Page 53

540 31 2
                                    

🏵🏵☀☀🏵🏵☀☀🏵🏵
          *☀WAYE MACUCI☀*         
🏵🏵☀☀🏵🏵☀☀🏵🏵
        '''Suhaib koh Suhail'''

***********************************

® *REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS P.M.L*💭💭💭

_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_

# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
      
          
                       ©
'''Marubuciyar Rayuwar Sumayyah'''

                   *eedatou😍*

'''Follow and ✅ote me on Wattpad''': *eedatou*    

                          5⃣3⃣

        Gudu yake sosai a hanya kamar zai tashi sama, sai wuce mutane fuuuuuuu yake da uban gudu, da kuma rusa traffic ba trafic da ya bi umurni ba, da taimakon Allah ya samu ya iso makarantar su tee, yana isowa ya k'ira ta a waya dan ta kwatanta mishi inda zai same su, ringing d'aya biyu ta d'aga da sallamar ta, kuna ina tee""?, tambayar da ya jefo mata kenan ba tare da ya tsaya amsa sallamar ta ba.
      Muna wurin gar......kitttttttt ya ji wayan ta mutu, ya k'ara kira yaji switch off, zufa na ya kuma k'argo mishi, haka ka kawai ya tsinci kan shi cikin tashin hankali mai tsanani,,
      sake bugo mata wayan ya kuma yi yaci ance switched off bai san sanda yayi wurgi da wayan cikin mota ba, ya fito ya buga k'ofan da k'arfi tare da buga saman motan da hannu d'aya da k'arfi yace" shiiitttttt", wasu uban mak'alallun hawayen da ya b'oye su tun daga gida ne suka shiga bin kuncin shi, bai san sanda ya kifa kan shi da jikin mota ba, zuciyan shi na mishi k'una yace" why teeeeee, me yasa a lokacin da nake bukatan wayar ki kika kashe ta?, kin san kuwa yanda zuciya ta ta kama da son ganin k'awar ki ash kuwa?,  haka dai ya dinga sambatu time to time yana k'iran wayan teee koh zai ci sa'a ta shiga".
     B'angaren tee kuwa tana cikin fad'a mishi inda zai same su taji wayar ta katse ta ciro a kunnen ta ta k'ira shi a tunanin ta koh matsalar network ne, tana danna wayar taji ta k'i kunnuwa, mtswwww ta ja tsaki tace" matsalata da phone d'in nan kenan bata rik'e caji, so take ta min bak'in ciki kar na sanya masoyina a ido, mstwww ta kuma jan tsaki tare da juyowa ta kalle su Ash da suka k'ure ta da idoooo suna zancen zuci".
     tace"Ash ara min wayar ki na k'ira ya Abdallah my phone was out of charged".
      Har Ash ta cire waya a bag d'in ta zata mik'a mata Suhail yayi saurin dakatar da ita ta hanyar aika mata da sakon harara da ya sa ta shan jinin jikin ta, ta hau kame kame tace" ops ba kud'i a wayan, na manta ban yi recharging ba wallahi."
     A sanyaye Suhail ya fiddo waya a aljihun shi kamar wanda aka sa shi dole yace" ga wannan ki k'ira shi, I think akwai digit a ciki".
     "Owk tnx", ta k'arb'a ta fara dailing ta fara dailing cuz ta haddace numban, hibb kuwa ta yi shiru tana jin su ba tare da ta furta komai ba.
     Wayar ce ta soma ringing tarrrrr tarrrrrr tarrrrrrr, cikin zak'uwa tee tace" ka d'aga mana !!!, ka d'aga wayan please kar ta katse, amma ina wayar ta katse.
     Sau 25 take k'ira wayan na nuna mata no answer har ta gaji ta daina ta mik'a ma Suhail wayan shi ta rik'o hannun hibb tace" k'awata muje ki gaka ni na dubo shi a waje may be ma yana daga gate".
      "Anya kina tunanin zamu iya samun shi kuwa?, hibb ta jefo mata tambaya".
      Me zai hana tee na san yanzu haka ya nemi wuri yayi parking kawai ki zo mije.
      Toh shikenan tee, haka suka tafi suka bar su Ash a wurin suka nufi gate suna dudduba wuri koh zasu ga ya parking mota duk tee ta wani birkice ta d'aga hankalin ta.
      B'angaren ya Abdallah kuwa sai da ya d'au lokaci a hakan kana ya shiga mota ya tada ya shiga bin hanya yana tambayar wuri, abu d'aya yake tambaya shine "gar....... ", da ya ji tee ta fara fad'a mishi.
      Wasu matasa ne ya hango suna doso wurin da yake, hannu yayi musu suka k'arasa wurin shi, sai da suka gaisa kana yace" dan Allah ina tambayar wani wuri ne, gar......, kawai aka fad'a min a waya wayar wacce ta fad'a ya katse gashi nayi ta k'ira ba'a d'aga ba".
