Page 47

727 41 0
                                    

🏵🏵☀☀🏵🏵☀☀🏵🏵
*☀WAYE MACUCI☀*
🏵🏵☀☀🏵🏵☀☀🏵🏵
'''Suhaib koh Suhail'''

***********************************

® *REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS P.M.L*💭💭💭

_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_

# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035


©
'''Marubuciyar Rayuwar Sumayyah'''

*eedatou😍*

'''Follow and ✅ote me on Wattpad''': *eedatou*


*BESTORED TO MY LIL SIS* ''' SUMAYYAH MUSA DAUDA'''

4⃣7⃣

Suhaib na barin gidan granny gida ya nufa, da isowan shi ya shige ciki ya mum da dad a zaune a kan kujera a parlor suna tattaunawa, rage tsawo yayi ya gaishe su fuska a d'aure suka amsa mishi ba su kuma bi ta kan shi ba suka ci gaba da abunda suke yi, shi koh yana ganin haka ya ja jiki sumi sumi ya bar wurin ya haura benen da zai sada shi da site d'in su zuciyan shi cike da tunanin disgracing d'in shi da Aysha tayi a yau.
Yana isowa d'akin cikin sa'a bai tarar da d'an uwan nashi ba, had'e kan shi yayi da jikin bangon d'akin tare da kai ma bangon d'akin bugu da k'arfi kana ya jiyo da fuskan shi da ta cika da hawaye k'iris ya rage su zubo mai ya hau magana da k'arfi muryar shi na rawa yace" why !!!, why !!! Aysha, me yasa kika tsane ni ?, na san ni mai laifi ne a gare ki ki please kar ki duba girman laifin da na miki, ki taimaka ki k'arb'i soyayya na,, zuciya ta ta gama k'amuwa da k'aunar ki, soyayyar ki ta gama ratsa jikin jikina, i'm deeply in love with you Aysha, ban san ta yaya zan iya controlling kaina a kan irin son da nake miki ba, my brother doesn't deserved you at all infact shine babban *macuci* ba ni ba", I love you Aysha !!! ba zan iya rayuwa babu ke ba", yana kawo nan kuka ne ya kwace mishi bai san sanda ya durk'usa da gwiwa ba yana aikin rusa kuka".
Maganganu kala kala ya hau yi yana kukan nadama, ganin babu sarki sai Allah da kyar ya samu ya lallashi zuciyan shi ya hak'ura da kukan".

