Page 63

828 52 4
                                    

🏵🏵☀☀🏵🏵☀☀🏵🏵
          *☀WAYE MACUCI☀*         
🏵🏵☀☀🏵🏵☀☀🏵🏵
        '''Suhaib koh Suhail'''

***********************************
          
                       ©
'''Marubuciyar Rayuwar Sumayyah'''

    *SA'EEDA MUSA DAUDA😍*

'''Follow and ✅ote me on Wattpad''': *SaeedaMusaDauda*

*BESTORED TO MY LIL SIS* ''' SUMAYYAH MUSA DAUDA'''

                        6⃣3⃣

       A parlor suka tarar da Suhaib yana cin abinci, kallo d'aya ya musu ya d'auke idon shi yayin da gaban shi ke tsanan ta bugu na ganin yanda rigar Aysha ya squeezed.
      Ko ba a fad'a mishi ba ya san cewa dole hasashen shi ya zama gaskiya.
    Ba tare da ya ankara ba sai ji yayi Suhail ya dafa kafad'an shi yace" bro yaya dai na ga kana juya cokali a hannu, ko dai wani abun ne ke damun ka? 
      Tari ne ya d'an kwace mishi, da sauri Suhail ya d'ebo ruwa a cup ya mik'a mishi shi koh ya amsa ya fara kurb'awa, sai da ya shanye ruwan tassss kana ya dire k'ofin tare da kallon Suhail, ya k'ak'alo murmushin dole yace" aahhh haba, noooo!!! kawai dai na fara jin k'oshi ne and kuma zuciya na na tashi".
      Cike da tsantsar kulawa Suhail ya sauya fuska irin ta tausayi yace" owk to, but ka daina over feeding, may be ko ka cika cikin ka da yawa ne ya jawo haka.
      "Owk i will", Suhaib ya fad'a yayin da yake share bakin shi da tissue.
      "Wai ina mum ne bro ban gan ta a dinning ba ko bata fito bane"? 
    "I don't know, ni ma fitowa na kenen ban tarar da kowa a dinning ba, but na ga an jero abinci a dinning shi ne nake ci".
     "Owk toh bari na kai baby school lokaci na dad'e tafiya idan mum ta fito ka shaida mata cewa na tafi kawai".
    "To abincin fa? Baza ka ci bane?"
    No sai na dawo kawai, yana gama fad'a ya ja hannun Aysha da niyar barin wurin, Suhaib ya bi bayan su da kallo yana ganin yanda Aysha take ta nonnokewa a bayan Suhaib tana k'ok'arin b'oye rigar ta ta gaba cuz zai iya kallon abinda bata so ya gani ta site view d'in shi.
       Murmushi yayi ya girgiza kan shi na ganin yanda ta daddage tana b'oyewa, abunda bata sani ba tun fitowan su yake lura da haka.
     Ganin sun kai bakin k'ofa, suna shirin fita yace" little ba sallama ne ? and you can't even wave me"?
      "Cikin alamar rashin gaskiya ta hau kame-kame tana tsotsa k'eyan ta da d'aya hannun ta tace" ummm ummm, na manta ne big bro but i'm sorry".
    "Ashe zaki manta da big bro d'in ki kena"? ya tsare ta 
    "Nooo, ina na isa? ai you are dear to me". Cike da tsokana Suhail ya hau dariyan su yana cewa" yau dai an gan ku a rana, tun ba'a je ko ina ba har an fara jin kan ku".