     Suka yi jimmmm suna kallon shi suna tunanin inda suka tab'a jin sunan, kana d'aya daga cikin su yace" a gaskiya babu wata gar...... a nan makarantar koh dai garden take so tace maka?,
       eeeehhhhh toh ban da tabbaci amma ta yihu hakan ne, please koh zaku taimaka ku kwatanta min wurin koh na ci sa'a na same su a wurin", ya fad'a yana mai tsare su da ido.
     Babu komai, d'ayan ya fad'a kana ya d'ora da cewa" kaga wancan bishiyar mangwaron ", eeeehhhh na gani", toh kana isowa wurin zaka ga wata kwana daga hannun hagu ka shiga wurin, idan ka shiga kayi tafiya mai tsawo zaka ga wani bini mak'ek'en gaske ansa *CAFETERIA* da manyan harufa kana wuce gudin zaka ga wani babban garden an zagaye shi da flowers ga fruits a kewaye a wurin toh nan ne garden d'in".
      Owk na gode suka yi musabaha da juna daga nan ya cigaba da tafiya yana mai bin kwatancen samarin suka mishi.
      B'angaren su Ash kuwa suna ta jira shiru shiru babu alamun dawowan su tee, da suka gaji da jira Suhail yayi sallama da Ash cuz akwai abunda yake son yi a gida, yana barin wurin Ash zata koma aji kenan sai ga wata mota ta parking a gefen ta da uban gudu kamar mai motan zai buge ta,
     Da sauri ta ja da baya a tsorace tana zazzare ido shi koh bai san dawan garin ba ya bud'e k'ofa da k'arfi ya fito Ash tayi wurin shi tana banbami ta jingina a jikin motan cikin rashin sa'a garin mai da murfin motan ya rufe ya had'a da kayan jikin ta".
      Kiiiiiiii kayan ya yage Allah ya taimake ta ta k'asa ya yage da sauri da kama k'asan rigan da k'arfi tana jaaa yana ganin haka ya bud'e murfin k'ofan da sauri ta ja kayan ta ta fice fuuuuuuuuuu kamar zata tashi sama, ya juyo kenan domin ya bata hak'uri ya ga ta b'ace mishi,,
     Guntun tsaki ya ja yace" yarinyar nan ta cika masifa da yawa, da ta san halin da nake ciki da baza ta min haka ba, da yake ya gano yarinyar da suka tab'a had'uwa da ita ne amma koh kad'an bai ga fuskan ta ba.
    Bayan barin Ash wurin sai ga su tee sun dawo kamar an jefo su, suna tad'i hibb tace" gaskiya tee kin wahalar da ni dayawa dubi k'afata ki ga yanda suka kumbura suke min tsami".
     Tab'e baki tee tayi tace" ai kin me kika ka yi?, du du tafiyar tak'u nawa muka yi da kike cewa kin gaji har da sharri wai sawayen ki sun kumbura kamar wata mata mai ciki".
      "Hmmmm ai dole baza ki ga nisan tafiyar ba tunda masoyin ki kike son gani, ni da ba kowa nawa zan gani ba ai ni sa san nisa da wahalar tafiyar".
      Suna cikin maganar ne tee ta hango motar ya Abdallah shi kuma yana daga ciki, laaaaaa hibb kin ga motar tashi can ashe ya ma gano inda nake nufi, yaya na masoyina kenan na tabbata ya Abdallah mai k'aunata ne".
     "eeehhhhh tee da gaskiyar kamar shi d'in ne", k'are maganar ta yayi dai dai da lokacin da suka iso wurin shi, tee ta bud'e murfin k'ofa tace" laaaaa yaya na ai na zata baza ka gane nan d'in bane, ina cikin maka kwatance wayar ta mutu diffffffff".
     Murmushi k'arfin hali yayi mata yace" ai kuwa gashi kin ganne, ya lek'a waje yana dube dube yace ina sauran mutanen baki ne naga ku biyu kuka zo".
      Sai yanzu ta lura da cewa ba su Ash a wurin ta zaro ido alamar mamai tace" kaiiiiiii ashe ma basa nan kuma fa a nan muka baro su".
      Da k'arfi ya bugi steering motar yace" shiirrrttttt wannan Ash d'in so take ta zauta ni".
     "Me kace? "
  "No babu komai" ya amsa mata a takaice daga nan bai kuma cewa komai ba.
     Ba dan ya so ba haka ya hak'ura yake ta biye ma tee suka taba hira dan koh kad'an baya k'aunar ta san abunda ke bugun shi a zuci".
      Ba wani dad'ewa sosai yayi ba ya mata sallama ya koma gida rai babu dad'i.
     Yana barin wurin suka nufi class suka tarar ana English class, cikin sand'a suka shiga zasu zauna suka jiyo muryar matar tace" get out of my class", a tsawace, sumi sumi suka kamo hanya suka fice y'an ajin suka tuntsire da dariya ganin an embarrassing d'in teehibb, Ash kuwa koh kad'an bata ji dad'in hakan ba, haka suka koma chamber suna jero uban tsaki.

