Part 3 and 4

1.5K 95 2
                                    

🏵🏵☀☀🏵🏵☀☀🏵🏵
          *☀WAYE MACUCI☀*         
🏵🏵☀☀🏵🏵☀☀🏵🏵
        '''Suhaif koh Suhail'''

***********************************

® *REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS P.M.L*💭💭💭

_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_

# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
      
          
                       ©
'''Marubuciyar Rayuwar Sumayyah'''

    *SA'EEDA MUSA DAUDA😍*

'''Follow and ✅ote me on Wattpad''': *SaeedaMusaDauda*

*BESTORED TO MY LIL SIS* ''' SUMAYYAH MUSA DAUDA'''
                 

                    3⃣—4⃣

         Tafe suke a hanya su biyu, babu abunda kake ji a sai kukan tsuntsaye da na karnuka ke tashi a wurin,, har sun yi nisa da tafiyar Sadeeq ya ja ya tsaya yace" affff ka ga na sha'afa wallahi tsabar rud'anin halin da na tarar da ka kai a ciki har na manta da kwatancen gidan da hajiya ta min.
      Suhail ya dube shi with so much surprised look in his face before yace" and what brought us here da kake cewa ka manta bayan ka san cewa gidan zamu atleast da ka fad'a min da ban sha wahalar fitowa ba, any ways ni dai ka ga tafiya ta dan bazan ci gaba da zaga gari cikin daren nan ba tare da sanin inda na dosa ba", ya fad'a tare da k'ok'arin juyowa da baya ya koma.
      Da sauri Sadeeq ya rufa mishi baya suka nufi coppers lodge suna tab'a hira har suka iso,  suna isowa direct d'akin su suka nufa da shigowan su ciki suka fad'a kan bed koh wannen su na mai da numfashi kamar wanda suka yi wasan tsere, daren ranar da tunani kala kala suka kwana a zukatan su barin ma Suhail da idan ya kulle idanuwan shi muryar yarinyar da kuma suffan jikin ta ne kad'ai ke mishi yawa a kwakwalwar.
       Washe gari da asuba Aysha ta taso daga barci idanuwan ta duk sun kunbura cuz of kukan da taci daren jiya, da kyar take d'aga k'afan ta hannun ta rik'e da sanda ta d'ebo ruwa a randar inna Larai, sanin kanta ne cewa muddin ta bari inna ta fito toh fa  ba zata bari tayi amfani da shi ba.
       Ta d'ebo ruwan kenan tana k'ok'arin d'aukawa inna Laure ta fito daga d'aki karaffff idanuwan ta suka sauka a kan Aysha da ta daddage tana kiciniyar d'aukan bokitin ruwan.
     Da k'arfi ta saki salati tace" eeehhheeee kai ka kaiiiiiii me nake gani haka ni Larai".
      A d'an tsorace Aysha ta janye hanun ta daga jikin bucket d'in ta juyo da face d'in ta dai dai saitin inda kunnuwan ta ke jiye mata muryar inna Larai, marairaice fuska tayi tace" ayya inna dan Allah ki taimaken wanka nake son yi", a harzuke tace" an k'i a yin dan uwar ki a yawon maular da kike yi baki samo kud'in da zaki saya ruwa wanka bane tunda idanuwan ki basa moruwa, toh wallahi ba zan lamunci hakan ba kuma kar ki sake ki sake ki kuma tab'a min randa ta balle ki shafa min lalurar nakasa,,
     Da sauri Aysha tace"'''Subahanalillah'''" haba inna kin manta cewa Allah ne ya d'ora min nakasar ba dan ya k'i ni ba??, me yasa lafiyayu suke kyamatan masu lalura irin tawa, shin kun manta cewa ba wai kun fi k'arfin hakan bane Allah ya bar ku da idanuwan Ku ku amfana da su a'a sai dai dan hakan ya so ya gan ku, kuma yana da ikon warkar da nakasassu ya kuma d'ora ma lafiyayyu lalura.
