🏵🏵☀☀🏵🏵☀☀🏵🏵
*☀WAYE MACUCI☀*
🏵🏵☀☀🏵🏵☀☀🏵🏵
'''Suhaib koh Suhail'''***********************************
® *REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS P.M.L*💭💭💭
_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_
# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
©
'''Marubuciyar Rayuwar Sumayyah'''*SA'EEDA MUSA DAUDA😍*
'''Follow and ✅ote me on Wattpad''': *SaeedaMusaDauda*
*BESTORED TO MY LIL SIS* ''' SUMAYYAH MUSA DAUDA'''2⃣6⃣
Sosai karuwan suke ta aikin gudu koh waccen su neman mafaka take yi Aysha kam ban da k'arar sawayen mutane da kuma sarin d'in sojojin babu abunda take ji.
tsabar kan ta ya kulle ta ma rasa inda zata sa ranta ta ji dad'i, zama dirshan tayi a k'asa hawaye na ambali a fuskan ta yayin da wutan tsanan *macucin* da ya jefa ta a cikin had'ari ke dad'a huruwa a zuciyan ta.
tana ji babu yanda ta iya haka sojojin nan suka k'araso wurin da take d'aya daga cikin su ya dak'a mata tsawa yace" ke taso muje tun kafin mu harba bindigan nan ta tarwatsa miki kai".
jin maganar sojan yasa cikin ta ya d'au rawa ga kuma uban tsoro da ya gama kama ta, cikin rawar jiki tana magana voice d'in ta na cracking tace" dan Allah kuyi min rai wallahi tsautsyi ne ya kawo ni wurin nan, ni makauniya ce wallahi yayana kuma macuci ne ya kawo ni".
"keeeeeee shut up rufa mana baki ina makantar taki a nan baki ji tsoron Allah ba kika taho nan kika baro iyayen ki kika taho yawon duniya, duniya ce ta ishe ki riga da wando dan dubun ki sun yi sun bar ta balle ke tatsitsiya da ke.
d'ayan ya k'ece da dariya yace" gaya mata dai taji da kyau ita duniya tamk'ar kasuwa ce kana gama cin ta zaka koma ka bar ta either ka aikata alkhairi koh sharri. "
ogan su daga cikin mota ya daka musu tsawa yace" hurry up ku fa muke jira oya sa mata ankwa a hannu mu tafi kamo sauran y'an uwan sana'an ta tin kafin su tsere,,
jiki na kyarma suka bi umurnin ogan nasu suka sa ma Aysha ankwa a hannun ta suka tusa k'eyan ta zuwa bayan mota, haka suka yi ta kamo sauran karuwan duk wanda suka yi yunk'urin tserewa bullet suke harba musu a k'afa su kame su da haka da haka har suka kame mutane sama da 30 suka tada motar su suka yi gaba.
suna k'aryo kwana sai ga motar Suhail ya shawo kwana da uban gudu ya nufi cikin lodge d'in, clashing motar Suhail da na sojojin yayi a daidai kan kwana ba tare da Suhaib ya kawo tunanin komai a ran shi ba kai tsaye ya danna hancin motar shi cikin lodge d'in, yana shiga yaji wurin shiru babu alamar motsin kowa, ba tare da ya damu da jin shirun ba ya fito daga motar shi ya hau kwad'a ihu yana k'iran sunan Aysha da k'arfi yana kewaye farfajiyar lodge d'in,,
mutumin nan da Suhaib ya bar Aysha a wurin shi yayi mata register a harkar karuwan ci shi da kuma sauran da suka b'oye a wurin suna hangen Suhail a wurin yayin da jikin su ke rawar d'ari d'ari dan dama lab'ewa suka yi a jikin motocin da suke parke a wuri guda, saboda bishiyoyi sun kewaye gaba ki d'aya motocin yasa sojojin basu gan su ba da kuma sauran abokan huld'ar shi sakamakon duhun da wurin yayi, amma kafff suna ganin duk abubuwan da ke faruwa game da b'arnan da sojojin suka yi musu na kamen mata karuwai abokanan huld'ar su,,
jin k'arar tafiyan sojojin da kuma muryar Suhaib yasa suka fito da sauri jikin su na b'ari dan tsoro dan su kan su shaida ne muddin aka kamo su sai na lahira sun fisu jin dad'i, bama wannan kad'ai ba sunan su zai b'aci a idon duniya most especially masu yi ciki sirri .
