® *REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS P.M.L*💭💭💭
_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_
# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
©
'''Marubuciyar Rayuwar Sumayyah'''*SA'EEDA MUSA DAUDA😍*
'''Follow and ✅ote me on Wattpad''': *SaeedaMusaDauda*
*BESTORED TO MY LIL SIS* ''' SUMAYYAH MUSA DAUDA'''Ina bama d'aukacin masoyana hak'uri a bisa rashin jina da suka yi kwana biyu wallahi rashin lafiya ce ta kama ni har ta kai bana iya hawa online balle na samu daman typing but na samu Sa'eeda yanzu insha Allah zan d'ora daga inda na tsaya da yardar Allah zan dinga kwatanta yi muku typing every day but insha Allah ba zan yi delaying d'in ku more than a day ba (koh wani bayan kwana d'aya). Much luv
5⃣—6⃣
A take zufa ya fara k'aryo mishi ta koh wani b'angare na jikin shi cikin tsantsar rud'ewa ya bi bayan ta cuz he need to know koh ita din wacece dan ya nemi yafiyar ta cuz a yanda muryar ta take tamkar ta yarinyar da ya ci mata zarafi ne,, gefe guda yayin da abokin ya yi mutuwar tsaye zuciyan shi cike da tarin al'ajabin abunda friend d'in na shi ke shirin yi.
Har yayi steps wayar shi ta fara ringing,, cakk ya ja ya tsaya domin amsa call d'in at the same time ya d'auke idanuwan shi a kan ta,, a sanyaye ya ciro wayan a pocket d'in shi,, ganin mai k'iran ne yasa murmushi ya sub'uce mishi, cikin tsantsar farin ciki ya d'aga wayan yana cewa" Assalama'alaikum bros yaya kake an tashi lafiya, yaya su dad da mumcy hope dai kuma lafiya??", a jere ya yi tambayar ba tare da ya bari wanda ya k'ira ya amsa.
Daga d'aya b'angaren aka amsa da cewa" Ameen wa'alaikummussalam lafiya lau bros hope dai you are done with the service??. Suhail ya tab'e baki yace" uhhmmm not yet bros but a cikin kwanakin nan zamu gama insha Allah ka san abubuwan ne sai a hankali,, but i will not tell you the exert date, ya k'arasa fad'a tare da d'aga girar shi sama kamar wanda yake waya da shi yana ganin shi.
bros d'in nashi yace" owk wooo shikenan but na san cewa you wanted to surprise us ne, any ways bye dama i called to confirm ne cuz we eager to see you cuz we missed you a lot and we wants you close to us, lumshe idanuwan shi yayi saboda dad'ad'an kalaman d'an uwan na shi da ya doke dodon kunnuwan shi,, a hankali ya bude su yana mai sauraran maganganun nashi.
Bayan sun gama wayan Suhail ya katse wayan shi zuciyar shi fallll farin ciki ya saka ta a pocket d'in shi a take ya fara tunano Aysha da sauri ya mai da idanuwan shi a kan hanyar da yake tunanin zai gan ta amma kuma kashhhh sai ya ga wayam babu su babu alamar su,, cikin bak'in ciki ya dafe kan shi yace"ooohh ssshhhhhtttt how comes na bari ta b'ace min ne, da i could have follow them dan na confirming koh ita d'in ce,, jiki ba laka ya juyo da baya ya nufo wurin da friend d'in shi da ke dask'are a wuri daya, ba tare da sun tanka ma juna ba suka fara tafiya a tare.
Bayan su Aysha sun iso gida da taimakon Humaimai ta samu ta juye ruwan a randar inna Larai tana juyewa tana fitar da hak'i saboda tsabar gajiyan da ta yi kasancewar daga rafin zuwa gidan su a kwai y'ar tazara mai yawa.
Inna Larai ce ta fito da y'ar wak'a a bakin ta tana yi tana murgud'a mazaunai irin ta tsofaffin y'an bariki d'in nan tana ganin su Aysha ta had'e rai tace" lallai yarinyar nan da munafurci kike wato dan na aiko ki d'eban ruwa dan salon munafurci shine bari ki nemo y'ar jagora salon mutane su ce ina cutar da ke koh??, ta fad'a tare da k'araso wurin ta ta rik'e kunnuwan Aysha da k'arfi ta murd'a cike da mugunta dan har sai da kwallan radad'in azaba ya zubo ma Aysha, cikin rashin rausayin ta tace" kina dai ji na koh??, murya na rawa Aysha tace"eh", inna larai ta ja kwafa tace" to daga yau na saka ki aiki kika nemo taimakon wasu sai na ci uban ki da duka wallahi kin ji dai na fad'a miki sakarai kawai oyya b'ace min da gani tun kafin rai na ya b'ace dan kema kin sani ba za mu rab'u ta dad'i ba, a duburburce Aysha ta fara tafiya tana nemo hanyar da zata bi da hannun ta cikin rashin sa'a tana tak'o kafan ta ta b'urma wata uban rami da k'arfi ta fasa wani razanannen ihooo Humayrah tayi kan ta da gudu cikin tsantsar rud'ewa,,
runtse idanuwa Aysha ta yi dan ta san wannan aikin inna Larai ce hankali a tashe ta fara nemo haryar da za ta fice a ramin but ta kasa, gumi ne ya fara k'aryo mata dan sanin kanta ne koh da kwana zata yi a ciki babu mai taimakon ta muddin ba ya Abdallah ba.
Ganin halin da Aysha take ciki ne ya sa Humayrah ta kwashe a guje ta nufi dandalin da ya Abdullahi yake hira da abokanan sa cikin sa'a kuwa tun daga nesa ta hange shi a tsakiyan abokanan shi suna ta barkwanci tana iso gurin fara'ar da ke d'auke a fuskan shi ta ragu cuz ya san cewa zuwan ta wurin ba alkhairi bane.
