Page 45

785 41 0
                                    

🏵🏵☀☀🏵🏵☀☀🏵🏵
          *☀WAYE MACUCI☀*         
🏵🏵☀☀🏵🏵☀☀🏵🏵
        '''Suhaib koh Suhail'''

***********************************

® *REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS P.M.L*💭💭💭

_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_

# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
      
          
                       ©
'''Marubuciyar Rayuwar Sumayyah'''

    *SA'EEDA MUSA DAUDA😍*

'''Follow and ✅ote me on Wattpad''': *eedatou*


*BESTORED TO MY LIL SIS* ''' SUMAYYAH MUSA DAUDA'''

     ~Ku min uzuri please tunda muka shiga tsakiyan littafi abubuwa suka min yawa, amma za ku dinga ji na duk bayan kwana d'aya wasto zan dinga tsallaken kwana d'aya, da fatan zaku karbi uzurina in mugun yin ku luv love fans💘💘💘.~

                       4⃣5⃣ 

Ba su san sanda suka yi wurin su Aysha da sauri ba hankali a tashe mum ta hau jijjigo ta tana cewa" wake up daughter, what happens to you, amma koh gezau Aysha ba ta motsa ba.
      Tsoro ne ya kama zuciyar Suhail dan har ga Allah bai fahimce abunda take nufi ba, a tunanin shi za ta nuna farin cikin ganin shi a had'uwat su ta farko ido da ido da ita amma kuma sai ya ga akasin hakan dan bisa dukkan alamu reactions d'in ta na nuna a tsorace take da shi.  Hhhuuuhhh, ya fuzar da iska lokaci guda ya hau sake sake a zuciyan shi yana cewa" I'm confused something might happen some were else, why lokaci guda ta turning haka kamar ta ga dodo koh dai ban mata a matsayin masoyi ba ne?, nooooo idan ma haka ne shi won't act like this, a fili kuwa fuskan shi na bayyana tsatsar damuwa dan ji yake kamar yayi kuka, cikin dakiyar zuciya yace" baby na taso please !!! ki taso kar ki sa zuciya ta ta buga ba zan jure ganin ki a haka.
    Ganin sai sambato suke yi sun fita a hayyacin su dad ya yi ta maza ya d'auko bottle water a fridge ba tare da ya tsaya ya gama bud'e covern ba ya hau shek'a ma Aysha ruwan ajikin ta, saukan ruwan ke da wuya ta hau jera dogayen ajiyan zuciya sau uku kana ta raba jikin ta da na Suhail, ta mak'ure a jikin bango ta cusa kan ta a tsakiyan cinyoyin ta tare da rufe idonuwan ta gammmmm dan har yanzu tsoroce take da shi lokaci guda ta kama tsambatu tana cewa" don't you ever come close to me, I have you !!!!, na tsane ka nace bana k'aunar ganin ka", tana fad'a ta hau hau rera kuka yayin da jikin ta ya hau kakkarwa.
     K'iris ya rage zuciyan Suhail ya buga dan jin irin munanan kalaman ta masu kama da dafi a zuciyan shi, ya k'ura mata ido lokaci guda gaban shi na tsananta bugu da sauri da sauri fatttt fattttt fatttttt kamar zai fatso k'irjin shi,,
    saurin dago da kan ta ta yi tana had'a ido da shi ta rarrafa da gwiwowin ta ta zo gun mum ta b'oye a bayan ta tare da lafewa a jikin ta, ba tare da ta tsagaida kukan ba dan koh kad'an ba ta k'aunar ta bud'e ta ga Suhail a gaban ta haka kawai take jin tsanar shi na d'arsuwa a ran ta.
     Ba ki a bud'e su mum suka tsaya suna kallon wannan bakon al'amari, abunda koh a mafarki ba su tab'a tsammanin hakan daga gare ta ba,  k'asa jurewa mum ta yi fuskan ta na bayyana tsantar mamaki tace" Suhail d'in ki ne fa daughter, the one you always dreamed of setting your eyes with, ta yaya za ki ce kin tsane shi bayan mu kan mu shaida ne a kan irin son da kike mishi. Janyo ta mum ta soma yi tana k'ok'arin zagayo da ita ta gaban ta tace" Oyya ta so ki ga masoyin ki mai k'aunar ki daughter wanda ya yi da ban da *macucin* da ya so ya jefa rayuwar ki cikin garari". Instead of ta sakin jikin ta sai dad'a shigewa jikin mum take ta cusa kan ta a jikin ta lokaci guda sautin kukan ta ke ta tashi a hankali.
    Suhaib kuwa mutuwar tsaye ya yi yana kallon ta dan ya fahimci cewa tsoron shi take yi, abu d'aya ya tsaya mishi a rai shine mai yasa daga had'uwar su take tsoron shi ? Me ya mata da take furta k'almar k'i a gare shi?, a iya hasashen shi ya san cewa bai da wani aibu da mace za ta futa k'almar k'i a gare shi kuma yana da tabbacin koh da aure ya taso ma yi bai da wani mummunan d'abi'a da za a hana shi yarinya, but sai kuma ya ga Aysha tsoron shi take ji, koh dai aljanu ne da ita ?, tambayar da ya yi ma kan shi kenan .