       B'angaren ya Abdallah kuwa haka ya iso gida yana jin zogi a zuciyan shi,,
     a parlor ya tarar da dad da kuma mum d'in tee a zaune suna watching movie yana ganin su ya musu sallama suka amsa ya shigo ya zauna tare da duk'ar da kai k'asa.
      Dad kuwa rage k'arar tvn yayi yana murmushi a fuskan shi yace" kamar ka san muna son yin magana da kai Abdullahi ka shigo a wannan lokacin, koh da yake mum d'in ku ta shaida min cewa ta isar maka da sak'o na.
       Ehhh dad ta fad'a min".
    Toh toh tohhhhh dama akan maganar alalar ka da daughter ne, mun lura kuna son junan ku, mun zuba muku ido muga iya gudun ruwan ku koh zaku tunkare mu da maganar aure muka ji shine muka ce bari mu mu same ku da maganar kar mu biye ta shiriritar taku ta yarinta".
      Tashin hankali matar misaltuwa Abdallah ya shiga, tsaboda tsabar bak'in ciki har tsigar jikin shi na tashi, idanuwan shi suka kad'a suka yi jaaaa, shiru yayi musu ba tare da ya furta komai ba, mum tace" yaya dai kayi shiru koh dai da wata matsala ce Abdallah".
     D'ago da jajaye n idanuwan shi yayi yana kallon su lokaci guda ya hau girgiza kai cikin murya mai rauni yace" a'a dad babu komai ina tunanin irin hallacin da kuka min ne, baku san koh ni wanene ba kuke shirin had'ani aure da y'ar ku amma ina so ku min izini na koma garin mu na shaida ma iyayena",
     "Babu komai kana iya tafiya Allah ya maka albarka na san dai baza ka watsa min kasa a ido na ba"
      "Ameen" ya amsa ya tare mik'ewa tsaye ya soma tafiya yana dafa jikin bango lokaci guda yana sharo hawayen bak'in ciki da suka zubo mishi har ya iso d'aki ya saki kuka mai cin rai yana cewa" me yasa zaku bijiro min da abunda kuka san ba zan iya mutsa muku ba?, me yasa kuke k'ok'arin cusa min Fatima a rayuwa ta bayan ina da murad'in zuciya ta, me yasa duk inda na shiga nake fuskantar tashin hankali ne a rayuwa ta, Allah ka bayyana min Aysha ka d'ora mata sona a zuciyan ta, haka dai ya dinga rusar kuka shi kad'ai a d'akin.
     




*eedatou✍🏻*
       ~Y'ar mutanen Dengi~

WAYE MACUCIWhere stories live. Discover now