Page 18

898 76 5
                                    

🏵🏵☀☀🏵🏵☀☀🏵🏵
          *☀WAYE MACUCI☀*         
🏵🏵☀☀🏵🏵☀☀🏵🏵
        '''Suhaib koh Suhail'''

                       ©
'''Marubuciyar Rayuwar Sumayyah'''

    *SA'EEDA MUSA DAUDA😍*

'''Follow and ✅ote me on Wattpad''': *SaeedaMusaDauda*


*BESTORED TO MY LIL SIS* ''' SUMAYYAH MUSA DAUDA'''

        '''Saboda posting din da nake yi a whatsapp da facebook yasa na samu kara cin followers da voters so na canja tsarin post dina zan dinga turo novel a wattpad kafin na turo a whatapp da facebook da fatan zaku bani had'in kai ina mugun yin ku irin sosai d'in😍😍'''

                        1⃣8⃣

Da isowan su suka tarar da mum a dad zaune, dad ya tsura ma watch d'in bangon parlourn yana kallon yanda agogon ke rotating clockwise mum kuwa ta rafka uban tagumi tana jiran fitowan kids d'in ta,,
     sallama su Suhaib suka yi musu suka amsa kana suka nemo wuri suka zauna a k'asa iyayen na su na seats, bisa al'adar gidan su duk ranar da suke da meeting a ranar ne ake tuntub'ar kuwa matsalolin shi sannan a samu hanyar warware ta ad kuma every ending month suke meeting sai kuma gashi rana a tsaka an tara su yin meeting da alama akwai muhimmiyar dalilin da ya sanya dad d'in yin hakan kenan,,
     abun da Suhail ke ta tunani kenan a zuciyan shi bai ankara ba sai jin muryar dad yayi ya gyara murya yana cewa" bismillah kids lets start with prayers and end of with prayers so some one should volunteer and pray for us,,
    saurin mai da fuskan shi kan d'an uwan na shi yayi yana mishi alama da yayi addu'an Suhail ya k'aucar da kai kamar bai gane abunda yake nufi ba, lura da hakan da mum ta yi yasa in other not to waste time ta fara kwarara addu'o'i tana iddawa suka shafa baki d'aya,,
      sai da suka natsa bafore dad ya kuma gyaran murya a karo na biyu yace" Alhamdulillah hak'ik'a mun gode ma Allah mad'aukakin tsarki da ya sa muka fi k'arfin bukatun mu Allah ya dad'e kare mu daga duk wata musiba da ke tunkaro mu,, 
     su duka suka amsa da cewa" ameen" kana dad ya ja nannauyan numfashi ya sauke, ya cire hulan kan shi ya d'ora a kan table tare da hard'e hannayen shi d'ora a kan table ya dube kids d'in shi ya d'ora da cewa" wato abunda ya sa kuka ga na tara ku a nan shine akwai wasu changes da na lura yana faruwa a gidan nan wanda idan bamu yi gaggawan magance shi a gidan nan ba zai zamo mana tashin hankali a gidan nan,  kawo nan yayi shiru kana ya d'ora da cewa" most especially kai Suhail mun rasa gane kan ka a gidan nan always kana cikin kunci muma ka san ya mu a cikin ta, i will like you to share your problem with us idan ma aure kake so a maka kana tsoron fad'a mana gudun kar mu k'i ammince maka feel free and tell us we are ready to give you your desires", dad ya fad'a tare da tsare shi da ido.
    a d'ararace Suhail tsunne kan shi a k'asa ya tsotsa kai yace" i'm damn dad there is nothing more mawai zazzab'i ne ke damuna,,
     ba tare da dad ya gamsu da maganar shi ba a tsawace  yace" look !!! bana na son ka b'oye min komai but since i insisted ka fad'a min but you refused shikenan ku tashe ku tafi but let me remind you koh da zuwa gaba ka tunkaro ni da wata magana wallahi sai ran ka ya b'ace, ooyyyaa get out of my sight before a give you a slap ya fad'a a fusace cuz he taught this is the only way da Suhail zai iya fad'a musu damuwan shi tunda su mum sun yi lallashin duniya ya k'i ya fad'a musu
      marairaice fuska Suhail yayi yana pleading d'in dad" i'm sorry for making you upset its not my fault dad ba laifina bane da na hiding muku komai i have no way than to do that, i knew that my problem is also yours but forgive me please this time around ba zan iya fad'a muku wannan abun kunyar da na aika ta ba, saurin jan bakin shi ya suke yayi dan idan yaci gaba da maganan toh abu d'aya zuwa biyu zai faru, koh ya fad'a musu main abunda yake itching d'in shi a zuciya koh kuma ya fasa musu kuka gashi kuma koh kad'an ba ya son yin kuka a gaban parent d'in shi dan yin hakan ba k'aramin ta da musu da hankali zai yi ba,,
    muryan da yaji yayi magana a fusace yace" if you like keep hiding thing you are on your own but duk ranar da kwai ta fashe maka don't you ever plead us for assistance ka dai ji na fad'a maka,,
