🏵🏵☀☀🏵🏵☀☀🏵🏵
*☀WAYE MACUCI☀*
🏵🏵☀☀🏵🏵☀☀🏵🏵
'''Suhaib koh Suhail'''***********************************
® *REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS P.M.L*💭💭💭
_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_
# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
©
'''Marubuciyar Rayuwar Sumayyah'''*eedatou😍*
'''Follow and ✅ote me on Wattpad''': *eedatou*
~Ku min uzuri kun jini shiru munyi hidimar buki ne shi yasa baku ga post d'ina ba, Alhamdulillah mun gama lafiya insha Allah zaku ci gaba da ganin post har zuwa sanda zan tsaya da typing sabods ba lallai na iya gama littafin a y'an kwanakin nan ba, amma isha Allah bai fi na gama bayan sallah da sauti biyu ba dole zan rage wasu abubuwan ciki, da fatan zaku fahimce ni ku bani goyon baya d'ari bisa d'ari.~
5⃣5⃣
Yana fitowa ya hango wasu yara su uku akan kake suna wasan tsere, da yake ba wani rata bane tsakanin su ya kwalla musu k'ira suna jiyo shi suka yi saurin taka burki suka jiyo suna kallon mai k'iran. Suna ganin abban Aysha ne suka tuk'o keken nasu a hankali zuwa gaban shi suna isowa suka sa keken a standard suka sauk'o tare da rusunawa a gaban shi suka gaishe shi.
Maida fuskan shi yayi kan babban cikin su yace Samaila ina zaku haka kuke ta zafga gudu bisa titi bakwa tunanin fad'awa a rami gashi titin namu bai da wani kyau bane da shi?
Wallahi wasan tsere muke abban Aysha, wai fa yaran nan ne suke cewa ban iya kake ba ni koh na ce musu toh mu gwada tsere muga wanda zai zo na d'aya a cikin mu shine fa ka gan mu haka muke ta kwasan gudu".
Abba ya gyara hulan kan shi yace" ikon Allah, toh a dai bi a hankali ban da tuk'in ganganci, ku dinga lura da titi da kyau idan kuna abun hawa sannan kuma ku rage gudu da yawa yana kawo hatsari, duk abunda aka bi a sannu ya fi wanda ake gaggawa shi yasa zaku ga idan aka yi accident da abun hawan da babu gudu sosai akan samu sauk'in raunuka kan wanda aka yi accident da abun hawan da suke ta uban gudu.
Natsawa sosai suka yi suna sauraran shi sai da ya kai aya kana suka had'a baki suka ce" mun gode abban Aysha insha Allah zamu kikyaye".
"Toh shikenan kuna iya tafiya", har sun mik'e sun fara tafiya yace" afff Sama'ila na manta dama aike zan muku, cikin sauri suka juyo da baya nan ya fara musu kwatancen gidajen da za su aiken yana gama fad'a musu suka mishi sallama suka hau keken su wannam karon ba wani gudu sosai suke yi ba, cikin nutsuwa suke tuk'i har suka iso gidan farko a haka a haka har suka gama zaga gidajen kafffff kana suka wuce wasan su.
B'angaren abba kuwa bayan sun yi sallama da yaran ya shige d'akin shi nan ya tarar da su ummi Sumayyah suna magana k'asa k'asa da Alhaji D'ahiru suna ganin shi suka yi saurin yin shiru suna murmushi a tsarge kamar an sa su dole,,
bai ce musu komai ba ya nemi wuri ya zauna suka ci gaba da tattaunawa a tsakanin su.
Jim kad'an sai ga mutanen da ya aiko a yi k'iran su sun zo, suka zauna suma nan abba ya shiga koro musu bayani kamar yanda su Sumayyah suka fad'a mishi tun farkon zuwan su har yanzu bai b'oye musu komai ba.
D'aya daga cikin y'an uwan mahaifiyar Aysha mai suna Habu ne yace" toh malam Sa'eedu ai ba mu da iko a kan aurar da Aysha duk abunda kuka ga ya dace shi kenan ba sai kun neme mu ba y'ar ku ce sai abunda kuka ga saman yi da ita".