     Girjin shi ne ya soma bugun tara tara dan ya fara tsorata da lamarin ta, da kyar dai ya iya bud'e baki yace" baby nine fa Suhail d'in ki ne fa wanda kike k'auna please come over to me, me na miki kika tsane ni ?", ya k'are maganar yana mik'o hannu ya tab'a jikin ta. 
    Wata uwar tsawa ta sakar mishi tace" kar ka kuskura ka ce za ka tab'a ni, wallahi tallahi ka kuskura ka tab'a ni sai na illata ka, i hate seeing you !!! ka b'ace min da gani mugu azzalumi macuci kawai, ka sani a da na so ka yanzu zuciya ta cike take da tsantsar tsanar ka, ta k'are maganar yayin ta dad'a k'ara sautin kukan ta.
     Wani irin tashin hankali ne ya ziyar ci zuciyan Suhail murya na rawa kamar mai yin stammering yace" mum..... alja....... nu ne da ita, wallahi Alja........nu ne da.......   it...... a, idan ba haka ba kuma sauya mana ita sukayi suka d'auke mana tamu Ayshar suka bar mana ta su, ku yi gaggawan dawo min da masoyi ta dan na san Aysha ta ba za ta tab'a tsanata ba hasali ma zuciyar ta cike take da k'auna ta.
     Yana gama rufe baki mum ta karb'e zancen cike da so much pain a zuciyar ta tace" kin san abunda kike fad'a kuwa daughter ?, please idan dramer kike yi ki daina kar ki sa hankalin mu ya tashi dan na san cewa baza ki tab'a tsanar Suhail ba, da Suhaib kika fad'a zan dora alhakin da irin cutar da yayi miki ne ya yawo hakan".
     Duk dramar da ake yi dad na dask'are a guri d'aya ya k'asa koh da kwakkwaran motsi, ji yake abun kamar almara, sai da ya ga da gaske take ta k'i barin jikin mum, ya ja jiki a sanyaye yana d'aga k'afa da kyar ya janyo ta da hannu d'aya daga jikin mum, Suhail na k'ok'arin kamo hannun ta ta daddage ta kwad'a mishi wani uban firgitaccen mari da sauri ya saki hannun ta ya dafe kuncin shi ya tsaya yana kallon ta lokaci guda yana jin wani irin zafi a zuciyan shi. 
    Anya kan ki d'aya kuwa Aysha ?, wallahi sai yanzu na tabbata cewa aljanu ne suka shiga jikin ki dan haka kawai ba za ki tsanne d'anuwan ki kuma masoyin ki ba balle kuma ki k'ira shi da macuci ba", infact ma *Waye macuci* ?? '''Suhaib koh Suhail'''??, dad ya k'are maganar tare da jefo mata tambaya.
     Zuwa yanzu zuciyar ta ta gama bushewa babu wata alamar tsoro a zuciyan ta, idan ka ga kwayan cikin idon ta za ka hango zallan revenge ne a ciki, murmushi mai ciwo ta sake ba tare da ta amsa ma dad tambayar shi ba tace" a cikin hayyacin na nake dad, kuma duk abunda ka ga na ma Suhail he deserved more cuz he ruined my life and my happiness,zuwa gaban Suhail ta yi ta watsa mishi kallon tsana tace" har ila hau ba zan yi dana sanin ja maka Allah ya isa ba, ire iren ku tamk'ar gub'a ne a cikin al'umma, have it been na san cewa kai ne macucin da ya d'and'ana min azaba, ya distroying life d'ina, ya maida ni tamkar wata mujiya a cikin al'ummma, da babu abunda zai sa na k'aunace ka, tana kawo nan ta had'iye miyau mai d'aci tare da bud'e bag d'in ta ciro zoben nan da ta jima tana adanawa saboda jiran rana irin wannan ta d'ago shi sama dai dai inda sautin fuskan shi yake ta nuno mishi kana ta d'ora da cewa" zaka iya tunowa da wannan zoben ? could you remember when you raped a decent handicapped lady ?
    Wani irin shocked Suhail ya ji lokaci guda gumi ne ke ta k'aryo mishi, tambayoyi ya hau jefo ma kan shi cikin tashin hankali yace" ashe da ma Aysha ce yarinyar da na jima ina dakon ta a zuciya ta dan ya nemi gafarar ta??  ashe dama a inuwa d'aya nake da yarinyar da ya lalata mata rayuwa ? '''ya Ilahi''' wannan wace irin rayuwa ce, Allah ka sa ta ganne cewa ba da son raina bane tsautsayi ne ya afka min,, saurin dafe kan shi ya yi saboda wani irin tsarawa da kan shi ke mishi mum da dad kuwa jikin su ne ya d'au rawa da jin abunda Aysha ta fad'a lokaci guda suka hau jifan shi da kallon tuhuma.
