🏵🏵☀☀🏵🏵☀☀🏵🏵
*☀WAYE MACUCI☀*
🏵🏵☀☀🏵🏵☀☀🏵🏵
'''Suhaib koh Suhail'''***********************************
® *REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS P.M.L*💭💭💭
_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_
# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
©
'''Marubuciyar Rayuwar Sumayyah'''*eedatou😍*
'''Follow and ✅ote me on Wattpad''': *eedatou*
*BESTORED TO MY LIL SIS* ''' SUMAYYAH MUSA DAUDA'''4⃣9⃣
Tee na ganin ya b'ace musu da gani ta ja dogon ajiyar zuciya har sai da hibb ta juyo ta kalle ta tace" what beb", ba komai hibb, wallahi tun da na fara d'ora idona a kan ya Abdallah zuciyata ta kamu da tsananin k'aunar shi, ban san hanyar da zan bi na nuna mai irin k'aunar da nake mishi ba, kin san mace an santa da alkunya shiyasa kika ga bana iya tunkarar shi da maganar".
"I understand how you felt but wai not ki cire duk wata kunya ki aje gefe kar fa garin kallon kwallo yayi miki ruwa", "no i can't", bazan iya yin hakan ba hibb na jira har sai ranar da ya Abdallah yace yana sona", tee ta fad'a cike da raunin zuciya.
Ringing d'in bell suka ji na change of period da sauri suka nufi class d'in su suna isowa suka tarar da maths teacher ya gama class nashi ya fice, nufar seat d'in da Ash take zaune suka yi tee ta zauna a zaman desk d'in yayin da hibb ta zauna a gefen Ash.
Ash tana ganin su tace" kun kyauta da yau baku attending class ba gashi maths teacher ya bada Assignment kuma bazan koya muku ba", ta fad'a tana aika musu hararar wasa.
Hibb tace"Allah Asha ba haka bane yayan tee ne fa ya zo shine muka tsaya gaisawa, kai gaskiya tee yayan nan naki is very friendly,,
Shine baza ku gayyace ni mu gaida shi ba, ta cuno baki tace Owk owk i know understand so kuke ku nuna min banbanci".
Marairaice fuska tee tayi tace" Duk me ya kawo wannan maganar Ash bayan babu irin neman da bamu yi miki a makarantar nan ba, wallahi har sai da ran ya Abdallah ya b'ace a garin neman ki da muke tayi dan sai cewa yake wai mun b'ata mishi lokaci".
Owk toh shikenan next time idan yazo baku min magana ba sai mun b'ata da ku".
Mai da wuk'ar other half Ashteehibb basa fad'a balle gaba, a kullum suna ma junan su yafiya da uzuri sannan suna yak'i da duk wani abu da suka san zai ia haddasa musu fitina a tsakanin su", tafawa suka yi su duka tare da lakatar hancin junan su suka fice chamban su cuz teacher d'in da suke da period d'in shi ya shaida wa class rep d'in su cewa ta sanar da y'an ajin ba zai samu daman zuwa ba a sakamakon wata tafiya da zai yi".
Haka suka fice daga ajin suna tafiya kowa na bin su da kallon burgewa cuz they are classy shi yasa da yawa matan makarantar ke jealous a kan su".
Suna isowa suka nemo seats suka zaunan nan tee ta shiga basu labarin yayan nata, da abun ya ishe Ash ta ja tsaki tace" wai nikam tee bakya gajiya da tad'in yayan ki ne duk kin bi kin cika ma mutane kunne da maganar shi, hala ma irin yayyi masu taurin nan ne komai nasu a murd'e".
Harar wasa tee ta sakar mata tace" tabbbb ba dai yaya na ba kam duk hassada k'aryar mutum ya zauna da shi ya kushe shi",
Sosai ma kuwa tee, wallahi d'an hirar nan da muka yi da shi wallahi na fahimci mutum ne mai dad'in sha'ani uwa uba sauk'in kai, he is very simple ba kamar bros d'ina da koh magana ka mai zai yi kamar ba da shi kake ba idan ka samu kyakkyawar amsa toh sak'on harara ya aiko maka".
eeehhheeennn you see ba ? kin ji hibb ta fad'a miki thank God ma ba daga baki na kika ji ba balle kice ina yabon yaya ne yasa na fad'a hakan".