     "Ba mai jin kan mu ni da little dan haka gara ma ka daina dariyar, koh ba haka bane little"? ya kafa mata da ido.
   " Yeah big bro", ta amsa mai tare da sakar ma Suhail hararar wasa tace" ba za dai ka ji kan mu ba eeeheee".
   Haka dai suka yi sallama da Suhaib suna wasa da dariya cikin shauk'i har suka fita daga parlorn suka wuce parking space, nan ne suka shiga cikin wani tsadadden mota ash colour suka d'auki hanyar makarantar su Ash. 
     Tun a mota tee ta k'ira Ash a waya cuz tun d'azu suke zaman jiran ta ba su gan ta ba, wayar na shiga Ash ta d'aga tace" hello!!!  tee ga mu nan a hanya ni da durling me, physics teacher d'in ya shigo ne"?
       "No bai shigo ba but kin san ya kusa shigowa, wai ma me kika tsaya yi ne bayan kin san muna da class da safe, ko kin manta cewa yau ba weekend bane?".
     "Gajiya tayi da mitan tee, ta juyo kalle Suhail da ke tuk'i amma rabin hankalin shi na kan ta tace" kaiiii tee dad'i na da ke mitan ki yayi yawa, ga mu nan fa mun kusa isowa".
     "Ohhh haka ma zaki ce ko? dama sai da na fad'a ma hibb cewa ba zan k'ira ki ba domin kuwa na san halin ki, amma ta matsa sai na k'ira", toh idan kika ga dama ki kai 8:00 tunda yanzu quarter to 8 (7:45) ne".
      Ganin yanda ta d'auki zafi Ash ta rage murya tace" haba other half ba za ayi haka ba, ko kin manta tsakanin Ashteehibb, ba ma fad'a ne"? 
     Ke d'in ce sai da haka, idan ba ai miki wuta-wuta ba sai ki ta b'ata ma mutum rai".
     Sallama suka yi ma junan su daga nan Ash ta kwantar da kan ta a saman seat tana satar kallon Suhaib, yana juyowa suka had'a ido da shi tayi saurin d'auke idanuwan ta daga nashi tana kallon tagar motan.
     "Da dai kin jiyo kin kalle ni y'an mata na, ki kalle ni ki k'ara kallo na, i'm all your".
   "Ni fa ba kallon ka nake yi ba", ta fad'a a kunyace.
    Hannun shi d'aya yasa yana murza tafin hannun ta, ya kashe mata ido d'aya yace" to me kike yi? eeyee fad'a min na ji, idan ma wannan abun nan ne mai dad'in nan ne bai ishe ki ba ki fad'a na k'ara miki, idan kika tsaya jan aji ki cutar da kan ki ni babu ruwana tammm".
   Cike da tarin shagwab'a ta turo bakin ta waje tace" ni fa na fad'a maka babu komai".
     Bin bakin nata yayi da wani irin mayataccen kallo yana ganin yanda libs d'in ta ke kad'awa slowly kamar da gayya take yi, bai san sanda ya paking motar a gefen titi ba, ya gamo libs d'in ta yana tsotsa kamar wanda yake tsotsan alawa. Sai da ya shafe kusan minti 3 yana tsotsa kana zare bakin shi a nata, ya jingina kan shi da steering  motan na tsawo minti d'aya daga baya ya ta da motan sai makarantar su Ash.
     Ba su suka iso ba sai 8: 55, cikin sa'a suka tarar da su tee a wajen da suka saba zama idan ba teacher a ajin su. 
