🏵🏵☀☀🏵🏵☀☀🏵🏵
*☀WAYE MACUCI☀*
🏵🏵☀☀🏵🏵☀☀🏵🏵
'''Suhaib koh Suhail'''***********************************
® *REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS P.M.L*💭💭💭
_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_
# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
©
'''Marubuciyar Rayuwar Sumayyah'''*SA'EEDA MUSA DAUDA😍*
'''Follow and ✅ote me on Wattpad''': *SaeedaMusaDauda*
*BESTORED TO MY LIL SIS* ''' SUMAYYAH MUSA DAUDA'''3⃣1⃣
A d'an zaman da Aysha tayi da Suhail a hospital ba k'aramin shak'uwa suka yi da ba dan almost every day yini yake yi cuurrr a wurin su sometimes ma sai mum tayi da gaske kana ya koma gida, kamar yanda suka shak'u da juna zukatan su ma haka dan idan babu d'ayan su ji suke tamk'ar they are missing part of them saboda kad'aici da zasu tsinci kan su a ciki.
Tsakanin Suhail da d'an uwan shi kuma abu sai dad'a gaba yake yi dan babu wata kyakkyawar alaka a tsakanin su dad'in dad'awa ma abunda ke dad'a ingiza rashin jituwa a tsakanin su kuwa shine kwata kwata Suhaib baya son ganin yanda d'an uwan shi ke zuga uban rawar k'afa idan za shi wurin Aysha a asubiti sai ya ji wani irin k'ullutun b'akin ciki ya tokare mishi mak'ogoro, ya kuma nemi natsuwar shi ya rasa.
Yau ma kamar kullum bayan Suhail ya taking bath ya fito daga bathroom yana taje suman kan shi Suhaib ya shigo d'akin bakin shi d'auke da sallama, ciki ciki Suhail ya amsa mishi kamar wanda bai son yin magana, sanin muhimmacin sallamar ne yasa ya amsa mishi da babu abun da zai sa ya amsa mishi,,
Shigowa Suhaib yayi ya saki y'ar k'ara "wash" a dai dai lokacin da yake zama a kan one seater d'in parlourn cikin gatse ya dubi Suhail yace" yau ina zaka kuma rival d'in kuturu koh dai dubiya za'a" ba'a fad'a min ba ?.
Maganar da Suhaib ya fad'a sosai ya haddasa ma Suhail b'acin rai dan shi bai ga dalilin da yasa zai k'ira shi rival d'in kuturu ba, ban da rainin sense how many times yake barin gidan ba tare da sanin shi ba,
banza da shi Suhail yayi dan ya san salon neman magana ne da cin fuska,,
wayar shi ce tayi k'ara alamar incoming call ta shigo, bin inda wayar take yayi kallo kana ya d'auke kan shi ya ja guntun tsaki cuz baya son distraction he taught it was Zee that calls him,,
ba tare da ya damu da ya d'aga ba ya ci gaba da abunda yake yi, ganin call d'in ya kuma shigowa ne yasa shi jan tsaki a k'aro na biyu ba dan ya so ba sai dai dan ya gaji da jin k'arar wayan ya nufi inda wayar take da mood d'in alamar mutum ya k'osa da jin k'iran ya d'au wayan yayin da Suhaib ya bi bayan shi da harar k'asan ido lokaci guda yana tab'e baki.
Ganin suna wanda ke k'iran ne yasa shi sakin y'ar karamar smile har ya d'an samu relief a zuciyan shi cikin sauri ya picking tare da manna wayan a kunnen shi yayi sallama daga d'aya b'angaren aka amsa.
Sai da suka gaisa kana Suhail yace" friend how far two days ka b'uya abun ka wai ina ka shiga ne kana min rowar kan ka, koh sai na bada cigiyar ka a gidan radio ne kan na gan ka ?"
Dariya sosai Sadeeq yayi yace" see you ni zaka ma sharri bayan kan ka shaida ne kan cewa ka fini wuyan gani dan koh a wayan ma da kyar na samu ka d'aga".
"Ummmmm baza ka gane bane friend i have some issues ne shi yasa ka ga bana neman ka and wasu lokuta ina ganin missed calls d'in ka bana samun daman picking call d'in ka talk less of calling you."
'''Subahanalillah''' friend don't tell me cewa har yanzu baka cire tunanin yarinyar a zuciyan ka ba, why didn't you take it as part of your destiny cuz ya kamata zuwa yanzu you dealt with this issue " cewar Suhail a tunanin shi koh the main sourse of his friend's problem shine fyad'en da ya ma yarinyar da ya bashi labari ne a Dengi not knowing that his twin brother contributed a lot in giving him headache.
Da yake Suhail ya gano abunda Sadeeq yake nufi cikin dakiyar zuciya yace" Hmmm this is a different issue shi yasa kaga tun farko na ce ma baza ka gane ba cuz it needs much explanations".
Dogon ajiyar Zuciya Sadeeq ya sake irin ta relaxations yace" Owk dama i called ne dan naji lafiyar ka tunda baka nema na gashi ni kuma ba zan iya fushi da d'an uwa kuma amini na ba shi yasa kaga na k'ira".