B'angaren Suhaib kuwa yau kwata kwata bai sanya Aysha a ido ba kasancewar a mak'are ya taso daga barci time d'in kuma har Aysha ta tafi makaranta, tasowan shi ke da wuya koh wanka bai tsaya yayi ba ya d'au car key d'in shi da saurin ya fice daga site d'in su ya nufi gidan su Sadeeq.
Sa'a yayi bai tarar da kowa a parlourn ba da mugun gudu ya haura matakalan benen ya shige d'akin Sadeeq yana shiga ya maida k'ofa ya rufe da k'arfi ya jingina bayan shi da jikin k'ofan yana hak'i".
Sadeeq da jin k'arar sakin k'ofa ya fito da sauri yana zazzaro ido a tsorace zai bar d'akin yana ganin Suhail jingine a jikin k'ofa ya sak'i ajiyar heart dan ba k'aramin tsorata yayi ba".
Kallon Suhaib yayi yaga yanda ya wani bircike bugu da k'ari kuma ga wani uban k'ashin wuyan da suka firfito mishi saboda tsabar rama, tausayi sosai ya ba ma Sadeeq cike da tausayin shi ya hau jifan shi da tambaya yace" friend me kuma ya sake faruwa ba dai su mum ba koh?"
Maimakon ya bashi amsa sai ya hau sura ma Sadeeq ido lokaci guda hawaye na ta bin fuskan shi,,
"Ya illahi wannan wacce irin musifa haka ?, badai su dad sun k'i hak'ura ba koh?, wallahi dama abunda nake guje maka kenan tun farko da kake ta b'oye musu, da ka fad'a musu halin da ake ciki da hakan bai taso ba dan na san komai zai zo da sauk'i amma ka k'iya gashi nan yanzu ka dad'a b'ata komai,,
Cikin muryar kuka Suhail yace" i'm going to die, rayuwa ta tazo k'arshe friend, ta yaya zan wanke kaina daga laifin da na aikata ?, yaya zan yi da soyayyar Aysha a zuciya na ?, friend up to now su mum sun k'i bani dama na fad'a musu ainihin abunda ya faru tsakanina da Aysha", ya fad'a cike da raunin zuciya.
Na san dole a yi haka friend, i told you tun farko kai ka b'ata komai, babu irin lallashin da ban maka ba a kan fad'a musu halin da ake ciki but you refused yanzu ga shi nan komai ya ruguje mana".
I know that i made a very big mistake, let's try another way, ka nemo mana wata hanyar da zan bi na wanke kaina daga laifin da na aikata".
Kafadar shi Sadeeq ya dafa yana kallon shi cikin ido yace" no way friend banda wata hanyar da ta wuce muje mu ba ma su dad hak'uri".
Da mugun mamaki Suhail ya sharo hawayen shi ya dubi Suhail yace" kana tunanin cewa su dad zasu saurare mu after all hakurin da na din ga basu a baya?,
Fuzar da iska Sadeeq yayi yace"insha Allah zan musu bayanin komai fatana Allah yasa su saurare mu".
Sannu a hankali Sadeeq ya hau lallab'a Suhail har ya samu ya saki jiki suka yi sallama da juna Sadeeq ya koma gida.
Isowan shi gida ke da wuya bai zarce koh ina ba sai d'akin Aysha, da isowan shi ya hau bin d'akin da kallo yana tunano moment da suka spending lokutan da take mak'auniya a take ya ji wani sabon son ta na diran mishi a zuciya, dafe zuciyan shi yayi da hannu yana magana kamar wani zararre yace" ni nafi dacewa da ke Aysha, ni ba *macuci* bane ni cikakken masoyi ne, kar ki manta ni na nuna miki so a lokacin da babu wani d'a namijin da zai so ki, Aysha tun kina d'auke da cikin da bansan cewa nawa bane na so ki, toh ta yaya na zama *macuci*?, ni ba macuci bane Aysha ki bani dama na fad'a miki gaskiyan abunda ya faru na san idan kika ji zaki tabbatar da cewa ni ba macuci bane", sharo hawayen shi yayi ya fice daga d'akin.