       Tun kafin su gama parking Ash ta lek'a ta tagar motan tace" hello guys", su duka biyun suka yi wurin motan cikin sauri suna masu nuna tsantsar farin cikin ganin ta.
      Ash na ganin suna zuwa wurin su, ta bud'e murfin motan, tare da d'ora hannun ta a kai, k'afan ta a ciki, d'aya a waje tana mayar musu da martanin murmushi saboda ita ma kan ta tana farin cikin ganin su".
      Har suka iso ba tare sun lura da squeezed d'in rigar ta ba, sai da ta fito ne tana yunkurin mai da murfin motan ta rufe kana suka hau bin ta da kallo. A tare suka saka shewa suka tafa su biyun, abinda kenan ya ja hankalin Ash ta hau bin jikin ta da kallo domin har ga Allah ta manta da nad'ewan da uniform d'in ta yayi.
       Tana d'ora idanuwan ta a kan rigar ta ji wani irin azabar kunya ya addabe ta, bata san sanda b'orin kunya ya kama ta ba ta hau kame kame tana cewa" ku,  ku au dariya ta ma kuke yi ko?  ai ban goge rigar da kyau bane".
      Dariya suka sake sakewa wannan karon har sai da suka kular da ita, ta hau b'ata rai tana burning face, su ko sai dariyan su suke yi ko a jikin su.
       "Hibb ta yi mata rad'a a kunne tace" kina shagalin ki other half, tun yanzu har an fara kashe juna da love a dai yi a hankali kar a runtumo mana k'aton tumbi kafin a yi tarewan, a bar mu da shan tarin kunya", da yake hibb ta san da maganar auren Ash da Suhail.
        Tee ta kanne mata ido murya k'asa k'asa tace" au ai dole ne ayi lattin makaranta yau, an tsaya ana ba ma soyayya hakkin ta".
     Dad'e kunnuwa Ash ta yi, ta cika tayi faammm da ita cuz sosai suka kawo ta har iya wuya.
     Suhaib na daga mota yana kallon dramar da ake, sai da ya ga yanda suka saka ta a gaba da tsokana kana ya bud'e murfin motan ya fito, ya zagayo wajen su tare da had'a hannun shi da na Ash ya dube su yace" me kuke fad'a ma baby ne haka? Na ga sai faman shan k'amshi take yi".
       "Ba komai fa bro kawai dan muna tambayan ta dalilin da yasa ta yi latti shine take wani fuskewa".
      " Allah babu wanin nan wallahi, tsokana ta suke yi wai fa..........", ta ja baki ta yi shiru.
     "Wai me? fad'a min na hukun ta su kin ji baby na"?, ya fad'a yana mai mutuke fuska kamar da gaske, wai shi ala dole an tab'a mishi babyn shi. 
      "Uhmmm uhmm ni dai ban iyawa kawai ka hukunta su".
    " Kin tab'a jin an yi hukunci ba tare da anyi laifi ba"?, ya jefa mata tambaya tare da tsare ta da ido.
     Suna cikin hakan ne suka hange physics teacher d'in su daga nesa, a gaggauce suka yi sallama da Suhail suka shiga class domin d'aukan darasi, shi ma ya shiga mota cike da mararin masoyiyan shi. 
    
