*🌟💫SHINNING STAR WRITERS ASSOCIATION🌟💫*
{'''The more we shine bright the more we educate and enlighten our readers.}'''
🏵🏵☀☀🏵🏵☀☀🏵🏵
*☀WAYE MACUCI☀*
🏵🏵☀☀🏵🏵☀☀🏵🏵
'''Suhaib koh Suhail'''***********************************
©
'''Marubuciyar Rayuwar Sumayyah'''*SA'EEDA MUSA DAUDA😍*
'''Follow and ✅ote me on Wattpad''': *SaeedaMusaDauda*
*BESTORED TO MY LIL SIS* ''' SUMAYYAH MUSA DAUDA'''
6⃣7⃣
🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚
Da kyar ya danne Ilu da maganar yace mishi da kan shi zai nemo mishi inda Aysha take. Haka Ilu ya fito yana sharar kwalla, d'akin shi ya shiga ya tarar da Ladiyo matan shi tana sham k'amshi wai ita ala dole ga mai kishi nan, zama yayi a gefen ta ya rik'o hannun ta, malam cika min hannu dallah. " uuummm haba Ladiyo idan ban tab'a ki ba zan zan tab'a, yana maganar yana tab'a hanci irin ta kutare".
" Ba tafiya za ka yi ba malam Allah kana tafiya k'afata k'afarka, muddin na had'a ido da Indon nan sai na b'ala ta.
Haushi ta ba ma Ilu ya ja tsaki, A gaban nawa zaki tab'a Shatu Allah kin taba takardar ki, nan ya hau ta da masifa ta inda yake shiga ba nan yake fita ba.
Zaune yake a parlor bayan ya ci abinci yana sipping fruit salat da Aysha ta had'a mishi, hannun shi rik'e da jarida yana dubawa.
Ash ce ta shigo cikin dinkin atamfa riga da shirt wanda ya bala'in kamata sai zuba k'amshi take, ba k'aramin kyau kwalliyar ta yayi ba, ta fito ta yauk'i.
K'amshin turaren ta ne yayi maraba a hancin Suhail, d'agowa yayi ya kalle ta ciki da begen ta. Bai san sanda ya waro hannu ta taho da gudu ta shege jikin shi, mai da hannun yayi ya rufe yana shinshinar ta, "baby na kin yi kyau, alamar babyna na jikin ki na dad'a fiddo miki da tsantsar kyaun ki.
Murmushi ta mishi cikin jin dad'in yaba kwalliyar ta, cikin shagwab'a tace"durling me yaushe za mu je gidan su mum mu gaishe su, ni fa missing mum d'ina nake yi".
" Kamo hannun ta yayi cike da sha'awa ya bata peck, nine ba'a missing d'ina ko, har so ma kike ki tafi ki barni".
"Kanne idon ta d'aya tace" why will i, you a my part ka ga idan ba ka tare da ni i'm totally incompletely.
Zagaye hannun shi yayi a k'ugun ta yana shafa tommy d'in ta, baby yaushe zaki juye min ajiyar ta ne ki sake d'auk'ar wata lodi?
"Baka tausayi na habibi, yaushe na gama da wannan ka ga gani fa kalar wahalar da na sha kwanakin bayan nan", ta fad'a a marairaice fuska.Gidan Suhaib kuwa Zee ce a d'aki tana charts tana dariya da alama abinda take ya d'auke mata kewa, dawowan Suhaib daga wurin aiki ya ga babu ita a parlour, ya duba kitchen bai ganta ba ya haye sama room d'in ta nan ya tarar da ita sai shek'a dariyar ta take yi. Kallon ta ya tsaya yi har yana gyara tsawuya ya ga tamk'ar sauya mishi ita akayi, tun da yake bai tab'a sanin Zee na da kyau kamar haka ba, "laughing beauty", ya fad'a a k'asan zuciyan shi, har ya shigo ya zauna bata sani ba sai ji tayi mutum ya rungume ta, juyowa tayi tana ganin shi ta ajiye wayar a gefe tare da d'ora kan ta saman k'irjin shi ta kwanta lamo a jikin shi, tana cewa " welcome husby".