     Shigowar su Sudeeq da Suhaib kenan suka tarar da su hakan, bin Aysha Suhaib yayi da kallo lokaci guda yana had'iyar miyau saboda yanda ta sauya mai kamar wata d'iyar laraba bai tare da ya lura da irin kallon tsanan  da take aika mishi ba, suna had'a ido ta watso mishi uwar harara,  duk da bata tab'a ganin shi ba amma jikin ta na bata cewa shine Suhaib *macucin* da ya kai ta gidan k'aruwai saboda kamanin da suke yi da Suhail lokaci hawayen da ke fuskan ta suka kakkafe, yana ganin haka ya had'iye miyau kuttttt.
     zagaye shi ta soma yi cike da bak'in ciki tace" '''Suhaib''' kenan a gaskiya na yaba da irin namijin k'ok'arin da ka yi na ganin ka b'ata min suna, ka zalunce ni ta b'angarori da dama, ka b'ata min suna a idon al'umma, ka san wani irin d'aci na ji a sanda aka yi ta d'aukan hotuna na a media a matsayin karuwa mai zaman kan ta ??, oohhhh yeeehh i see you have done a well job, dole na saluting d'inka na k'ok'arin da ka yi ka min public disgraced and kuma ba ka bar ni ba ka sa min karara a rigata sannan kuma ka yage rigar, put it at the back of your mind sai na zame maka tamk'ar ciwon ido ??, uuummmm so painful da ka k'ira ni magajiyar k'aruwai.
      Barin wurin shi ta yi ta tak'o a hankali ta zo gaban Suhail ta hard'e hannun ta tace" '''Suhail''' masoyi sannan kuma macuci, i have been looking for you wanted sai kuma ga shi Allah ya bayyana min kai, lokaci guda Allah ya sa na d'ora idanuwana a kan ka,   ka yi nasarar jefa zuciyata cikin kunci, a dalilin ka kowa ya kyamace ni, hhhhmmmmmm dole kaima ka d'and'ana irin suyan da na ci, tana fad'a ta d'auke idanuwan ta daga kan Suhail ta maida kan dad tace" no need of answering your question dad let mum judge and answer it.
      Tana fad'a ta ba da bayan ta tace" mum, *Waye Macuci* ?? '''Suhaib koh Suhail''' ??
    K'asa amsa mata tambayar mum ta yi ta ak'o har wurin da Suhail yake ta jacking d'in shi tace" is it true that you raped Aysha ?, da gaske ne cewa ka raping daughter ? haushe ka sauya daga tarbiyar da na ba ka ??, sunno kai k'asa ya yi ya k'asa d'aga ido da ita hakan ya tabbatar mata da cewa ya aikata laifin da take tuhuman shi da shi. murmushi mai ciwo ta saki kana ta d'ora da cewa" ashe dama cikin da Aysha ta yi b'arin shi jinin ka ne ??, da na d'auka kai mutumun kirkine but now you have broken all the trust i have for you, ta k'are maganar tare da fashewa da kuka mai cin rai.
     Jin kukan da mum ke yi ne ya dad'a tsumama zuciyan dad a take ya hau kwad'a ma Suhail mari ba kakkautawa da kyar Sadeeq ya iya taro shi yana ba shi hak'uri dad kam sai cewa yake bar ni na kashe shi na huta da bakin cikin da ya cusa min".
    Sai da Sadeeq yayi da gaske kana dad ya hakura ya haura sama yana huci mum ta biyo bayan shi.
    Da shigowan su yace" Maryam ban tab'a tunanin yaron nan zai iya mana haka ba, wai yaushe ne duniya ta lalace da har yaro kaman Suhail zai iya yin wannan zalunci for God sake babu koh d'igon imani ya k'eta ma yarinyar nan haddi, wallahi abu d'aya ya hana ban koro su daga gidan nan ba, kawai ban san wace irin rayuwa za su fuskanta ba idan suka bar gidan.
     Sharo busassun hawaye mum tayi tace" dadyn kids so nake ka kwace ma Aysha hakkin ta, kar ka bari auren su ya yihu idan aka yi haka an zakulci Aysha balle kuma yaron nan Abdallah da d'au alkawarin auren shi da Aysha.
    Sai yanzu maganar alkawarin da ya ma Abdullahi ya fad'o mishi a rai,  bai ce komai ba ya sura ma ceiling ido yana tunani.
     B'angaren su Aysha kuwa su dad na barin wurin da gudun ta ta fad'a d'akin ta tana kuka, duk da dai cewa makauniyace ita a baya bai hana ta gano d'akin ta ba saboda she is imagining yanda ta yi rahuwa a gidan hakan ya taimaka mata wurin gano d'akin ta.
     Da isowan ta ta maida k'ofan ta rufe gam tare da fashewa da matsananciyar kuka, bugun Suhail take ji sosai a k'ofan yana kuka yana magiya yana cewa"ta bud'e please, ta tsaya ta saurare shi ba a cikin hayyacin shi ya zalunce ta ba amma innaaaa sai k'ara sautin kukan ta take yi shi kuma bai fasa ba, sai da Suhaib da Sadeeq suka janye shi daga jikin k'ofan suka nufi site d'in su da shi.
     Daren ranar gabaki d'aya barci ya k'aurece musu kusan kwana zaune suka yi su duka balle kuma Aysha da koh alamar barci babu a idanun ta.