Kamar yanda ya zata hakan ta faru cuz da isowan ta wurin tana haki ta kwashe komai tsafffff ta fad'a mishi,, ba tare da ta k'are maganar ba ya mik'e cikin k'unan rai da tausayin mak'auniyar Allah ya nufi gidan su Aysha a 360.
Ganin babu sarki sai Allah Aysha ta yi jigum a ramin sai uban zufa ne yake ta k'aryo mata zuciyan ta cunkushe da bakin ciki. Jin sallamar ya Abdullahi ne yasa ta sakin sassanyar ajiyar zuciya,, da sauri yayi gurin ramin har yana had'awa da gutun gudu zuciyan shi cunkushe da wasi wasin wanda ya hak'a ta cuz a iya sanin shi ya san cewa babu rami a gidan how comes yau Aysha ta fad'a a ciki??,, dole akwai wanda ke shirin cutar da ita,,
yana d'ora ido akan ta wata irin fad'uwar gaba ce ta kama shi cikin sauri ya tsuguna a gefen ramin kad'an ya riko hannayen ta biyu ya fara kiciniyar janyo ta waje,, k'iris ya rage ta idda fitowa k'afan ta ta taka wata dutse cikin rashin sa'a tsantsi ya ja ta ta koma ciki sai ga ya Abdullahi ya biyo ta tsundummm a ciki,,
jini ne ya fara bin kafan shi,, ba tare da ya damu da jinin da yake zubo mishi ba burin shi kawai ya taimaka ma makauniyar Allah ya ciro ta a ramin,, da kyar ya mik'e tsaye yana matsa idanuwa ya shiga kiciniyar d'ago ta,, da taimakon Allah ya samu ya taimaka mata ta fito daga ramin shima ya fito zuciyan shi cike da tunani faaallll dan a iya sanin shi babu rami a wurin ta yaya aka yi har aka tona ramin??,
lokaci guda tunanin koh inna ce dai ta hak'a ramin ya fad'o mishi a rai yayin da d'aya b'angare na zuciyan shi ke gargad'in shi da cewa" ta yaya mace kamar inna Larai wacce tsufa ya fara kama ta zata iya hak'a rami mai zurfi kaman wannan", bai idda tunanin nan ba ya tsince kan shi da k'arasowa gaban ta, sai da ya daidaita natsuwan shi kafin ya rik'o hannun ta yana d'ingisa k'afa yayi mata jagora zuwa d'akin ta ya kuma taimaka mata ta zauna a kan gado,,
cike da tsantsar tausayin ta ya tsugunna a gaban ta ba tare da ya sake hannun nata ba murya na rawa yace" k'anwa ta, yaya aka yi hakan ta faru da ke eeeyyee, ki fad'a min garin yaya kika fad'o cikin rami kuma wa ya hak'a ta, yanzu ba don Allah ya taimaka na taho ba da me kike tunanin zai faru??, jero mata tambayoyin yayi ba tare da ya bata dama ta amsa d'aya daga ciki ba, sai da ya gama yi mata tambayoyin before ya tsaya ya zubo mata eyes yana jiran ya ji ta bakin ta.
Bata iya amsa mishi ba ta saki kuka mai cin rai with so much pain in her heart,, maganar zuci ne ta fara yi dan tunawa da tayi da *macucin* da ya zalunce ta tana cewa" kaico na !!! kaico na ni Aysha !!! dubi yanda muryar ya Abdullahi ya nuna alamar rud'ewa a d'an abun nan da ya faru da ni d'in nan ta yaya zan iya bud'e baki na fad'a mishi babban mik'in da ke fame a cikin zuciya ta,, nace mishi an k'eta min haddi ??, *Waye Macucin* da ya raba ni da martaba ta ta d'iya mace ya cutar da ni?? ta yaya zan iya gane shi balle na d'auke mata ki a kan shi?? Ohhh Allah ka sada ni da wanda ya cutar da ni dan bazan tab'a barin shi ba sai ya d'and'ana fiye da bak'in cikin da ya jefa zuciya ta a ciki........
Ba tare da ta gama maganar zucin da take yi ba sai jin muryar shi tayi yana cewa" k'anwata ki fad'a min wanda yayi miki wannan cuta ya hak'a ramin dan na san cewa da wata manufa aka yi hakan".
Da kyar ta bud'e baki cikin muryar kuka tace" Allah ne masani yayana sanin kanka ne cewa y'ar k'anwar ka bata iya tantance kamanin ta balle har ta iya gano shi amma babu komai Allah na nan kuma yana sane da ni, , duk abubuwan da take fad'a kan ta na kan cinyar ta bata d'ago ba,,
Tana kawo aya ya saki huci mai zafi ya mik'e tsaye zuciyar shi na tafarfasa ya kai naushi ma iska nan ya shiga kewaye d'akin, sai da ya kai tsawon minti biyar yana zagaye d'akin kafin ya sake tsugunawa a gaban ta ya d'ago kanta ya zubo mata idanuwa yana zallan aikin kallon ta, jikin ta ne ya bata hakan da sauri ta k'awar da kan ta gefe guda ta inda take tunanin ba direction d'in da yake.Vote
Share
Comment if you like d novel08036424738
*Sa'eeda✍*
~Y'ar mutanen Dengi~
YOU ARE READING
WAYE MACUCI
Historical FictionLabari ne a kan wata mak'auniyar Allah mai suna Aysha wacce take soyayya da yayan ta amma kwatsam sai wata tsautsayi ya afka mata har hakan ya saka ta cikin bakin ciki,ba tare da ta bayyana mishi ba sai daga baya ya fahimci halin da take ciki a tsan...