" Thank dear".
"Yaushe ka shigo d'akin ban sani ba?
Ina za ki sani bayan kina ta chatting kin manta da time d'in dawowan mijin ki yayi, wa ya baki dariya ne haka?
" Uuhhmm "Husby wallahi Ash ce ke ta bani dariya tun d'azu, mun karb'a d'inkin ashoben Hibb da Tee me fa shine ta gwada wai yayi mata kad'an, ka san cikin ta ya k'ara mata k'ib'a kad'an.
" Shine kike mata dariya to, ba sai ku je a bud'e mata ta yanda zai shiga jikin ta ba.
" ai dole nayi dariya har video ya Suhaib ya min tana kuka, Ash da rigima take wallahi".
"Dariya yayi shima kana yace" ki dai a hankali y'anmata na, ba'a dariyar mota gawa".
"Me kake nufi?, ta fad'a cikin hararar wasa.
A kunne yayi mata rad'a yace" mu je ki shirya Ni, ki cika min ciki da abinci sauran maganar zamu k'arasa a master room", mik'ewa suka yi suka fice daga d'akin zuwa nashi.Kwanci tashi babu wuya a wurin Allah, lokaci na dad'a matsowa cikin ikon Allah yau aka tashi da events na bukin su Tee da Hibb, an d'aura aure cikin amminci aka kai amare gidajen su, Tee aka kai ta gidan mijin ta da ke unguwar su Suhaib yayin da Hibb kuma a Abuja za ta zauna, tuni mijin ta ya processing karatun ta ya koma can d'in. Ba k'aramin kuka k'awayen su uku suka yi ba, ance aure mai nisanta mutum da gida, babu yanda suka iya haka suka lallashe junan su, suka ci gaba da zumunci da Hibb a waya.
Bayan wata takwas Ash ta tsungumo tsantaleliyar baby girl mai kama da uban ta, farin ciki a wurin bayin Allah nan ba'a magana, duk wanda ya ga babyn sai ya yaba da kyaun da Allah yayi mata.
Bayan sati d'aya aka rad'a mata suna aka saka mata suna Sa'eeda amma ana k'iran ta da amra".
Ama ta taso cikin kulawa ta ko wani b'angare, duk gidan da ta je sai an yi marmarin ta k'ara zuwa musu.
Shekarar Amra d'aya a duniya Ash ta sake d'aukan ciki, a lokacin ne Zee ta haihu d'a namiji shima aka saka mishi suna Abubakar, ana k'iran shi da Assiddiq. Hibb ma su samu labarin itama tana d'auke da nata cikin haihuwa kawai take jira ya kawo ta gida, Tee kam bata samu ciki da wuri ba, dan ita sati biyu ne nata cikin.
Lokaci zuwa lokaci Ash na zuwa makarantar nakasassu tana yi musu kyaututtukan na musamman, tare da ga su gudumawwan duk abinda makarantar ta nemi taimakon inganta rayuwar yaran makarantar.
Wanda ya ba ma Suhaib giya ya sha sun samu labarin an harbe shi ya mutu a wurin bathday bati na wata budurwar shi Titi a sakamakon snatching d'in budurwa da yayi ma wani tantirin yaro.
A lokacin ne duka family d'in suka saka ranar tafiya Dengi su duka, Allah cikin ikon shi ranar Litinin suka d'auki hanyar Dengi su duka cike da tarin tsarabar su.*Dengi*
Inna Larai ce yau ta tashi ta hauka tana zaga gida ita kad'ai tana kuka, Abban Aysha da fitowan shi kenan daga band'aki ya gan ta, girgiza kai yayi cike da takaici ya shige d'akin amaryar shi mai suna inna Mari.
Sallamar mutane ya ji, kamar Muryar da ya sani ya fito ya lek'a" a'a maraba da mutanen Jos, yana washe baki, inna Mari ma ta fito saboda jin sun yi baki.