Yana saukowa kenan Aysha da dawowan ta kenan daga school dad ya biya ya d'auko ta ta shigo gidan tana kwala ma mum k'ira tana cewa" mum !!! mum where are you i'm back".
Jin muryar Aysha na k'iran ta mum ta fito da murmushi d'auke a fuskan ta, tana fitowa ta ga dad a gaba Aysha na biye da shi a baya yiyin da ta ratayo school back d'in ta a hannu". K'arasowa gun su tayi da sauri ta k'arb'o jakan dad tare da jawo d'iyar ta a jiki ta bata peg a gishi tace" daddy's pet "you are welcome, nayi kewan ki sosai daughter da kika tafi kika bar ni".
Cikin shagwab'a tace" ummm ummmm mum ba wanin nan ban yar ba bayan koh d'aukata baki zo ba".
Allah da gaske daughter rashin ki a gidan nan sai na ga gidan ta min fad'i", mum ta fad'a kuma har k'asan zuciyar ta tana nufin abunda ta fad'a.
Waino eyes balls d'in ta tayi tare fad'awa ragwabbb a kan kujera lokaci guda ta a sakin y'ar k'ara tace"wahhhhhh mum na gaji sosai yau wallahi baki jin yanda jikina ya min tsami ba, ohhhh i forgot to tell you, kin ga yanda yau aka min public disgrace kuwa ? duk sai na ji mutumin ya fice min a rai".
Zama mum tayi a gafen dad tace" wa kuma ya tab'o min ke fad'a min na ji", hmmmm wallahi wani d'an rainin hankalin maths teachern mu ne kawai ina zaman zamana ya koro ni daga class kuma har da duka min tsawa what i hate the most".
Kallon ta dad yayi cike da tuhuma yace" anya kuwa ba wani abun kika mishi ya koro ki ba?, kamat gaske ta marariraice murya tace" oohh no da babu abunda na mishi kawai dai haka teacher din yake fa".
Ba tare da ya kuma furta komai ba ya ciro wata sabuwar waya fara kalll da ita ya mik'a ma Aysha yace" daughter this is my gift nabtaya ki murnar bud'ewan idon ki , tun a Madina na sayo na b'oye shine yanzu na d"auko miki.
Woowww dad dad Allah ya biya ka ga gode sosai, k'arb'a tayi tana jujjuya wayan tare da yaba kyan wayan mum kuwa sai masy dariya take, a wurin dad ya b'allo mata sim card ya bata ya nuna mata yanda zata yi amfani da wayan, bata sha wata matsala ba tahaddace kafff abubuwan da dad ya koya mata tana tsallen murna ta haura matakalen benen da zai sada ta da d'akin zucinyan ta cike da farin ciki su mum suka raka ta da ido.
Suhail na jiyo muryar ta lab'e a corridor ita kuwa hankalali kwance take taka matakalan benen tana jujjuya wayan a hannun ta lokaci guda kuma tana rero wak'a a bakin ta, tana isowa dai dai inda Suhail yake b'oye taji an finciko ta da k'arfi ta fad'a jikin mutum zata kwalla k'ara kenan yayi saurin rufe bakin ta da tafin hannun shi, kusan suman tsaye ya rage Aysha ta yi kasancewar hurin da duhu bata san cewa shi ne ba,,
