Part 9

1.2K 75 0
                                    

🏵🏵☀☀🏵🏵☀☀🏵🏵
          *☀WAYE MACUCI☀*         
🏵🏵☀☀🏵🏵☀☀🏵🏵
        '''Suhaib koh Suhail'''

***********************************

® *REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS P.M.L*💭💭💭

_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_

# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
      
          
                       ©
'''Marubuciyar Rayuwar Sumayyah'''

    *SA'EEDA MUSA DAUDA😍*

'''Follow and ✅ote me on Wattpad''': *SaeedaMusaDauda*


*BESTORED TO MY LIL SIS* ''' SUMAYYAH MUSA DAUDA'''

  
      ~I'm back again my fans thanks you all for the best wishes yawan ku baya iya fad'uwa shi yasa nace bari na had'a jam'i na nuno muku tsantsar godiya ta lol i Sa'eeda Musa Dauda appreciated all your loved and prayers, much love my real fans Allah ya bar mu tare ya bani ikon sake faranta muku this time around,, my besty *Firdausi Muhammad Mainasara(Feeby)* you are also included thanks more and more,  Kawata *Rukayya( Nabeelat*) and *Lissa* kuma ban bar ku ba, fatan Alkhairi *Lipton*, and the rest that i didn't mention most especially my groups *Sa'eeda Musa Dauda's novel* and Waye *Macuci fans* i heart you all guys.~

                           9⃣

Treaning sosai coppers d'in suka sha dan tsabar wahala kad'an daga cikin su wand'an da tsoro da wahala yayi musu yawa na ta sakin fitsari tsiiiiiiiii a jiki k'amar k'ananan yara,,
     sai yamma lissss kana sojojin suka tashe su ba wai sun gama basu horon bane a'a sai dai dan ganin time is almost over,,
      su Suhail suna komawa d'aki suka fad'a wanwass a kan matras suna mai da numfashin wahala, almost 15 minutes suka d'auka a hakan kana suka mik'e suka had'a ruwan wanka su duka suka shige bathrooms saboda rage tsami da gajiya koh wannen su na ta jan uban tsaki saboda rashin saftar wurin,,
      Bayan sun kammala wankan sun fito ne Sadeeq yace" wai ni friend i saw you following a lady dama can ka san ta ne koh kuma yau ne kurum ka tab'a ganin ??
      iska mai zafi Suhail ya fuzar a bakin shi zuciyan shi na tafarfasa, jiki a sanyaye ya dubi Sadeeq yace" i'm sorry friend can't explain right now,,
      ganin mood d'in shi ne yasa Sadeeq yace" not too bad guy but you have to take heart cuz yawan sanya kan ka a cikin damu na iya haifar maka da matsaloli da dama, i know it most be something very important da yake damun ka a cikin zuciyan ka, please try to avoid sanya kan ka a cikin damuwa as i said it before,,
       with a worried face Suhail ya kuma kallon shi yayin da a zuciyan shi yake cewa" hmmmm, ta yaya zan manta da alhakin yarinyar da na cuta zuciya ta, could you imaging an innocent  handicap lady na destroying life d'in ta, shin da lalurar ta zata ji koh kuma bak'in cikin cutan da na d'and'ana mata though dai na san cewa it wasn't my fault", a fili kuwa ya saki sassanyar ajiyan zuciya yace" alright friend i appreciated all your loved and carings over my conditions, have it been friend where like you da al'ummar duniya zasu kasance most trustworthy ",,
       don't mention dear you deserved more from me dan ka fi k'arfin friendship a wuri na cuz i took you as my biological brother, any ways let's pray and later on prepare something to eat ka san since morning rabuwan mu da abinci,,
      mik'ewa Suhail yayi kana yace" oyyaaa let's go and perform Asar prayer, a tare suka yi alwala suka nufi  masallacin  dake unguwan suka bi jam'i,,
    bayan sun idar da sallar ne suka koma d'akin Suhail suka shirya lafiyayyen jelof d'in taliya wanda ta sha kifi da yankan nama k'anana suna ci suna tab'a hira sama sama, basu wani dad'e da cin abincin ba aka fara k'iraye k'irayen sallar Isha'i, a hanzarce suka kuskure bakin su dan dama can da alwalar su suka wuce masallacin, bayan sun idar da sallan ne suka sake komawa d'akin Suhail, sai da suka yi hira sosai kana Sadeeq yayi sallama da friend d'in na shi ya koma lodge d'in da yake zama cuz a can d'in yayi niyar, but almost half of Suhail's mind was not with Sadeeq at all a time d'in da suke hirar,,
      Sadeeq na fita Suhail ya runtse idanuwan shi kaman mai yin barci alhali kuma ba barcin yake yi ba, tunani ne yayi mishi katutuuuu a zuciyan shi, kasancewar ya dawo da tarin gajiya mai yawa bai san lokacin da barci b'arawo yayi awun gaba da shi a daren ba ,,
     