Ash ta tab'e baki tace" kan ku ake ji, ni dai kun ga tafiyata i have alot to do, idan zaku biyo ni na koya muku yanda ake solving d'in maths d'in nan idan baza ku biyo ni ba kuma fine, tana k'orarin barin wurin suka bi bayan ta da sauri.
A tare suka solving maths d'in suna gamawa Ash ta fiddo wayan ta ta kashe ido d'aya tana musu nuni da shi tace" surprise,",
Hibb ce ta fara k'arba tana jujjuya wayan a hannun ta tace" wow beb kin fatso gari wayan tsadadden waya haka?
Other half wa ya sayo miki wannan uban waya haka ba dai wai kika samu kika wanko shi ba ya sayo miki waya, tee ta fad'a tare da Jefo mata tambaya".
Harara Asha ta b'alle mata tace" God forbid !!!, kamar ni na tsaya wani d'a namiji ya saya min waya da ajina da komai d'ina bayan ina da iyaye na?,
"Mtwwww Ke kin cika d'aukan zafi da yawa, wasa fa nake miki Ash ai duk abunda aka gani mai tsada a wurin ki an san cewa aikin dad ne so me abun d'aga hankali a nan".
Suna cikin zancen ne time keeper ta ringing belt d'in change of period da sauri suka ruga class domin submitting assignment d'in English teacher.B'angaren ya Abdallah kuwa yana isowa gida d'akin shi direct ya nufa ya bud'e fridge ya d'auko goran ruwan faro ya b'alle murfin ya kafa a baki, sai da ya shanye ruwan tasss kafin ya d'ago yayi wurgi da goran ruwan tare da dafe kan shi yana tunanin yarinyar da ta bangaje shi a makarantar su tee, runtse ido yayi da k'arfi lokaci guda zuciyar shi ta fara tunano suffan yarinyar, yayi juyin duniya ya tunano inda ya tab'a ganin ta amma ina ya k'asa, haka ya zauna babu walwala a fuskan shi ya d'afe kanshi a sakamakon tsara mishi da kan yake, yana cikin tunanin ne mum d'in tee ta shigo d'akin ta tarar da shi a hakan, magana tayi mishi taji shiru hai amsa mata ba ta tapping d'in shi da hannu tace" son lafiya da koh"?
"Ummm uuummmm mum ba komai zuciya ta ce take zafi".
" Ehhyyaa bari na k'ira doctor ya duba ka tana gama fad'a ta bar d'akin ta koma nata ta d'auko wayan ta tana dubawa numban doctor, tana gani ta dailing numban ta shaida mishi halin da ake ciki tana gamawa ta koma d'akin ya Abdallah ta zauna a gefen shi tana ta jero mishi sorry bila adadi.
Jim kad'an sai ga doctor ya shigo ya mishi gwaje gwaje tare da rubuto mishi maganin da zai yi amfani da shi ya ba shi suka fice da mum.
Bayan fitan su ne mum tace" ni kam doctor me yake damun yaron nan ne baka fad'a min ba, ka bar ni cikin tunanin halin da yake ciki". Gyara tsuyuwa doctor yayi yace" gaskiya madam is something serious and had becoming worst, your son is suffering from heart attack".
What !!! ta fad'a da k'arfi, garin yaya hakan ta faru da shi, nawa nawa Abdallah yake da zai kamu da ciwon zuciya"?Ahhhhaaaaa muje zuwa
*eedatou✍🏻*
~Y'ar mutanen Dengi~
YOU ARE READING
WAYE MACUCI
Historical FictionLabari ne a kan wata mak'auniyar Allah mai suna Aysha wacce take soyayya da yayan ta amma kwatsam sai wata tsautsayi ya afka mata har hakan ya saka ta cikin bakin ciki,ba tare da ta bayyana mishi ba sai daga baya ya fahimci halin da take ciki a tsan...