Wani irin shocked su duka suka ji wanda tun da suke basu tab'a jin irin shi ba sakamakon had'uwar fatan jikin su da ya had'e da na juna, kiittttt wuta ta d'auke musu, tsigar jikin su ya tashi yaarrrrrrr a take wata muguwar kasala ta saukan musu su duka musamman Suhail da farar jikin Aysha ya rikita mishi kwanya ga kuma booobs d'in ta da suka tokare mishi chest kamar da gayya suna bin beating d'in zuciyar ta suna tsalle up and down, habawa bai san sanda da ya kai hannu yana shafo mata jiki ba hakan da yayi kuma yasa jikin Aysha ya d'au rawa ta hau kiciniya kwace kanta.
Sai yanzu Suhaib ya ankara da abunda yake yi, sautin cire hannun shi yayi daga jikin ta ya sa hab'a ya tallab'o da fuskan ta suka k'ura ma juna ido suna ma junan su kallon ido cikin ido lokaci guda dukan su da sun jin beating na zuciyoyin su.
Zaro firgitattun idon ta tayi tana nuno shi da hannu d'aya tace"you? ", ba tare da ya amsa mata ba ya tsugunna a gaban ta ya rik'o hannun ta hawaye na gangarowa a saman fuskan shi cikin murya mai kama fa ta kuka yace" gani natsugunna a gaban ki ki d'au kussan hukuncin da ta dace da ni amma please kar ki gujeni Aysha", wallahi ba da son raina bane tsautsayi ne.
Kallon ta tsayi yi lokaci guda k'aunar shi da bak'in abunda ya aikata mata ya dirar mata a zuciya, kuka ne ya kusa kwace mata amma sai ta dake ta dube shi tana jin zafi a zuciyan tace" kana tunanin zan yarda da kai ne Suhail koh har yanzu baka gama biyan bukatar ka a kaina bane ka dawo gare ni?
Na san nine silar zuban hawayen ki but please sassautawa zuciya ta na samu Sa'eeda rad'ad'in azabar k'aunar ki a cikin zuciya ta, ban tab'a aikata zina ba abunda kika ga ya faru tsakanina da ke k'addara ne, wallahi ba a cikin hayyacina na d'and'ana zuman ki ba, sharin huld'a da b'ata garin abokin ne", ya fad'a lokaci guda yana bin ta da kallon ido cikin ido.
Me yasa kake furta maganar da hankali ba zai iya d'auka ba, koh zaka iya tunano lokacin da amon murya ta ke ta dukan dodon kunnen ka ina magiya ina baka hak'uri akan ka kyale ni ?, me yasa a lokacin ba ka saurare ni ba sannan kuma baka tausayawa halin da nake ciki ba ka gama kwasar garar ka ka barni a yashe a wurin babu koh d'igon imani a zuciyan ka balle kayi tunanin taimaka mini, tsayawa da maganar ta yi a tsakamakon hawayen da suka gangaro mata a fuska, sai da ta sa hanno ta sharo hawayen kana tace" i don't know why my heart always beats for you, ban san me yasa har yanzu zuciyata take k'aunar ka ba kuma na k'asa cire son ka a zuciyata, jim tayi ta tsaya for some minute kafin ta bud'e baki in a cool, sweet and slowly voice ta d'ora da cewa
"Suhail i love.... you..... and always do,, ta fad'a da karfi, da sauri ya d'ago fuska yana kallon ta da mugun mamaki a zaton shi koh mafarkin da ya saba yi akan cewa ta yafe mishi ne.
Ba tare da ya yarda da maganar da ya fito daga bakin ta fa yace" me yasa kunnuwa ta suke yaudara na da cewa kin ammince eeyeeeee, i know is very heart ki ammince da ni yanzu"