        Da daddare around 8:15 Aysha na kwance a kan gadon ta, tunanin maganar da ya Abdallah ya fad'a mata ne yake ta yawo a zuciyan ta, wani irin tashin hankali ne mai tsanani ya bala'in kama ta, ji take tamk'ar ta had'iye zuciya ta mutu idan ta tunano maganar da yayan nata ya fad'a mata na cewa yana son ta bayan ta san irin tarin kiyayyar da mahaifiyar shi ke nuna mata, bugu da k'ari kuma wannan *Macucin* da imani yayi mishi karanci a zuciyan shi ya k'eta mata haddi ba tare da ya tausaya ma halin da take ciki ba,,
       hawaye masu d'umi ne suka fara bin fuskan dan tunawa da cewa ba k'aramin illa bawan Allah nan yayi mata ba, wani irin k'ullutun bak'in ciki ne ya tok'are mata zuciya,,
       tana wannan hali ne inna Larai ta shigo da guntuwar sallamar ta mai kama da ta tsoffin munafukan matan nan, da yake inna ta shirya salon munafurci ta zauna a gefen Aysha tare da taping d'in ta tace" taso ki ji wata maganar arziki da ta same mu kin ji Aysha ta" ??
      mamakin jin karshen maganar da inna larai ta fad'a ne ya kama Aysha dan jin cewa da tayi wai" Ayshan ta", a heart d'in ta tana cewa" ta yaya yaya na zama Ayshan ta ohhhoooo bayan irin kyamar ta da take nuna min da kuma tsana ta,,
     ba dan ta so ba ta fara juye juye tana k'ok'arin tasowa, garin juye juyen nata ne bata sani ba tayi bakin gado sai ga ta fad'a timmmmm a k'asa,,
       da yake inna ta san da cewa Aysha bata iya ganin ta zund'e ta fara yi mata tare da mata gwaliyo a zuciyan ta kuma tana cewa" Allah ya k'ara shegiya munafuka kawai", gudun kar Aysha ta fahimci wani abu ne ya sa da sauri inna tace" Subahanalillah taso y'ata ai da na san hakan zata faru da tuni na taimaka miki da kaina kin taso", ta k'are maganar tare da marairaice fuska lokaci guda tana yunkurin d'ago ta,,
     Aysha kam bata ce komai ba illah mamakin da ya dad'a kama ta ganin yanda inna take wani tarairayar ta har da ce mata "sannu" kamar yau ne ta fara ganin ta fad'a a gaban ta bayan ta san cewa sometimes ita ce ke saka mata k'afa ta fad'i koh kuma ta yi mata abunda ta san zai iya cutar da ita,,
       gaban Aysha ne ya fara beating dan ta san haka kurum inna ba zata tab'a jin tausayin ta ba,,
      Jin maganar da inna ta fad'a ne ya doke dodon kunnuwan ta, ba komai bane inna ta fad'a illa cewa da tayi"Aysha taso Ilu na k'iran ki a waje ga sadar ki nan  da na kwato a wurin ki na taho miki da ita, yanzu sai ki hanzarta ki taso da sauri kar yayi ta zaman jiran ki".
    Hantar cikin Aysha ne ya fara kad'awa a d'an tsorace kuma fuskan ta na bayyana tsantsar mamaki da kuma tashin hankali ta dafe k'irjin ta da hannayen ta biyu  tace" wanene Ilu kuma inna da har zai zo wurina da daddaren nan ba dai d'an gidan malam sabo mak'ocin mu ba wanda na ji mutane ke cewa yana fama da lalurar kuturta sannan kuma yana biye biyen mata" ??
       washe baki inna Larai tayi dan ta san cewa" mahaifin Ilu mai kud'i ne sosai dan kaffff unguwar su babu wanda ya kamo k'afan shi a kud'i balle ya fi shi,,
