Part 8

1K 92 0
                                    

🏵🏵☀☀🏵🏵☀☀🏵🏵
          *☀WAYE MACUCI☀*         
🏵🏵☀☀🏵🏵☀☀🏵🏵
        '''Suhaib koh Suhail'''

***********************************

® *REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS P.M.L*💭💭💭

_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_

# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
      
          
                       ©
'''Marubuciyar Rayuwar Sumayyah'''

    *SA'EEDA MUSA DAUDA😍*

'''Follow and ✅ote me on Wattpad''': *SaeedaMusaDauda*


*BESTORED TO MY LIL SIS* ''' SUMAYYAH MUSA DAUDA'''

   

                          8⃣

             *Cigaban Labari*

         Sai da ta ci kuka iya isan ta kafin ta tsagaita tare da share hawayen da suka subo mata, tana so ta d'ebo ruwa ta yi wanka but tsoron masifar inna ya hana ta,,
       Da kyar ta iya satan jiki ta d'ebo ruwa ta shiga band'aki ta tsarkake jikin ta kasancewar da najasa ta kwana,,
      Tana fitowa taji muryar ya Abdallah yana ta surfa ruwan bala'i a tsakar gida, bata san ko mai yake fad'a ba tayi shigewar ta d'aki, da kyar ta iya nemo kayan da zata saka sannan ta shafe jikin ta da man shafawa Vaseline ta sannan kuma ta saka kayan.
       Jim kad'an sai ga shi ya shigo d'akin ta ya iske ta a kan kado tayi tsiiiiitttt da ita kamar mai tunani da alama bata san da shigowan shi ba.
        Zama yayi a gefen ta kad'an ya zubo mata ido k'irrrrr cike da tausayin ta can ya saki ajiyar zuciya yace" k'anwata ina sandar taki take d'azu na hango ki babu ita a hanun ki shin bakya tsoron ki sake fad'owa a ramin koh koma tsautsayi ya sanya tsantsi ya d'ebo ki ki fad'i ??
       A firgice ta dawo hayyacin ta tana cewa" uuummm uuummm" dan jin maganar shi cuz bata ji motsin shigowar shi ba,
       Hmmmmmm Aysha kenan bana so ki sanya wata damuwa a ran ki game da abun da na fad'a miki d'azu, abunda nake so da ke shine ki ammince da bukatata kawai ayi abun nan, duk wannan tunanin nan da kika fara saka kanki a ciki baza su k'are ki da komai ba illah tashin hankali da kuma bak'in cike da kike dad'a sanya kan ki a ciki , ya jim kad'an domin ya bata daman da zata ce wani abu yayin da a zuciyan shi yake rokon Allah akan ta amince da shi.
      Sassanyar aziyar zuciya ta sake kana tace" har yanzu baka fahimci inda na dosa ba ya Abdallah sanin kan ka cewa maganar da ka zo da ita ba mai yihuwa bace ba, ka taimaken ka janye kudurin ka idan ba so kake ka jefa zuciya ta cikin matsananciyar tashin hankalin da tafi wacce nake ciki ba,
       Dafe kai yayi da k'arfi ya furta "Subahanalillah" Aysha soyayyar tawa kike k'ira da tashin hankali, shin kin san yanda son ki  da kuma k'aunar ki ke d'auwaniya da ni ??, ya d'an sassauta muryar k'asa k'asa yace" please k'anwata ki taimaka ki sama min gurbi a zuciyan ki, ki sama min gurin zama a cikin ta koh da kad'an ne,, na bar ki lafiya sannan kuma ina saurarar amsa ta idan kin gama nazari,, yana gama fad'a ya fice ya bar ta koh wa da  abubuwan da yake sakawa a zuciyan shi.
        Yana fitowa waje direct k'ofan fita daga cikin gidan ya nufa da isowan shi ya d'auki hanyar majalisar su,  a hanhar ta shi ne ya hango wad'an su masu baro guda biyu nan ya k'ira su yayi musu bayanin aikin da zasu mishi suka yi ciniki ya biya su, a tare suka nufi gidan su Aysha nan ya nuno musi ramin suka cike ta tasssss da yashi kafin nan suka five shima ya bi bayan su.
     B'angaren Suhail kuwa babu irin neman da bai yi mata ba Sadeeq na taya shi duk da cewan bai san dalilin yin hakan ba but ya san halin friend d'in nashi dole sai da wani muhimmin abune ya sa yake neman ta,,
      Rashin ganin ta ba k'aramin d'aga mishi hankali yayi ba yana ji yana gani haka ya hak'ura suka ci gaba da tafiyan su har suka iso camp, suna isowa suka ga sojoji birjikkk sun saka wad'an su copper hawan igiya, wad'an su na pareti yayin da sauran ke ta training masu matuk'ar wahala sojoji na bin su da bulala duk wanda ya tsaya su zane shi,,
      daga inda suke suka jiyo muryar wani soja yace" heee you late comers come here",,
      Ai kuwa da mugun gudu suka yi wurin shi da isowan su yace" join that queue my friends, ai kuwa kafin ya gama rufa baki har sun shigo layin wanda zasu kwanta da baya a k'asa  a aza musu k'arfe su d'aga sama da hannayen su


_'''Manage please

    Gaskiya duk groups d'in da nake ciki idan bana ganin comments wallahi zan yi left cuz na fara gajiya da magana idan yaso duk wacce take son cigaba novel d'in ta bini private ta min magana zan dropping number na a kasa na adding d'in ta a group d'ina mata zallah please banda maza.'''

 

Vote
Share
Commet

     
08036424738

*Sa'eeda✍🏻*
        ~Yar mutanen~

WAYE MACUCIWhere stories live. Discover now