Instead of ta bashi amsa sai ta jingina jikin ta da matakalar benen ta hard'e hannayen tanim tana kallon yanda hawaye ke ta bin fuskan shi, murmushi ta mishi tare da kai hannu ta waping mishi tears ba tare da ta daina murmushin ba, shi kam mutuwar tsaye yayi yana mamakin al'amarin dan ya kasa yarda, lokaci guda yana ji jina al'amarin cikin zuciyan shi".
Cikin sanyin murya ta dube shi kuma har yanzu fuskan ta na bayyana alamar murmushi tace" yaya na, a da na k'ira ka da *macuci* amma ni kaina na san cewa kai masoyi ne in the other hand kuma zan iya k'iran ka da jarumi,,
Yes of course dole na furta hakan ka cancanci na k'ira ka da suna jarumi saboda kai ka nuna min k'auna tsantsa, baka kyamace ni ina matsalin mak'auniya ta ba, baka nuna min kyama lokacin da nake d'auke da cikin ka a jikina ba tare da sanin cewa kaine ka yi min cikin ba, sannan kuma baka guje ni a lokacin da aka watsa hotona a idon kuniya a matsayin k'aruwa ba, wannan dalilai ne kad'ai suka wanke min tsanar ka a zuciya ta sannan suka canja min ra'ayi na akan ka, now I have forgiven, ka cancanci yafiya ta saboda abubuwan da ka min a rayuwa, ba ma wannan kad'ai ba koh dan su mum ma".
Murmushi farin ciki ne ya kwace ma Suhail, ji yake kamar an tsunduma shi a aljannah saboda tsabar fari ciki, wangale baki yayi ya tsaya sororo yana kallon Aysha dan gabaki d'aya ya rasa k'almar da zai yi amfani da ita wurin nuna mata godiyar shi, lura da hakan da ta yi ta kashe mishi ido d'aya tace" hi !!! you wannan kallon fa is too much ya fara wuce gona da iri eeehhh, ka bari sai ka biye bride price d'ina sannan kayi yanda kake so".
Saurin lumshe idon shi yayi a zuciyan shi yana hamdala ma Allah mad'aukakin sarki, a fili kuwa sai cewa yayi" i'm speachless, words can't express my gratitudes, i'm grateful baby, i'm waiting for the day that you will become mine, zan nuna miki k'auna tsantsa kuma na miki alk'awari ba ki ba b'acin rai, zan jiyar da ke dad'in da baki tab'a ji ba baby".
Kunyar kalaman shi ne ya kamata da sauri ta toshe kunnuwan ta ta saka gudu yana bin ta a baya yana cewa" baby bar ni na biya bashin kalaman da na jima ban furta miki su ba, zai kamo kenan cikin rashin sa'a ta shige d'aki tare da maida k'ofa ta rufe ta sa ta a lock ta jingina a jikin k'ofan tana maida k'ofan.
Bugun k'ofan ya hau yi yana mata magiya ta bud'e amma sai ta k'i, murya k'asa k'asa in a romantic voice tace" babyna ka kwantar da hankalin ka, zuciya ta da gangan niki na mallakin ka ne, na jima ina maka tanadi na musamman fatana Allah ya nuna min ranar da ni Aysha zan zama mallakin ka".
Maganar na shiga dodon kunnen shi yaji wani irin sanyin dad'i na ratsa shi, shafo suman kan shi yayi lokaci guda ya hau k'iran sunan ta amma ina tuni ta yi shigewar ta inner room,,
Gano hakan da yayi ne ya sa shi jan jiki da kyar yana d'aga k'afafuwan shi a kasalance ya bar site d'in ta ya d'auko k'asa ya shige parlour, cikin sa'a kuwa bai tarar da kowa parlourn ba dan su mum an shige other room tarbar maigida.