       Inna Larai ta dak'a mata tsawa tace" bana son munafurci banza kin fini ibada ne da zaki saka ni a gaba kina min nasiha, toh na fad'a nakasa abun kyama ce ki yi abunda zaki yi".
    Wasu tsiraren hawaye ne masu d'umi suka gangaro a face d'in Aysha ran ta na mata k'una ta fara dogara sandar ta tana d'aga k'afa da kyar yayin da inna Larai ke ta aikin bank'a mata harara.
      Ta zo zata wuce da sauri inna Larai ta ficik'o ta da k'arfi ta doka uban ashar sannan tace" oohhh ni Larai na gamu da gamo na me nake gani a jikin ki haka eeyyeee Aysha mak'auniya".
       Tuni hantar cikin ta ta kad'a heart d'in ta na beating da sauri fatt fattt fatttttt kamar zai fita da kyar ta iya dai daita natsuwar ta cikin inda inda tace" uuuhhmm uhhmm damaaaa, "dama me??", inna Larai ta fad'a a d'akale. Sai da ta had'iye miyau masu d'aci kuuuuttt before ta d'ora da cewa" dama bayan fita ta ne daga gida jiya a hanya wata mota ta  kad'e ni Allah ya taimaka da sauran kwana na da kun samo labarin mutuwa ta".
       Mtsssssss inna Larai taja tsaki tace" Allah ya k'ara kad'an kika gani tunda dai jarabar son kud'i ne da ke koh da yake ba sabon abu bane a wurin nakasassu dan sun fi mai lafiya jarabar son kud'i", tana gama fad'a ta d'auko k'aton bucket ta mik'a ma Aysha tace" ungo karb'i wannan ki je ki d'ebo min ruwa na dan bana yafewa eeehhheeennn, babu ruwana da rashin idanuwan ki idan ma mutuwa zaki yi sai dai ki mutu, ta k'are maganar tare da dad'a turo ma Aysha bucket d'in a hannun ta, dan mugunta inna Larai ta fisge sandar Aysha a hanun ta a cewan ta wai kar garin dogara sanda ta yi mata b'arin ruwa koh ta shafa mata datti.
       Ba dan ta so ba ta k'arb'a bucket d'in tare da sauya kayan da ke jikin ta zuciyan ta cike da tarin bak'in cikin halin inna Larai, gefe guda kuma tunanin abunda mutumin nan ya aikata mata ya fad'o mata a rai, wani irin kullutun bak'in ciki ne ya dirar mata a zuciyan ta, da kyar ta fara tafiya tana lalil'o hanya da d'aya hanun ta tare da daidaita tafiyan ta cuz of gudun kar wani ya gan ta ya zarge ta,  Allah ya taimake ta ma tana fita taji muryar yarinyar mak'ociyar su, daga inda take ta kwad'a mata k'ira yarinyar ta taho a guje tace" laaaa adda Aysha ina zaki da bokiti a hannu??.
   Cikin dak'ewar zuciya Aysha tace" Humaimai d'ebo ruwa za ni a rafi koh zaki min jagora ne kin ga inna ta kwacen sanda ta gashi kuma ba ido gare ni ba".
     Da yake Humayrah yarinya ce k'arama but akwai ta da kaifin basira da sanin ya kamata da muryar tausayin Aysha tace" toh adda" rik'o hanuna mu tafi kin san yaran anguwar nan da mugunta sai su buge ki ki fad'i k'asa, "toh" Aysha ta fad'a tare da lalib'o hannun humayrah ta had'a da tata ta r'iko gammm suka nufi hanyar rafi da tunani falllll a ran Aysha.
      B'angaren su Sadeeq kuwa basu farka ba sai around 7:00, a gaggauce suka shirya suka fice suka d'au hanyar tranning cuz a yau ne ranar su ta k'arshe da zasu yi treaning, tun a hanya Suhail yake jin jikin shi so weak but ya dangan ta hakan da rashin samun isasasshen barci da bai yi ba, daga nesa ya hago wata yarinya tana tafe kan ta d'auke da bocket yarin da d'aya hannun ta ke rik'e da wata karamar yarinya suna tafe, suna isowa daidai kusa da da su yarinyar ta k'auce ta ba su hanya, ita kuwa Aysha bata san da mutane a gaban su ba sai tafiyar ta take yi hankali a kwance ba tare da san da mutane a gaban ta ba,,