Cikin jin dad'i Suhail yace" wow i'm so proud of you and i so much loved it been seeing ma self close to you fried, you are such a kind of person that i couldn't think some one will replace your position in my heart as d'an uwa kuma amini na", da gayya ya fad'a hakan dan ya b'ata ma Suhail rai dan ya san tun sanda suke kids basa tab'a yarda su fifita son wani a kan d'ayan su,,
hakan kuwa ya faru dan sosai Suhaib ya shak'a iya wuya cikin tsananin b'acin rai ya hau biting libs d'in shi har suka soma jini amma saboda tsananin b'acin rai bai damu da hakan ba,,
Cikin wayar da suke yi Sadeeq yace" oohhh realy ? so if really you mean what u said ina expecting d'in ka a gida any time, so bye for know cuz ummi ta min aike and i have to deliver it,,
"Owk dear ba case but please extend my regards to her before i come", Suhail ya fad'a.
Daga d'ayan b'angaren Sadeeq yace" own woooo your wish is my command dan haka sai na gan ka kawai ina zuba eyes".
A tare suka yi sallama koh wannen su ya katse wayan shi cike da kewan d'an uwa shi.
Bayan Suhail ya gama wayan ne a gurguje ya shirya ya fito daga gidan ya d'auki hanyar asubiti, da isowan shi ya tarar da Aysha dan ita kad'ai ce a d'akin ta lumshe eyes d'in ta kamar mai jin barci,, dan mum ta tafi office d'in Doctor dan ya duba lafiyar Aysha cuz tun d'azu ta zuba ido koh zata gan shi gashi kuma its getting late,,
Jawo stool yayi ya zauna a gefen ta ya zuba ma halittar fuskan ta ido yana kallon baiwan kyau da Allah yayi mata dan k'aryar maharada su kushe ta.
Jikin ta ne ya bata ana kallon ta saurin dafa bango tayi ta taso ta zauna da mazaunan ta tana tambayar wanene ya shigo.
Sautin daddad'an voice d'in ta da ya jiyo ta kamar ana busa sarewa da kuma yanda lips d'in ta ke kad'awa a hankali a hankali ya bala'in tafiyar da immanin Suhail bai ankara ba sai jin muryar ta yayi tace" yayana na san kai ne ka shigo ka bayyana min kanka dan jiki na na bani cewa kai d'in ne".
Tsadadden smile ya sakar mata wanda sai da sautin shi ya fito yace" k'anwata kenan ashe zaki iya gane yayan naki gaskiya you realy surprises me".
"Hmmmm yaya na kenan ai dole na na gane ka saboda a cikin kwanakin nan ji nake kamar na fi shekara guda da sanin ka, kar kayi mamaki idan nace maka k'amshin turaren ka kad'ai ya isa ya bayyana min cewa kana kusa da ni.
Sosai ya ji dad'in kalaman ta dan shima same abunda take ji game da shi haka yake ji game da ita,,
Rik'o hannun ta yayi wani irin shock suka ji a gab'ob'in jikin su su biyun tamk'ar an jona electric charged sakamakon had'ewan da hannun su yayi su duka har numfashin su na shirin d'aukewa most especially Suhaib da yaji wani irin abu ya tsirge b'argo da gangar jikin shi tun daga tsakiyar kan shi har zuwa tafin k'afan shi da sauri yayi saurin sakin hannun ta ya daidaita nutsuwar shi yace" ke ta dabanne ce k'anwata bana had'ashi da na kowa i'm grateful and the most luckiest to have you as a sis".
Duk da dai bata san abunda k'arshen maganar na shi ke nufi ba but sai ta tsinci kan ta da jin dad'in kalaman shi,,
haka dai suka yi ta fira yana d'ebe mata kewa yana bata labaran duniya masu ban dariya har mum ta shigo ta tarar da su a haka itama ta joining d'in su aka yi firar da ita.
Sai k'iraye k'irayen salar Magrib yayi sallama da su mum ya wuce gida ya gabatar da sallah tare da haurawa site d'in su koh ta kan abinci bai tsaya ci ba ya kwanta ya rufa idon shi yayin da abubuwa da dama suka ta yi mishi yawo a zuciyan shi.
Bai san me yasa ba a y'an kwanakin nan tunanin Aysha ya addabi zuciyan shi son ta da k'aunar ta ke ratsa shi yayi yayi ya cire ta a ran shi abun yaci tura, fargabar shi d'aya yanda dad ya ma Aysha alk'awarin aure da wani kenan yana shirin rasa ta a rayuwar shi kenan.
"Ohh Allah help me out ya fad'a tare da matso hawayen da suka cicciko a eyes d'in shi. Daren ranar da kyar ya runtsa.
B'angaren Aysha ma hakan ta kasance dan sai juye juye take a kan sickbay ita kad'ai mum na lura da yanayin da sai da ta but sai ta nuna kamar bata san ma abunda take yi ba.
*Washe gari*
YOU ARE READING
WAYE MACUCI
Historical FictionLabari ne a kan wata mak'auniyar Allah mai suna Aysha wacce take soyayya da yayan ta amma kwatsam sai wata tsautsayi ya afka mata har hakan ya saka ta cikin bakin ciki,ba tare da ta bayyana mishi ba sai daga baya ya fahimci halin da take ciki a tsan...