B'angaren su tee kuwa bayan maths teacher ya fita daga class d'in chamber d'in su suka nufa a zaton su koh zasu tarar da Ash a wurin, isowan su ke da wuya suka tarar da wurin wayam babu kowa, da yake closing hour ne daga maths class babu wani class d'in da suke da shi yasa suka yi tunanin koh dai ta koma gida ne, da wannan tunanin suka yi sallama da juna ita da hibb yayan tee ya zo ya d'auke ta hibb ma drivern ta ya d'auko ta su duka suka koma gida.
Tun a mota tee take ta damun yayan nata da zancen kawayen nata, tare da bashi labarin sharrin da suka yi mata wai tana b'oye musu shi, shi koh yana jin haka yayi murmushi haka kawai ya tsinci kan shi da son labarin yaran musamman ta wacce aka k'ira da Ash.
Suna isowa gida kamar k'aramar yarinya tee ta fito da gudu ta shige gida yayan nata na bin ta a baya.
Suna isa suka tarar da parent d'in su, hugging d'in su one by one tee tayi tare da zama a gefen dad d'in ta d'ora kan ta a saman kafad'an shi tana maida numfashi,,
Dad d'in ta ya dube ta cike da so da k'aune yace" my kid yaushe zaki girma ne ki daina guje gujen nan, you have grown enough and ready to get married fa", rigima ta sakar mishi cike da kunya ta turb'une fuska tana kallon yayan nata da ta jima tana dakon son shi a zuciyan ta tace" ya Abdallah ka ga dad koh ?, nawa nawa nake da zai min maganar aure duka duka fa shekarata 19years ne fa".
Kallon ta yayi yana mamakin ta wai ace mace kamar hibb tana danganta kan ta k'ank'anta, yarinyar da ta ji kayan aiki ga komai tubarakallah masha Allah. Murmushi yayi mata yace" gaskiya dad yake fad'a miki lil sis yakamata ki san kin girma gudu da tsalle ba naki bane".
Marairaice fuska tayi tare da barin jikin dad ta nufi wurin mum d'in tana buga k'afa da a k'asa da tsigar shagwab'a ta fad'a jikin ta lokaci guda kuma ta shagwab'e fuska kamar zata yi kuka tace" mum you see them ba, had'e min fuska suka yi su biyun dama can basa so na ke kad'ai ce me sona mum, uummm ummm babu ruwa na da ku ma".
Dariya su ya Abdallah suka hau yi mata, hakan ya tunzura ta ta hau kukan shagwab'a tare da shegewa jikin mum d'in ta tana kuka k'asa k'asa, ganin haka yayan nata ya taso ya rage tsawo a gaban ta tare da rik'e kunnuwan shi biyu yace" ki yi hak'uri k'anwata wasa fa nake miki, babu mai raba ki da gidan nan har sai kin fi haka girma".
Kan ya gama rufa baki ta taso ta hau tsalle tana murna har da yi ma dad gwaliyo wai yayan nata na son ta, dariya suka yi su duka kana
mum d'in ta ta taso ta shige shige kitchen ta fito da kulolin abinci a hannun ta ta dire bisa table kana ta koma wurin su ta shaida musu cewa lunch is ready.
Dad da mum ne suka fara hallara a dinning su kuwa d'akunan su suka nufa suka fad'a bathroom suka yi wanka, sai da suka gama shiryawa kana suka fito suka fice suka joining su mum a dinning.
Cin abincin su suke hankali kwance suna yi suna hira a tsakanin su har suka gama kowa yayi shigewan shi d'aki.
Da daddare kuwa tee na hango da yayan ta a parlour suna hira, a cikin hirar su ne naji ya Abdallah yace" tee kenan daga ganin mutane baku wani dad'e da su ba sai ki saki jiki da su har kina basu labari na koh bakya tunanin koh irin matan nan ne marasa kamun kai".
Kallon shi tayi tace" yayana kenan me zai sa nayi abota da marasa kamun kai ?, Allah dukan su suna da dad'in zama ga , ka san sai hali yazo d'aya ake abota, yanda ka san tagwaye haka muke a school kuma ina jin dad'in zama da su musamman Ash dan yarinyar akwai hankali sosai.
"Wai wacece Ash d'in nan duk kin bi kin dami mutani da maganar ta komai kice Ash komai Ash, ya fad'a a takaice tare da sura mata ido yana jifan ta da kallo.
Ai yaya na ba sai ka tambaya Ash ba domin gobe insha Allah zaka ga Ash d'in nan da kuma hibb da nake basu labarin ka, kasan me ?, ta jefo mishi tambaya.
"Ummm ummm sai kin fad'a, dazu da nake baka labarin su suma cewa suka yi ina b'oye musu yaya na, shi yasa nake so gobe nayi musu surprice su gan ka ka gansu".
Hmmmmm, ya ce mata tare da mik'ewa tsaye yayi mata sai da safe ya shige d'akin shi ya bar ta a parlor, haka kawai yaji baya son yawan magana tunda suka fara zancen Ash.
Bin bayan shi tayi da kallo sai da ta ga ya b'ace bata da gani kana ta d'auke idon ta daga kan shi tayi murmushi lokaci guda ta mik'e tsaye ta yi mik'a tayi mik'a tare da buga hamma kana tayi shigewan ta d'aki ta kwanta rufffff a kan gado tana tunanin yayan nata, juyi kad'an idan tayi sai ta rungumo filo tana sakin murmushi lokaci guda.
B'angaren ya Abdallah kuwa yana isa d'aki zagaye d'akin ya hau yi ya je ya dawo ya je ya dawo haka yake ta yi yana tunanin Ash, sosai tunanin ta ya tsaya mishi a rai ya hana shi sakat, daren ranar da ya juya sunan Ash ne yake mishi yawo a zuciyan shi.





*eedatou*
~Yar mutanen Dengi~

WAYE MACUCIWhere stories live. Discover now