      Bayan sun shiga aji sun zauna, physics teacher ya shigo yana tambayan assignment d'in da ya ba su, ko waccen su ta fito da na ta, ta submitting ma monitor d'in su daga nan ajin yayi tsitttttt teachern ya fara introducing musu sabon topic d'in da za su shiga.
      "MOTION" na ga ya rubuta a jikin allo yayi musu takaitaccen bayani wanda sai da ya tabbatar da ya gamsar da fiye da rabin aji, daga baya ya rubuta questions a jikin allon ya solving musu.
      Period d'in shi na cika ya tattara dukkanin assignment d'in ya fita daga ajin domin yin marking.
     Haka suka wuni jugummm a ajin suna d'aukan darasi daga maluma da dama, wannan ya shiga, wancan ya fita, breakfast ne kad'ai ya fitar da su, sai da closing awa ya cika kafin suka samu suka gama classes d'in yau.
    
     Bayan kwana biyu Ash na kwance a kan three seaters tayi pillow da cinyar Jummai da ke tsefe mata gashi, mum na gefen su tana kallon labarai a talabijin.
    Wayan Ash ne yayi ruri, da sauri Jummai ta mik'a mata ta amsa wayan tare da mannawa a kunnen ta tace" hello!
      "Shiru yayi mata kamar ba zai amsa mata ba, jim kad'an yace" baby sallama ya kamata ki min ba hello ba, kin ko san muhmancin sallama kuwa?
      "Mantawa nayi fa", ta fad'a tana mai marairaice fuska.
   Kece kullum a cikin mantuwa ko,? to duk ranar da na sake k'ira ba ki min sallama ba ke ma kin san sauran ba sai na fad'a miki", ya ja kwafa.
      "Me kike yi yanzu"?
Babu komai Jummai ce ke taimaka min tana tsefe min kai ina so zan saloon".
     "Da izinin wa zaki tafi?
    Shiru ta mishi tare da had'e ran ta kamar yana ganin ta, ganin haka Suhaib yace" to ban yarda kije wani saloon ba, idan kin shirya magana ki zo ki same ni idan ba haka ba kuma a fasa maganan tafiyan, kitttttttt ya kashe wayan.
     Tana ganin ya kashe ta maida wayan ta ajiye, ta hau gunaguni, mum ta juya ta kalle ta, ta ga yanda ta had'e rai ga hawaye fallll a fuskan ta, cike da kulawa tace" what's wrong daughter? me ke damun ki, wa ya tab'a min ke?, ta jera mata tambayoyi tare da kafa ta da ido".
     " Mum cewa fa yayi wai ba zan je saloon d'in ba saboda ban nemi izini ba, Allah baki ga yanda kan ya dame ni da kaikayi ba, bana jin zan iya barci idan ban wanke kan ba", ta fad'a tana fitar da kwalla.
      Me yasa tun farko baki nemi izini ba kika tsefe?
     Na fa tambaye ki fa kafin na tsefe wani izini zan kuma nima?
     Murmushin wautar daughter d'in ta tayi, Aysha na ganin haka ta ta fashe da kuka tana wutsil wutsil da k'afa, sai abun ya ba ma Jummai dariya itama.
      Jin yanda ta daddage tana kuka, mum ta tsagaita dariyar ta ta hau lallashin ta tace" come one daughter stop crying, ban da abun ki ai yanzu ba mu da iko a kan ki, mijin ki shi ya fi dacewa ki tambaye izinin shi ba ni, ko kuma daddyn ku ba, tun daga ranar da aka d'aura auren ku komai naki ya koma kan shi, dan haka ki daina kuka jin ji? tashi ki je ki lallab'a shi har sai ya hak'ura".
     Ba k'aramin kunya maganar mum ya ba ta ba, a kunyace ta hau share hawayen ta, ta mik'e kamar marar gaskiya ta nufi site d'in su Suhail.
      Shigowa ta yi ta tarar da shi a zaune a kan kujerar da ke parlour d'in su, ya hard'e k'afafuwan shi, d'aya kan d'aya yana chatting da wayan shi.
      Ta zauna a kusa da shi tare da zumb'uro baki wai ita tayi fushi tace" gani na zo fa kuma ka k'i ajiye wayan bayan ka san na shigo".
      Juyo da kai yayi ya kalle ta, ya ga yanda fuskan ta ya canja launi yace" haka mum ta koya miki idan mijin ki na fushi da ke ki yi"? 
     Dad'a had'e ran ta tayi ba tare da ta yi magana ba, ta hau kallon tagar palourn.
      Ga zaton ta sai ji tayi ya kwanto da kan shi saman kafad'an ta yana shafa suman kan ta a hankali ta yanda ya san zai iya kashe mata gab'ob'in jikin ta.