Haka ne Habu, na aiko a k'ira ku ne na shaida muku ku san me ke tafiya a matsanin ku na y'an uwan mahaifiyar ta".
K'aramin cikin su mai suna Usman yace" toh malam Allah ya sanya alkhairi babu komai tunda abu ne na gida ba sai an tsaya b'ata lokaci ba.
A gurin aka yanke ma Suhaib sadaki dubu 30 ummi Sumayyah ta ciro dubu d'ari ta dire a gaban su aka saka rana nan da sati biyu, daga nan suka yi sallama kowa ya kama gaban shi.
Tun a mota ummi Sumayyah ta k'ira zee da Suhaib ta shaida musu halin da ake ciki, murna sosai a wurin su kamar su zuba ruwa a k'asa su sha dan murna, Suhaib kuwa k'asa hak'uri yayi suna isowa Jos har sai gashi ya zo gidan suka zauna suna maida zance.
Ummi na kina biya na da yawa, duba ki ga cikin kwanaki k'alilan kin sa bro zai angwance kaiiiii gaskiya kin iya beating brain sosai fa", cewar zee kenan tana magana tana kallon inda Suhaib yake zaune.
Wallahi kam sis i kept wondering wani irin basira ne da ummi, abun kamar almara su dad sun gama sake baki cewa Aysha wani can zata aura bani ba not knowing that she belongs to me and always be, hahahaaaaa let them do woooo i don't give a damn lokaci kawai muke jira .
See you kids da kun d'auka zan nad'e hannu ne na gan ku kun loosing choices d'in ku?, never!!!, ta fad'a da k'arfi kana ta d'ora da cewa" hmmmmm ku bar ni da yaya kawai kafin ya farga daga doguwar baccin da yake sai dai ya samu an d'aura muku aure kai kuma a nan naka salon tak'un zai fara koh da ya nemi takardar saki a wurin ka kar ka kuskura ka bayar, idan ya ja ka ja dole d'ayan ku zai hak'ura kuma na tabbata shine, duk barazanar da zai yi maka muddin ka sa tsoro a zuciyan ka toh dole wasa ya hau kan ka so you get me right?
Yeah mum kin san i'm always stubborn zan playing role d'ina da kyau".
Yeah na yarda da kai d'ari bisa d'ari so mission stated get prepaid".
Mum ta d'ora hannun ta a kan centre table sai Suhaib and lastly zee daga nan suka janye hannayen su, sai da Suhaib ya jima sosai a gidan kana yayi sallama da su ya tafi gida, ya bar su zee suna ci gaba da zantawa a tsakanin su.
Fitan Suhaib ke da wuya zee ta kwanta ajikin mahaifiyar ta tace" see this rascal he taught kina taya shi fighting ne, not knowing that duk abubuwan da kike yi dan ni kike yin su".
"Uhmmmmm rabu da shi kawai, idan muka samu muka hankad'a k'eyan shi ya Aure Aysha ai kin ga dole Suhail ya hak'ura da ita ya aure ki ke kuma sai ki koya mishi yanda zai manta da wata mai suna Aysha ya so ki, ya zamanto ke kad'ai ce a birnin zuciyan shi.
Cike da murna ta dad'e lafewa jikin Sumayyah tace" thanks mum, you are the best mum ever", ta bata peck a hannun ta.
Mention not my last hope farin cikin ki shine nawa oyya let's go and have a lunch cuz da yunwa sosai na dawo a ciki na".
Owk ummi na, haka suka jera zuwa dinning a tare da ka hango su zaka ga
babu damuwan komai a tattare da su suka fad'a dinning suka cika tummy d'in su da abinci.
YOU ARE READING
WAYE MACUCI
Historical FictionLabari ne a kan wata mak'auniyar Allah mai suna Aysha wacce take soyayya da yayan ta amma kwatsam sai wata tsautsayi ya afka mata har hakan ya saka ta cikin bakin ciki,ba tare da ta bayyana mishi ba sai daga baya ya fahimci halin da take ciki a tsan...