     hankali a tashe Suhail ya faki idon dad yayi ma mum da har zuwa yanzu hannun ta na dafe da kuncin ta yayi mata signal da ido tare da had'e tafukan hannayen shi biyu yana mata nuni da ta taya shi ba ma dad hak'uri ita kuwa harara ta sakar mishi dan ita ma ran ta ya fara b'aci dan ta d'auke hakan a matsayin rainin sense wai ace a yi ta tambayar mutum yana b'oyewa, cire hannun ta a kuncin ta tayi ta ja tsaki mai k'arfi "mttsssww" dan sai da dukan su suka jiyo da fuskokin su suna kallon ta, rai a b'ace tace" don't thing i'm by your site and kuma kar ka tab'a tunanin zan cigaba da saka damuwa a raina ne, hankali na a kwance jan ci gaba da mu'amala ta kamar ta farko har zuwa ranar da zaka bayyana wa kowa halin da kake ciki.
     duk da dai cewar Suhaib ya fahimci cewa ba har zuciya mum ta fad'a hakan ba illa bata da wani zabi than ta yi hakan, ya dube mum cike da tausayin d'an uwan na shi ya marairaice fuska yace" mum you have to calm down please duk hakan bai taso ba kamata yayi mu sake bashi time sannan mu k'ara tutub'an shi idan yak'i kuma shikenan",,
      "uummmm son kenan nawa nake tambayar yaron nan akan ya fad'a min damuwan shi amma ya k'i fad'a toh yaya kake so nayi, so kake na tusa shi a gaba na yi ta lallashin shi kamar k'aramin yaro koh so kake na goge shi a baya na dan na damu da na san damuwan shi  har zuwa san da ya fad'a mana kafin na sauk'e shi ?, bayan kai kan ka shaida ne a kan irin lallashin yaron nan da nayi ta yi ma yaron nan a gidan nan".
       Suhaib ya bud'e baki zai kuma magana dad ya dakatar da shi a tsawace yace" shut up my friend !!!, ka fi mu sanin abunda ya dace mu yi ne ?? so kar na kuma jin ka furta wata magana a nan tunda kunnen k'ashi ne da shi,,
      saurin tsuk'e bakin shi yayi dan ganin yanda dad ya d'au zafi da yawa bai kuma cewa komai ba har suka rufe taro da addu'a su biyun suka yi part d'in su suka bar su mum na tattaunawa a tsakanin su.
     Suhail ne ya bud'e k'ofa ya fara shigowa sannan kuma sai Suhaib, yana shiga ya mai da k'ofan ya rufe ya jura hand d'in shi a cikin aljihun wandon shi tare da tak'owa  a hankali zuwa wurin Suhail da tsaye a jikin window ya sarke hannayen shi yana zuba ma cars d'in da ke jere a parking space ido yana kallon yana kallo but a zahiri tunanin yarinyar da ya cuta ne ya tsaya mishi a rai yana tunanin yanda zai yi ya gane ta dan ganin da ya mata time d'in da yake maye ba zai tab'a iya gane fuskan ta ba, but duk ranar da ya runtsa idanuwan shi dare da rana amon muryar yarinyar ne ke mishi yawo a kan shi da take cewa"bawan Allah ka ji tausayi na kar ka yi garguwa da lalurata   ka cutar da rayuwa ta........ka dubi maraici na, ka tausayamin,  wayyo ni Aysha wai ba mutane ne a wurin........., ya Abdallah ka kawo min d'auki...,,
     wasu zafafan hawaye ne suka tsiyayo mishi a idanuwan shi na tausayin ta dan a maganar ta ya fahimci cewa nakasasshiya ce, bai san me yasa ba a duk lokacin da ya tuna kalaman yarinyar ya kan tsinci kan shi da tsananin tausayin ta da kuma tsanan kan shi,,
     wani tunani ne ya fad'o mishi a rai a game da sunan da ta ambata" ya Abdallah" toh wanene ya Abdallah da kuma matsayin shi gare ta,,
     Suhaib da ya spending almost 20 hours yana kallon d'an uwan na shi kasa jurewa yayi dan k'iris ya rage ya zubb da kwalla shima, a sanyaye ya dafa kafad'an Suhail  yace" me yasa kake wahalar da zukatan mu ne bayan ka san mu duka muna cikin damuwa, zuwa yanzu ya kamata ka fad'a mana damuwan ka dan mu samu rest of mind, and also about about our promised (the missing ring) ".
     Jin an tab'o shi ta baya da kuma muryar d'an uwan na shi da ya jiyo ne ya sa shi saurin wiping d'in hawayen face d'in shi ya juyo da sauri yana kallon Suhaib ido cikin ido k'irjin shi na bugu ya ce" ba laifina bane na ke b'oye muku abunda ke damu na ba zan iya bud'e baki na furta muku hakan bane, and about the promised har yanzu na tare da ni but ba zan iya fad'a maka inda yake ba amma ina ji a jikina ba zan tab'a rabuwa da alkawarin mu ba, na tanadar da shi ne a wani wuri saboda muhimmancin shi gare ni amma ina tabbatar maka da kaina zan samo maka a cikin kwanakin nan may be a ranar da zamu Dengi koh kuma bayan barin mu Dengi i promised".
     murmushi ne ya kwace ma Suhaib na jin k'aryar da Suhail ya sharara mishi dan ya gane hakan ne a kwayan cikin idanuwan shi,,
      ware hannayen shi yayi irin ta oho d'in nan koh ma menene zamu gani kamar yanda ka yi alkawari, idan ma misplacing d'in shi ka yi time will tell, kana ya mai da hands d'in shi a aljihun wandon shi yana zagaye shi yace" uuuhhhhm alright time will tell and with time zamu gano komai,,
     a zaton Suhail koh Suhail ya gane abunda yake nufi ne a take ya zaro ido yana raka shi da su shi kuwa Suhaib ganin yanda yake zare eyes kamar an tare burgu a rami ya bala'in bashi dariya but sai ya dake ya murmusa kawai yayi shigewan shi d'aki ya bar Suhail a tsaye kamar gawa.
     