***********************************

Duk hanyar da Suhail ya san zai bi Aysha ta sakko daga fushin da take da shi ya bi amma koh alamar saukowa Aysha ba ta yi ba, b'angaren Suhaib ma hakan ya kasance dan ya yi magiyan har ya gaji amma inna ta k'i sauraran shi gashi a y'an kwanakin nan son ta ya gama mishi babban illah dan kwana yake yi yana mafarkin ta sometimes ma har jikewa yake,, babban abunda yake d'aga mishi hankali shine yanda tayi wani b'ulb'ul da ita ta koma tamk'ar irin fresh ajeboters d'in nan, ta wani clean kamar ba Aysha ta illu da ya sani a baya ba, hakan ya sa shi shan Alwashin muddin yana raye sai ya mallake ta, babbaratsalan shi d'aya yanda bros d'in shi ya gama macewa a kan ta, shi kuma a handa yake jin shi cire Aysha a zuciyan shi abu ne mai matuk'ar wahala.
     Duk da dai Aysha na sane da halin da kowannen su yake ciki amma koh kad'an babu alamar tausayin su a zuciyan ta.
    A cikin lokacin ne dad ya nema mata transfer daga makarantar da take ta nakasassu ya nema mata makarantar *Alhilal* ta garin Jos cikin sa'a kuwa js3 suka bata.
     Haka take tafiyan makarantan ta hankali kwance kullum dad shi ke kai ta ya d'auko ta, sosai take mai da hankalin ta kan karatu dan ajin shakkan ta suke dan bata kula kowa bayan kawayen ta Muhibba ana ce mata hibba, sai kuma Fatima ana k'iran ta teema.
    Sun yi k'aurin suna sosai a makaran ta saboda hazakan da kuma k'ok'arin su dan duk inda ka ratsa zaka ji ana cewa the triplets (Ashteehibb) sunayen da suka rada ma junan su kenan Ash, Aysha kenan, teema kuma tee, yayin da hibba suke ce mata hibb, bayan su ba su yarda wani ya k'ira su da sunan ba bayan inkiyan su.
     Wata Safiyar laraba ne Aysha ta fito cikin shirin ta na tafiya school, sosai ta sha kyau sai wani d'aukan ido take yi kamar yanda kuka san an k'era jikin ta da gold.
    Suhaib ne ya fito daga cikin gida za shi gidan granny dubo ta dan rabuwan shi da ita tun lokacin da suka je gidan ta da Suhail kwanakin baya kan maganar ta lallab'o mai su mum su hak'uru da fushin da suke da shi.
     Fitowan shi kenan eyes d'in shi suka sauka a kan Aysha da ke sanye cikin uniform d'in ta ta wani yin uban kyau da ita ga wani yala yalan gashin ta da ta tufke su wuri d'aya, duk da dai ba wani make up ne a fuskan ta ba amma sai ta bala'in yi mishi kyau sosai kamar ya sace ta ya gudu.
    Tsintar kan shi ya yi da yi mata murmushi ita kuwa ta wani d'aure fuska ta yafito shi da hannu ta d'aya, k'asa kin bin umurnin ta yayi jiki na rawa ya k'araso gaban ta yana washe baki kamar wani tsohon munafuki tace" k'anwata har kin fito kenan ??,
