free dad ya saka wayan kan dad ya k'ara sa maganar tuni Suhaib ya hau magiya yana ba ma mum hak'uri, hakan ya sa mum tuntsurewa da dariya saboda ganin handa d'an nata ya susuce lokaci guda a kan mace.
    A haka dai suka gama wayan cikin raha da anushuwa daga bisani dad ya kai ma Aysha wayan tare da ficewa daga d'akin tare da yi mata sai da safe idan ta gama gobe da safe ya k'arb'o wayan saboda da he can't wait cuz there is too much stress a jikin shi. 
      Tana jin ya fice daga d'akin tayi sallama cikin tsiririyar muryar ta, Suhaib ya amsa cike da jin dad'in voice d'in ta ya kwatar da murya yace" da fatan amarya ta ta iso Marina lafiya ? yaya kwannan bakwanta ?
     Cike da jin dad'in sunan da ya k'ira ta da shi tace" Alhamdulillah yaya na na mun bar ku lafiya ?
    Lafiya lau babyna sai dai abu d'aya ya min cikasss ha hana ni sukunni kuma ya sanya zuciya ta cikin kad'aici".
     Cike da damuwa tace" Subahanalillahi, wani abu ne ya d'aga maka hankali har ya hana ka sakewa yaya na,?         
    Murmushi yayi na jin dad'in yanda ta damu akan damuwar shi sannan yace" ba komai bane illah rashin ki, Aysha ina son ganin ki kusa da ni, da kin ga halin da nake ciki yanzu da kin tausaya min domin kuwa a yini d'aya raakkk na rame na fita hayyaci na kamar ba Suhail d'in ki ba".
    Da murya irin ta tausayawa tace" kar ka damu yayana da yardar Allah na kusa dawowa gare ka dan sai ka gaji da gani na, abu d'aya nake so da kai, ina so kayi yaki da zuciyan ka ka cire duk wani abu da ka san zai hana min kai sukuni sannan ka dinga saka wa a ran ka a duk inda kake ina mak'ale a cikin zuciyan ka kaga kenan har abada ina tare da kai tunda zuciyar ka na tare da gangar jikin ka".
     Wani irin kayataccen murmushin jin dad'i ya sake kamar tana ganin shi saboda jin dad'ad'an kalaman da ke fitowa a bakin ta he can't believe cewa Aysha ce take furta wad'annan kalaman, tabbbbbb idan koh haka ne idan ya aure ta zai more dan zai ga soyayya tsantsa.
     K'asa b'oye farin cikin shi yayi sai da ya bayyana shi a fili yace" idan koh haka ne a duk lokacin da tunanin ki yayi min yawa zan sa hannu a saitin zuciya ta na rungume gurin, a koh da yaushe zuciya ta zata zame min abokiyar hira har sai ranar da kika dawo".
     Su duka suka yi jimmmmmm yayin da suke maimaita k'almomin da suka fad'a ma junan su a zukatan su lokaci guda shauk'i da begen junan su ke dad'a ratsa bargo da b'argon jikin su".
    jin shirun yayi yawa ne cikin mutuwar jiki Suhail yayi k'arfin halin cewa" me kika fi so a zuciyan ki kiyi arba da shi bayan idanuwan ki sun bud'e ?
     Shiru ta mishi kamar baza ta amsa mishi tambayar ba can ta bud'e baki tace" y'anci na shine abu na farko da zan so na fara ganin, sannan kuma masoyi na da bai kyamace ni ba ya nuna min soyayya a lokacin da na ke matsayin makauniya".
    "Y'anci" ya nanata a k'asan zuciyan shi yayin da lokaci guda ya kama sake sake a k'asan zuwan shi yana tuanin wani irin y'anci ne ta fad'a da har zata yi mararin gani bayan shi ? 
       shin y'anci mutum ne koh kuma wani abu ne da za'a iya gani da ido, koh dai wani ya mata k'aryar cewa ana gani y'anci da ido ne ?, inko haka ne dole na tambaye ta kuma dole ta bani amsa".
    yana kawo nan ya gyara kwanciyan shi  yace..........

'''Manage i'm out of charge'''

Pls share
*eedatou✍🏻*
      ~Y'ar mutanen Dengi~

WAYE MACUCIWhere stories live. Discover now