       Tsigan jikin ta ne ya hau tashi a sakamakon jin da take yi kaman tafiyan tsutsa ne a kan ta, ta lumshe ido a hankali ta bud'e su tana amsar sakon shi.
      Harshen shi ne ya zura a kunnen ta yana wasa da shi cikin salon shi mai tafiyar da zuciyan masoya, a hankali ya hau gangaro da hannayen shi saman cibiyan ta yana gogawa a hankali cikin kwarewa, a take ta hau mik'a kamar mai jin barci, ta hau  nishi, yana gangaro hannayen shi kasan ta, huta ta d'auke mata ta hau nishi da k'arfi da k'arfi tare da sakin y'ar k'ara.
        Sosai su biyun suka fita a hayyacin su, suka manta inda kan su yake, suka kasa tan-tancewa a wace duniyan suke, sai da Suhail ya tabbatar su biyun sun ji zam zammmm, sun gamsar da junan su kana ya zare hannun shi daga kasan ta, yace mata ta jira shi yana zuwa,ya shige band'aki domin tsakake jikin shi.
    Bai wani b'ata lokaci a bad'akin ba ya fito yana tsane ruwan jikin shi, kallon ta yayi a hankali tana kwance a inda ya bar ta, murmushi yayi sabida shi kan shi ya san sahibar shi ta sha dad'i hakan ne ma ya kashe mata jikin ta.
   Zama yayi a gefen ta tare da jan ta jiki shi cikin tsokana yace" ko na k'ara ne? na ga kamar har yanzu akwai sha'awa a jikin ki".
      Daga kwance ta galla mishi harara tace" ba abun da ya kawo ni ba kenan dama can wayo ka min shi yasa kace sai na nemi izini ga shi daga zuwa ka hau yi min".
     "Me na miki?
"Abun".
"Wani abu"? ya fad'a tare da d'ago kan ta ya d'ora saman cinyan shi.
     "Ni ma ban sani ba ai kai ka yi", ta fad'a a shagwab'e.
      Ina zuwa, da sauri ya d'aga kan ta ya mike tsaye yayi hanyar parlor nan ya tarar da Jummai da mum a zaune suna hira dan tuni aka gama labaran.
       Gashe da mum yayi kana yace" Jummai ina kifiyan da kike tsefe ma baby kai? mika min ki huta karasa mata".
    "To, to, ga shi nan dama so nake na gama mata tsifan na kama aikace aikace na".
     "Kafin ki fara ki had'a min fruit salat".
"To ta amsa tare da mikewa ta yi hanyar kitchen.
       Bayan Jummai ta bar wajen mum tace" son ko kunya ta ma baka ji a gaba na kake maganar za ka ma matar ka tsifa, ummmm, ta tab'e baki kana ta d'ora da cewa"bari daddyn ku ya zo ayi a gama maganar tarewan ku dan naga rawar k'afan ka yayi yawa".
        "Ohhhhhh shhhhiittttt!!  mum ba matata bace? kawai dan zan taimaka mata sai a sa min ido".
       "Ohoooo dai kai ka sani amma ba zan yarda ku kai min one weak a gida ba balle ku b'are mana aiki".
        A d'an kunyace ya shafa suman kan shi ya haura sama da gudu yana wai-wayan mum k'asa-k'asa yayi magana yace" idan baku bani matata ba cikin kwanakin nan sai dai ku shirya rainon baby".
       Bin shi da kallon mamaki mum ta yi dan tsafffff ta ji abunda ya fad'a, a zuciyan ta kuwa sai farin ciki take yi da irin yanda Suhail yake tsananin k'aunar Aysha, baya iya b'oye son da yake mata a gaban kowa. 
      Bayan Suhail ya shiga d'aki, ya hau tsefe ma Aysha kai yana yi yana jan ta da hirar soyayya, yana gamawa ya taje mata, ya parking mata, kana ya rike hannun ta suka fita waje.
     Ba su tarar da kowa a parlorn ba dan mum tuni ta gaji da zama ita kad'ai ta mike ta shiga d'aki ta kwanta kafin lokacin sallar la'asar yayi.
       D'akin Aysha suka nufa ya zaro akwatin kayan ta, ya bud'e ya hau nima mata hijabin da za ta saka.
       Yana d'aga wani hijabi mai ruwan madara ja ji fad'uwan wani abu, bin wajen da ya ji k'aran yayi ya hange wani zobe mai matukar kyau da kyalli dan har kashe ido yake.