      Ba k'aramin mamaki Suhail yayi ba da ya ga yarinyar tana dad'a nufo su koh alamar d'arrrrr babu a tattare da ita and kuma duk wanda ya gan ta a hakan ba zai tab'a cewa makauniya bace ba cuz babu wani alama da ya nuna hakan daga gare ta dan idanuwan ta ba a rufe suke ba,, ba tare da ya kauce mata a hanya ba ya cigaba da tafiyan dan ya auna iya hankalin da kuma nutsuwar ta,, har tazo dai dai gaban shi jikin shi na k'ok'arin had'uwa da tata ya ja gefe da sauri da k'afi yace" '''Subahanalillah''',   yana pointing d'in ta da hand cikin tsananin b'acin rai ya d'ora da cewa"baki da hankali ne koh cikakkiyar tarbiya ce ta miki karanci da har kika d'auki jikin ki da arha haka??·
      Da kallon mamaki Sadeeq yake bin shi da shi dan duk dramar da ake yi bai sani ba cuz hankalin shi ya raja'a wurin bama friend d'in na shi labari sai da ya ga friend d'in shi ya ja dogon tsaki ba tare da ya d'auke hanneyen shi daga nuno tan da yayi ba d'in before Sadeeq ya mai da idanuwan shi gare ta yana mai mamakin abunda ya had'a ta da friend d'in shi har ya hasala haka .
     Ita kuwa uwar d'aki na bata san ma yana yi ba ta jiyo muryar shi but a zaton ta koh da yara yake yi cuz tana jin hayaniyar su a wurin,, yana ganin haka ya zubo mata idanuwan shi k'irrrr babu d'aukewa cuz tunda yake bai tab'a ganin irin haka ba,, ji yayi karamar yarinyar tace" adda Aysha kad'an ya rage ki buge wani mutum fa da ba dan ya kauce ba da tuni kin bige shi,, ki rik'e kafad'a ta ki dinga bina a baya nayi miki jagora gudun kar mu had'u da wani marar mutunci a hanya".
       Mamaki ne ya kama shi cikin tsantsar mamaki ya zaro eyes ba tare da ya d'ago idanuwan shi daga gare ta ba,,  in a surprised mood yace"what",, ya tsaya shiru yana mamakin wannan al'amari,, gabaki d'aya maganar yarinyar ya bala'in kulle mishi kai,,
     Bai k'ara cika da mamaki ba sai da ya ga yarinyar(wacce aka k'ira da adda Aysha tana lalib'o kafadar karamar yarinyar da hannu daya tace" toh Humaimai kin ga da ya Abdullahi na nan da koh inna Larai ta kwacen sanda ta da shi zai d'ebo ruwan ya kawo ba tare da sanin inna ba.
      Jin an ambaci sunan "ya Abdullahi" tuni abubuwan da suka faru a daren jiya suka yi ta mishi yawo a zuciyan shi,, bugu da k'ari kuma muryar ta yayi mishi kama da ta yarinyar da take ta pleading d'in shi a kan kar ya k'eta mata haddi.
     A take zufa ya fara k'aryo mishi ta koh wani b'angare na jikin shi da tsantsar rud'ewa ya bi bayan su cuz he need to know koh ita d'in wacece dan ya nemi yafiyar ta yayin da abokin na shi ya yi mutuwar tsaye zuciyan shi cike da tarin al'ajabin abunda da friend d'in na shi ke shrin yi.



     Sorry for the errors ban da isasshen lokaci ne shi yasa ban samu damar yin editing ba ina yin ku irin sosai din nan most especially my die heart.

Vote
Share
Comment if you like d novel

08036424738

~Yar mutanen Dengi~
     *Sa'eeda✍*

WAYE MACUCIWhere stories live. Discover now