      B'angaren Aysha kuwa tun ranar da aka kawo lefen ta da Ilu zuciyan ta ta k'asa samun nusuwa gashi an rasa wanda zai hana inna maganar d'aurin auren nan dan duk ranar da abba ya d'au zafi a kan maganar auren inna Larai saka mishi kukan kissa take yi yi tana cewa" wato ita bata da ikon aurar da y'ar shi kenan koh so yake ya gwada mata bata da iko da Aysha", hakan ne yake sa shi saukowa daga fushin da yake yi, ba dan ran shi ya so ba ya ammince da maganar auren har Allah yayi yau saura four days dai dai da ranar da y'an uwan shi zasu ziyarce shi.

       Safiyar litinin Inna ce na hango a d'aki tana ma ya Abdallahi warning a kan ya fita harkar Aysha dan koh kad'an baza ta bari tilon d'an ta ya aure Aysha ba,,
     a cikin maganar ta ne na ji tana cewa" ban san me yasa ka nace ma yarinyar nan ba wallahi dubi yanda ka zabge ka rame lokaci guda dan dai kawai a kan yarinyar nan, da ace zaka san irin gatan da nake maka da tuni ka fita harkar ta dan Aysha ba matar aure bace sammm,,
     ya Abdallah ya dubi mahaifiyar shi da damuwa a fuskan shi tafffff yace" haba inna wata irin gata ce kike ik'irarin kina min bayan ke da kan ki kike shirin tarwatsa farin ciki na da rayuwa na ??,,
     sassauta murya k'asa k'asa irin ta munafurci ta inda babu mai jiyo ta sai d'an tayi tace" hhhmmm kwarai kuwa koh shakka babu abunda na fad'a maka hakan take dan Ilu kwarton Aysha ne dalilin da ya sa kenan ka ga nake dad'a nacewa a kan auren ta da Ilu, dan na sha kama su turmi da tab'arya da idanuwa na, ka ga duk b'ata ran da take yi bai kai zuci ba kawai tana yi ne na kan fuska dan kar a gano su, tana fad'a ta yi shiru tana jiran me zai ce,,
     rufa bakin ta ke da wuya ya Abdallah yace" Subahanalillah sammm wannan maganar bata dace ba inna, bai kamata ace kina aibata y'ar da ta taso a gaban ki ba, na sani Aysha baza ta tab'a aikata abunda kika fad'a ba dan mace ce mai natsuwa da tarbiya,,
     burning faska inna tayi cike da borin kunyar rashin samun biyan bukata tace" k'arya kake tunanin zan maka ??", wallahi kar ka bari son da kake ma nakasasshiyar yarinyar nan ya sa nayi fushi da kai Abdullahi", haka dai tayi kullo sharrin da ta san zai iya rusa dukkan soyayyan da kuma dasa kiyayyar Aysha a gun ya Abdallah amma koh kad'an ya Abdallah bai yarda da zancen ta ba illah nuno mata illa da kuma rashin dacewan kiyayyar da take nuna ma Aysha karara yake yi.