    cikin tsigar lallashi inna tace" kwarai ma kuwa shi nake nufi, ki kwantar da hankalin ki yarinya na san matsalar ki bata tab'a wuce ta lalurar shi, yooo in banda abun ki ma menene na wani d'aga hankali bayan kin san cewa duk unguwar nan shi kad'ai yafi dacewa da ke tunda dukan ku nakasassu ne, kenan babu yanda zai ai ya wulakan ta ki bugu da k'ari kuma koh ban fad'a miki ba na san cewa kin samo labarin irin tarin dukiyan da mahaifin shi ya mallaka, kin ga yanzu muddin kika amince aka yi abinnan hankali kwance kakamu ta yank'e saka dan mu duka zamu ci ribar arzikin su, muna daga kwance sai abunda muka ga daman yi ga kud'i nan birjikkkkk,  maza maza taso da kai na zan miki jagora har zuwa wurin Ilu dan ban bari ki jaho min hasara ina ji ina gani daula ta wuce ni,,
     bak'in ciki ne ya gama kama Aysha ji take yi gaba ki d'aya ta tsana kan ta da ma duniyar ma gaba ki d'aya, ita kenan babu kwanciyar hankali a zuciyan ta sai tarin bak'in ciki na yau daban na gobe daban",,
     ba tare da ta bi umurnin inna Larai ba sai ta kama zancen zuci tana cewa" Ya Ilahi ni Aysha ina zan tsoma kaina na ga haske ne, ashe haka duk nakasasshe yake ji a rayuwar shi, gaba ki d'aya ya koma cikin kunci da tak'ura ??,  yanzu dubi matar da take cewa kar na kuma tab'a mata randar ruwan ta saboda kar na shafa mata nakasa, amma saboda tsabar son kud'i tana wani lallab'a ni, koh dai ta manta cewa har yanzu ina tare lalular da take kyama a jiki na??,,
     zufa ne ya fara k'aryo mata a take jikin ta ya fara b'ari a sakamakon wani uban zazzab'i da yake nema ya rufe ta from no where,,
      da kyar ta iya bud'e baki cikin kwantar da murya  tace" haba inna ta yaya zaki yi yunk'urin had'a ni da Ilu bayan kin san cwa bai dace da ni ba, wallahi ba wai nakasar tashi ce tafi damuna ba,  kowa a unguwar nan ya san cewa Ilu tataccen d'an iska ne, da kud'in uban shi yake yaudaran bayin Allah ya aikata d'anyen aiki a kan su,,
      "dan Allah rufe min baki munafukar banza" inna ta fad'a a hasale kana ta d'ora da cewa" da kike cewa shi d'an iska ne wa ya kai ki iskanci ke da kika bin lungu da sak'o kina bin gidan samari kina fakewa da cewa kin je neman maula ki ta tsula tsiyar ki, toh bari ki ji na fad'a miki dole ki fita wurin shi zance kuma maganar aure na nan daram ba gudu ba ja da baya kamar an yi an gama da yardar Allah dan ban bari haka kawai ina ji ina gani ki min hassada arziki ta wuce ni,,
      kwakkwaran motsi Aysha ta k'asa yi, wata irin arniyar tsawa mai firgitar wa inna Larai ta d'oka mata, a rud'e Aysha ta fara lalumo abun da zata rik'e ta tashi cikin ikon Allah hannun ta ya sauk'a a kan sandar ta da inna ta kawo mata, da sauri ta d'auka tana dogarawa a k'asa har ta fice daga d'akin inna Larai na bin ta da masifa a baya har suka iso wurin shi,  suna isowa inna ta dakatar da ita gudun kar ta wuce shi tunda ba wai gani take yi ba,,