     "eehh" ta amsa mishi tana kakkau da kai kamar ta ga kashi lokaci guda tana aika mishi kallon wulakanci, please help me to upon this door na yi na bud'e but na k'asa", ta fad'a tare da pointing mishi jikin k'ofan motar.
    Da mamaki yake kallon ta saboda ganin sauyawan ta lokaci guda but sai ya dake ya b'oye mamakin shi yace"owk", ya fad'a tare da nufar k'ofan da take nuno mishi, murmushin mugunta ta yi mishi ta cije libs d'in ta na k'asa.
    Bud'ewan shi ke da wuya already ta samo macicin roba a wurin k'awar ta tasa macijin a motar tana ganin ya bud'e motar ta danna remote sai ga macuci ya tunk'aro wurin shi gadan dagan.
     Tsorata yayi sosai yana ja da baya ganin haka ta yi sautin ciro b'awon ayaba ta sa mishi a dai dai bayan shi, yana takawa sai ga shi ya zame tsuuuuuuuuuu ya fad'i k'asa timmmmm.
    Dariya ne ya kwace mata but sai ta masge ta marairace fuska tace ta yi wurin shi tace" sshhiittttt yaya na how comes ka fad'a k'asa koh baka rik'e handle d'in motar da kyau bane ? .
     Fusata yayi sosai dan ya fahimci tambayar rainin wayo ta ke mishi dan yana ganin santa take controlling macijin da remote sanda ya fad'a.
      A harzuk'e ya mik'e zai sharara mata mari fitowan dad kenan yayi sautin zuwa wurin su, ita koh daga nesa ta hange shi ta fasa ihuuu da k'arfi Suhaib yayi saurin janye hannun shi yana kallon ta da mamaki.
     Dad na isowa ya kwad'a mishi mari a birkice ya juyo ya dafe kuncin shi yana kallon dad, abun nema ya samu ta hau fidda kwallan munafurci cikin kissa tace" dad why is it dad brothers d'ina suke cuta ta ba sa k'aunar su bud'e ido su kalle ni a gidan na ?? could you imaging dad dan kawai na ce shi nake so ya kaini school yau wai na raina mishi hankali shine ya hau kwad'a min mari.
     Kallon ta ya tsaya yi cike da mamaki na jin irin sharrin da ta sharara ma dad, lallai makirci sai mata, abunda kenan ya fad'a a k'asan zuciyan shi.
     Ran dad ne ya bala'in b'aci yace" wai sai yaushe ku daina haukannan na ku ne, wannan wani irin zalunci ne haka, oyyya maza tun kafin a ji mu da kai ka yi abunda ta sa ka kuma ka kuskura ta dawo tace ka mata wani abun sai ran ka ya yi mummunan b'aci sakarai kawai.
     Jefo mishi key ya yi rai a b'ace yayi shigewar shi wata mota ya ja ya tafi.
     Suhaib kuwa ya d'au key d'in ya shige mota yana jiran ta shigo su tafi, sai da ta gama b'ata mishi lokaci kana ta shige back seat ta zauna instead of ta zauna a gefen shi.
    Hakan ba k'aramin k'ona mishi rai ya yi ba da sauri ya juyo yana kallon ta, zai mata magana ta wurgo mishi harara tsana tace" kad'an ma ka gani, u most pay for every thing you have done to me mtswwww. 

Pls share

*Sa'eeda✍🏻*
     ~Yar mutanen Dengi~

WAYE MACUCIWhere stories live. Discover now