      bayan faruwar hakan da two days ya Abdallah ya shiga d'akin Aysha da sallama a bakin shi ya tarar da ita tana kan sallaya hannun ta rik'e da Qur'anin nan ta makafi tana k'ira'a,,
     ba tare da ta amsa sallamar ba ya shigo ya zauna a kan kujerar ruba da ke gefen ta kad'an ya zuba ma hannun ta ido yana kallon yanda take tattab'a Qur'anin da hannu a zuciyan shi yana mamakin yanda makauniyar take kwararo da karatu, sometimes idan ta yi mistakes sai ta sake d'ora hannun ta a daidai wurin da tayi mistakes d'in kamar majic sai ka ga ta d'au gyara tsafff,,
     zancen zuci ya kama yi shi kad'ai yana cewa" iko sai Allah sarkin da babu kamar shi, idan ba ikon Allah ba ta yaya makafi zasu iya karanta Qur'ani bayan idanuwan su a rufe suke ?? uummm Allah kenan sarkin da babu kamar shi mai kowa mai komai mahaliccin sammai da k'assai",,
     idanuwan shi ne suka sauk'a a kan zoben da ke sanye a hannun ta a lokacin da ta idda k'ira'ar tana k'ok'arin rufe Qur'anin ta maida a  ma'adana,,
     sai da ta ajiye Qur'anin kana ta amsa mai sallamar k'asa b'oye murnar ta a fili ta yi saboda ganin shi da ta yi dan rabuwar ta da shi tun lokacin da suka dawo daga chemist suka tarar da inna da y'an kawo lefe har inna tayi ta rafka ma ya Abdallah masifa a kan ya fita harkar ya Aysha,,
     tsinkayo muryar ta yayi tace" ya Abdallah yau kai ne a d'akin nawa maraba da kai yara na",,
     murmushi ya mata kamar yana ganin shi yace" toh ya na iya bayan k'anwa ta ta k'i ni ai dole nayi nesa da ita gudun kar ciwon zuciya ta kai ni makwanci na", ya k'are da tsigar tsokana,,
     rik'e hab'ar ta tayi tace" lalalaaaa yaya na wannan sharri haka ?? a'a babu ruwana ni dai ",,
      "da sharri na miki bayan kin san cewa gaskiya na fad'a ??, ya jefo mata tambaya yace" uuummm k'anwa ta a ina kika samo wannan zoben da ke sanye a hannun ki ne dan na ga alamar zoben da tsada and koh manyan mutane masu kud'i da wuya ki gan su da irin shi, ya fad'a tare da tsare da ido like yana kallon shi,,
      gaban ta ne ya yank'e ya fad'i rassss ba tare da ta amsa tambayar ba tayi saurin basar da tambayan zuwa wani hira da ban wanda ya dangace halaiyan d'an Adam thank Allah bai kuma d'auko mata zancen ba suka sha hirar su har da wasa da dariya kamar babu wata matsalan da ke damun su.

       Yammacin ranar Aysha ta tashi da matsananciyar zazzab'i duk abunda ta ci a take zata amayo shi, lura da hakan da inna ta yi ne ya sa ta debo abinci ta kawo mata dan koh kad'an zuciyan ta bai yi na'am da amman da Aysha take yi ba,,
     dan mugun ta inna tutsiye ta a gaba tayi a kan lallai sai ta ci abincin nan haka dai ta daure tana matse idanuwa tana ci, tana kai loma uku ta ji amai na taso mata da sauri ta d'au sandar ta tana k'orarin fita suka yi kicib'is da ya Abdallah da ke k'ok'arin shigowa d'akin ai kuwa sai ga amai shhuuuu" ya taso mata sai a jikin ya Abdallah da ya yayi saurin taro ta,,
      da sauri inna taso domin ganin kwakwaffff tana zuwa ta rafka salati da k'arfi tace" na shiga uku magana ta ta tabbata ciki Aysha  !!!



         '''Saboda posting din da nake yi a whatsapp da facebook yasa na samu kara cin followers da voters so na canja tsarin post dina zan dinga turo novel a wattpad kafin na turo a whatapp da facebook da fatan zaku bani had'in kai ina mugun yin ku irin sosai d'innan😍😍'''

Please Share
             Comment
              Follow and vote page on wattpad

*Sa'eeda ✍🏻*
     ~Y'ar mutanen Dengi~

WAYE MACUCIWhere stories live. Discover now