     shi kuwa gogan na ka yana ganin ta ya wani washe baki yana maganar su ta kutare yace" Shatu ta an taho tarbar masoyi ne haka"??, ba tare da ta ce mishi komai ba     ya juyo wurin inna Larai ya ciro kud'i a aljihun shi yana maganar kutare yana kai hannu hanci yace" gaskiya inna Larai na gode kwarai da kika kawo min indo ta, ya mik'o mata kud'i yace" amshi wannan k'irga ta nawa ne a wurin"??,,
    ganin damin kud'in da ya zaro a aljihun shi ya dad'a sa inna shan alwashin sai an yi auren Ilu da Aysha matuk'ar tana raye,,
      da yake son kud'in ta yayi ma inna Larai yawa jiki na kyarma ta k'arb'a ta fara k'irgawa tana washe baki kaman an bata wankan gardi, tana gama k'irgawa tace" dubu Ashirin ne ciffff angon shatu",,
     "Mik'o min nan",  ya fad'a yana k'ok'arim amsa daga gare ta, garin amsar kud'in ne ya dadumar hannun ta a rashin sani"
     "kai ka kai haba Ilu wannan wani kalan sabon iskan ci ne haka ai koh ba koma ka bari na mik'o maka da kaina na ba wai ka tab'a min hannu da nakasassun hannayen ka ka, taja tsaki mtssssss kana ta d'ora da cewa" wallahi kuturu bai yi ba a rayuwa, cewar inna kenan a masifan ce",,
       ran shi ne ya b'ace sosai cikin b'acin rai yace" tabbasss kuturu bai yi ba, kin ga gara kurum na maida kud'i na aljihu na wata k'ila gaba zasu min amfani, Allah sarki kuturu bayan Allah ana son kud'in ka ana kyamar ka", Ilu kenan yake fad'a yayin da yake k'ok'arin mai da kud'in shi a aljuhu,,
    ganin cewa da gaske yake yi idan bata yi wani abu ba zata ma kanta tsakiyar da ba ruwa, da sauri ta tare shi wannan karon harda damke hannun shi da hannayen ta biyu, saboda tsabar son kud'i har ta manta cewa yanzu ta gama yi mishi mashifa akan ya tab'a mata hannu,,
      jikin ta na b'ari ta marairaice fuska cikin k'arye  murya tace" haba Ilu dan gidan Alhaji Mudi angon indo ai ba'a yi haka ba, ba zaka d'and'ana min zuma a baki na ka bar ni haka ba wallahi subutar baki ne, kar ka manta cewa da kuturu da lafiyayye duk halittar Allah ne fa ,,
      Jin yanda take kod'a shi gaban shatutuwan shi ya sa shi fiddo kud'in ya bata yana dad'a washe baki yace" daga baya kenan Larai, ya bude hannayen shi irinta wanda sai yi washe ma kan shi yace" hohohooo sai ni na shatutuwa ikon Allah ba gaba da gaba ba koh ta baya ka zo min sai ka shirya", duk abubuwan da yake fad'a yana yi ne yana kai hannu hancin shi irin yanda kutare ke yi,,
     da murnar ta ta amsa tayi cikin gida tana zubo mishi k'irari har ta b'ace,,
      Aysha na jin su kamar ta kashe kan ta huta dan bak'in ciki, Ilu kuwa ganin ina ta b'ace ya rungumo Aysha yana tab'a mata jiki yace" taho na ji d'umin ki amarya ta kin san banda hak'uri ni dai dan kaffff y'an mata babu wanda nake so kamar ki shi yasa kika ga nace akan zan aure ki",,
     wani irin k'arfi ne ya zo mata da ba ta san tana da shi ba,  da k'arfi ta ture shi daga jikin ta tace" wa'iyazubillah Ilu iskan cin naka har ta baro tantiran y'an matan ka ta koma kai na ??, wannan was d'abi'a ce haka",,