      Gaban shi ne ya fad'i dan ko ba'a fad'a mishi ba ya san zoben ko na wanene, jiki a sanyaye ya juyo da kai yana kallon Aysha da tun fad'uwan zoben ta k'ura ma mishi ido tana kallo, idan bata manta ba tun lokacin da ta gane mai zoben ta cire ta ajiye a k'asan akwatin ta, bata sake bin ta kan zoben ba sai yau da Allah yayi za ta sake sanya idanuwan ta a kai.
     A hankali ta d'auke idanuwan ta daga kan zoben, karaffffff suka had'a ido da Suhail da har zuwa yanzu ya k'asa d'auke idon shi a kan ta.
      Shiru suka yi su biyun suna bin junan su da kallo aka rasa mai k'arfin halin d'aga zoben.
      Sun kai kusan minti biyar a hakan suna sak'a abubuwa da dama a zuciyoyin su kana Suhail yayi k'arfin halin d'auke idon shi a kan ta, ya d'auki zoben yana jujjuyawa a hannun shi yace." *WAYE MACUCI"?* '''Suhaib ko Suhail?''', ya jefa mata tambaya.
     Murmushi ma d'auke da hawaye ta sakar mishi tana kallon, a hankali ta taka zuwa gaban shi, ta tsugunna tace" to me zan ce? cewa zan yi yaya na ne macuci, ko kuma masoyi na kuma miji na?
      Now over to you, *"WAYE MACUCI"?* yaya na ko kuma miji na.
      Ba tare da ya amsa mata ba ya mayar da zoben ya ajiye, ya mayar da kayan akwatin ya rufe ya ajiye a wajen da ya d'auka, ya rike hannun ta ta mike tsaye ido cikin ido suke kallon juna yace" yayan ki mai laifi ne, yayi miki manyan laifuka a baya, d'aga daga cikin laifukan da yayi miki shine ya b'ata miki suna a idon duniya, ya kafa mishi shaidan da har a bada ba zai goge a idon duniya ba, daga baya ya gane kurakuren shi ya ya kuma d'auke ki da muhimmanci, ya maida ki tamkar ciki d'aya kuka fito da shi, and a shirye yake da ya fighting miki right d'in ki wato ya kwace miki y'ancin ki a idon duk wanda ya nima ya wulakanta ki".
       Mijin ki kuma shine wanda yayi sandiyan duk abubuwan da ya faru da ke a baya, har ya zamanto ana kyamar ki. Da wannan dalilin ne yayan ki yayi amfani da shi wajen kafa hujjan cin zarafin ki". Mijin ki shi ne ya rusa darajar ki da k'imar ki a lokacin da kike tsananin bukatan taimako, amma a shirye yake da ya nema miki farin ciki mai d'orewa, ya mayar da ke tamkar sarauniyar da take mulki a duniya baki d'aya".
      Yana kawo nan ya ja dogon numfashi yace" ga amsar tambayan ki nan, kai na ya gama kullewa, na kasa gane *MACUCI* tsakanin yayan ki da kuma mijin ki, ki taya ni banbance tsakanin mutane guda biyu wato yayan ki da kuma mijin ki".
     Makalallun hawayen da ke d'auke a fuskan ta ne suka samu daman gangawa, ganin kuka na neman kwace mata tayi saurin toshe bakin ta cikin muryar kuka tace" na manta da dukkan shari na tuna da dukan alhairin yaya na da miji na, na rungumi k'addara, sannan na d'aya cewa haka rayuwa ta zo min, sanan kuma na yafe ma dukan yanda ya *CUCE NI* da yaya na da miji na.
        Ta yaya zan k'ira yaya na da sunan *MACUCI*, bayan ya maye matsayin ya Abdallah a rayuwa na?
     Ta yaya zan k'ira miji na da *MACUCI* bayan shine farin cikin rayuwa na?
       Tana kawo nan ya rungume ta kyam a jikin shi yana bubbuga bayan ta a hakali da tsigar lallashi har ta daina kukan kana ya sanya mata hijabin suka bar gidan sai shagon saloon.

       Bayan tafiyan su da awa uku sai ga dad ya shigo gidan, mum ta fito ta tarb'e shi kamar yanda ta saba yi, ta had'a mishi ruwan wanka tare da taimaka mishi ya rage kayan shi, daga nan kuma ya fad'a band'aki. Yana gama wanka ya fito ta shirya shi fessssss cikin dark blue d'in jallabiya, ta fetsa mishi turare daga nan kuma ta gayyace shi zuwa dinning.
      Yana zama ta hau gabatar mishi da abincin da Jummai ta fawa ya zauna ya fara ci.
     Sai da ya cika cikin shi yayi nakkkk kana suka koma parlor suna hirar su. A cikin hirar ne take tuna mishi maganar tarewan Aysha.
 
     

*eedatou* 
        ~Y'ar mutanen Dengi~

WAYE MACUCIWhere stories live. Discover now