" Babban taburma ta d'auko ta shunfud'a musu, ta d'ebl ruwa a robar juk ta dire musu tare abinci.
Gaishe da dad tayi da su daddyn Tee kana suka fara gaisawa da mum, mommyn Tee da ummi Sumayyah dan tuni suka yafi juna, daga nan yaran suka gaishe ta suma, Ash kam na yaba hankalin inna Mari ta na jiye ma mahaifin ta dacen mace ta gari da yayi.
Kuka suka jiyo daga gefe kan su ankara sai ji suka yi wacce take yi ta zube a gaban su tana kuka tana neman yafiyar Ash, domin kuwa bata tab'a manta fuskan ta.
"Ina Larai ke ce kika koma haka? '''Innalillahiwa'inna ilaihiraji'un''' Allah yayi gaskiya da yace" duk wanda ya cuce wani zai saka mishi", yau ga sakayar abinda tayi mata tana girb'ewa.
" Kan kace me ita mata kama kuka, tunanin ya Abdallah ya dawo musu sabo ita da Tee, mutane suka hau lallashin su. Da kyar suka daina daga nan Ash tace ta yafe ma inna Larai, daddy tace idan za su koma da ita za'a tafi yayi mata jinya a can.
Kwana d'aya suka yi suka yi sallama da su Abban Aysha, ya raka su waje.
Su bud'e motocin su za su shige sai ga Ilu yana d'angana k'afa ciki lastest takalmin shi ta bi-shanu a dole wai ya ji labarin dawowan Ash yana gudu ya tare ta.
" Tsaya!!! Ina za ku tafi min da Shatu na?
"Tsayawa suka yi suna bin shi da kallo.
" Yana isowa yayi wurin Ashe yana murmushin farin cikin ganin ta, Shatu indodo, Shatu na, ashe rai kan ga rai?, yana dad'a washe baki.
" Wai kai Ilu yaushe za ka yi hankali ne ka gane ni Aysha ba taka bace, haba ta k'are maganar cikin fusata.
"Haba Shatu ni masoyin ki kike ma haka? Ko dai zuga ki aka yi,yana yunkurin kamo hannun ta Suhail ya buge nashi yace". Kai mahaukaci ina ne za ka tab'a matar aure, Allah ka yi yunkurin tab'a ta sai na saka an kulle min kai.
" Kai malam ina ruwan ka da soyayyar mu, da ma can tawa ce an raba mu aka yi, yarinya ya gani a hannun Zee yace" kam bala'i wannan yarinyar fa, Zee tace ta Shatu ce.
Tabbbb Allah Shatu na fasa aradu sai dai ko mutuwa za ki yi da kauna ta ki mutu na koma baturiya kawai,,
Kallon Suhaib da Suhail yayi yace" ku yi ma Allah da Annabi, bana manta fuskan ku cikin ku na san akwai mijin Shatu, ku aura min baturiya a ta biyu na k'ara.
Dariya ya ba ma su gaba ki d'aya sai da suka dara dad yace" Wai ka fasa Shatun ne Ilu?
Ina tsammmm ban san ta ba aradu ni baturiya nake so suka kuma kyal-kyale da dariya su duka har suna hawaye.*eedatou*
Tamatbihamdulillah, Allah na gode da ka bani ikon sauk'e littafina mai suna *Waye Macuci* Allah ka bamu ikon amfana da tarin darusan da ke cikin littafin, ka hane mu aikata cuta ga bayin ka nakasassu, ka saka mu fi karfin zuciyan, Ameenn ya Allah, mu had'u a littafina wanda yanzu haka nake yin mai Suna *MAGANIN MATA* '''Damuwa''' bissalam
YOU ARE READING
WAYE MACUCI
Historical FictionLabari ne a kan wata mak'auniyar Allah mai suna Aysha wacce take soyayya da yayan ta amma kwatsam sai wata tsautsayi ya afka mata har hakan ya saka ta cikin bakin ciki,ba tare da ta bayyana mishi ba sai daga baya ya fahimci halin da take ciki a tsan...