      dad'a matsowa gare ta yayi ya sa kutaren hannayen shi ya dad'a rungumo ta yace" haba indo ta mai yasa kika fad'a haka ne kam bayan kin san auren ki zan yi, to menene dan munyi soyayyar shan minti da ke,  da dai na ce ki ban kan ki ne sai ya zama wani abun amma d'an wannan abun ai kya bar ni na rab'e ki dai koh",,
      wani irin tsanar shi ne ya kama Aysha a tsiwace ta hankad'a shi daga jikin ta tace" tirrrr da halin ka, muddin ka kuskura ka sake zuwa wurina sai na shayar da kai ruwan mamaki, tana gama fad'a tayi hanyar shiga cikin gida cike da b'acin rai,,
         da sauri ya nufo ta cike da mugunta ya kwace sandar ta ba tare da ta kula shi ba ta fara lalimo garu da hannun ta burin ta kurum ta samu ta shige cikin gida.
      bin ta yayi a baya yana cafko mata boobs, idan ta canza direction ya biyo ta tana zagin shi yana kwasan uban dariya kamar ya samu catoon yana dad'a cafko boobs d'in ta,,
       wasu sabbin hawaye ne suka wanke mata fuska, gero mishi Allah ya isa take ta yi wane cikin kwando shi kuwa gogan naka yana dad'a bin ta ya tab'a mata na shanun ta,,
      Ya Abdallah na daga majalisa yaji gaban shi ya yanke ya fad'i raaasss, da sauri ya dafe zuciyan shi yana mai karanto addu'o'i, ba tare da gaban na shi ya daina fad'iwa ba illa tsanan ta beating d'in da yake yi a kai a kai,,
     d'aya daga cikin abokan nashi ne mai suna Hafiz ya lura da yanayin shi, da mugun mamakin ganin dai lafiya lao suke zaune amma kuma sai lokaci guda ya canja mood d'in shi,,
      a sanyaye ya dafe kafad'an ya Abdallah fuskan shi na bayyana alamar tambaya yace" lafiya dai koh abokina na ga lokaci guda yanayin ka ya canja ??,,
    murmushin yaken da yafi kuka ciwo ya Abdallah yayi kana yace"  hmmm  wallahi aboki na ni kaina ban san dalilin hakan ba, kawai dai na ji zuciya ta ce ke tsanan ta fad'uwa kamar dai wani abu na shirin faruwa da ni ne",,
       Asha ya kamata ka koma gida ka huta hirar tayi haka nan, taso ma na raka ka gidan,,
     jiki lakwas ya Abdallah ya taso suka nufi hanyar zuwa gidan su Aysha da addu'o'i kala a d'auke a bakin shi,,
     suna zuwa dai dai kan kwanar gidan Hafiz ya tsaya kana yace" toh ni na gama maka tawa rakiyar zan koma daga nan dan ka san yau hirar mu ta dandali tayi dad'i sosai bana so ta wuce ni",  ya Abdallah yace" shikenan abokina na gode da kulawar ka gare ni",  daga nan suka yi sallama yayi shigewar shi,,
     yana shawo kwanan gidan su Aysha gaban shi ne ya yanke ya fad'i rasssss dan ganin haske macin ya haska mishi Ilu da yana ta cakumo boobs d'in Aysha yana dariya kamar irin ya samu abun wasa dan sai jujjuya ta yake yi tamkar kwallo,,
     daga inda yake yana iya hango tsiraren hawaye a fuskan ta,,
     a take ya fara ganin wuri na mishi dishi dishi, ai kuwa bai san lokacin  zuciya ta kawo shi iya wuya ba a kufule yayi wurin su ya damk'o Ilu yana fadda hucin bak'in ciki kamar wani mayunwacin zaki,,


       *Please*
'''Share'''
'''Vote'''
'''Comment'''

*Sa'eeda✍🏻*
        ~Y'ar mutanen Dengi~

WAYE MACUCIWhere stories live. Discover now