Suhaib bai ma san da mutune a wurin ba sai ji yayi mutumin yace" yallab'oi how may i help you ?, akwai y'an mata of different sizes a nan duk wacce ta maka ka biya kud'in ta each day da zaka spending night da su 10k ne kud'in sy dan haka gasu nan a gaban ka ka zab'a ka darje".
wani irin haushi da takaici ne ya rufe Suhail ji yake kamar ya rufe mutumin da duka tsabar haushi but sai ya danne abun cuz babban burin shi yayi ido hud'u da Aysha tun kafin wani mugun ya afka mata tun da ba wani makami take da shi da ba zata iya k'are kan ta ba.
bai k'ara cika da bak'in ciki ba sai da sauran karuwan da suka tsere suka fito gantsar gantsar da su kamar sabulun k'ato a tub'e ganin Suhail yasa wasun su ke ta botsaro k'irji su ta tsigar jan hankali yayin da sauran ke ta jujjuya mazaunai abun haushi koh kad'an bayyana tsiraicin su bai dame su ba they are willing to have costumer da zasu ja ra'ayin shi har ya k'auce hanya su shek'e ayar su,,
tsigar jikin Suhaib ne ya tashi yarrrrrr dan duk d'a namjin da ya shiga tarkon y'an duma duman nan toh idan bai yi da gaske ba zasu kai shi su baro shi,,
da sauri ya kulle eyes d'in shi gammmmm yana maimata k'almar ''' Inalillahi wa inna ilaihi raji'un, Allahumma ajirni fi musibati wa aklifli khairan minha"''', a zuciyan shi yayin da y'an matan suka ruhu mishi a kai c'aaaaa suka kai hannu suna shafa tsatsan jikin shi cikin kissa,,
Da yake addu'a makamin mumini ne shaid'an bai yi wani tasiri a kan shi ba a fusace ya ture su daga jikin shi tare da daka musu uwar tsawa yace" ku matsa daga jikina koh na fisge suman kan ku dukan ku ku mutu,,
ban da tsautsayi ma kun isa ku had'a najasar jikin ku da nawa, mind you i'm not your type and kuma ban ga abun d'auka a jikin ku ba mttssww, ya juyo kan mutumin yace" heeee you a soud of warning giving to you kar ka kuma had'a ni da tantiran tsoffin bariki irin ka wanda banda tsinuwa da kuma zunuban Allah da suke d'aukawa babu komai,,
pleading d'in shi mutumin ya hau yi dan sai yanzu ya gano cewa mutumin da ya kawo mishi yarinya d'azu ne, lokaci guda zufa ya fara yanko mishi dan a gaban idon shi aka tafi da Aysha.
da yake a tsorace yake yasa tun kafin Suhail ya tambaye shi yayi saurin cewa" sorry sir an samo matsala fa yarinyar da ka taho da ita sojoji sun kame ta nima nan da ka gani da kyar nasha dan Allah ne ya kwace ni".
what ? an kame ta fa kace" ya '''Ilahi''' wannan wacce irin musfifa ce ta afko mana ??, Suhail ya fad'a a fili dan ya gane cewa mutumin taught it was Suhaib.
a take tunanin sanda yayi clashing da sojojin ya fad'o mishi a rai hankali a tashe ya bud'e motar shi da k'arfi ya fisga ya bar lodge d'in ya bi bayan y'an sandan da mugun gudu amma ina koh k'eyar su bai samo ba hakan yasa ba shiri yayi you turn zuwa gida domin ya sanar ma mum halin da ake ciki.
B'angaren mum kuwa bayan barin Suhail gidan da kyar ta samu ta daina kukan, abunda idan ta tuna ke bak'an ta mata rai shine ta yaya Suhaib zai kai Aysha gidan karuwai bayan da mutuncin ta da kuma gatan ta a garin ?, tsabar kukan da taci har idanuwan ta sun canja launi sun yi jajazur da su amma Suhaib kam koh a jikin shi, farko dai ya fara jin tausayin yarinyar but da yaga yanda d'an uwan nashi ya d'aga hankalin shi akan yarinyar sai yaji wani irin haushin ta ya turnuk'e shi har ma a ran shi yana jin dad'in abun da ya aikata,,
haka dai suka yi jigummm a parlourn kowa da abunda ke sakawa a ran shi time to time kuma phone d'in mum na ringing tana avoiding d'in k'iran cuz k'arar wayan ba k'aramin d'aga mata hakali yake yi ba dan ta san dad ne ke k'ira cuz yana son yayi magana da Aysha kamar yanda ya fad'a that" he will call later.
k'arar bud'e k'ofa suka jiyo da saurin suka maida fuskokin su kan k'ofan suna kallo, Suhail ne ya shigo hankali a tashe ya tunkaro wurin da mum take, tun kafin ya k'arasa isowa ta nufo shi saboda hakalin ta ya gama tashi over and ta k'osa ta ji halin da ake ciki, hankali a tashi ta hau jero mishi tambayoyi tace" where is she son ?, ka same ta kuwa ? a wani condition take ciki yanzu?, duk wannan tambayoyin tayi shi ne out of her senses gefe guda kuma sautin beating d'in numfashi ta ne ke fita da k'arfi fatt fattt fatttttt.
Duk da dai shima yana cikin tsananin rud'ewa amma bai hana shi calming d'in kan shi down ba kana da murya ta mai kama da wanda yake cikin tashin hankali yace" relax mum na gano inda take but like seriously kwato ta will be a kind of hard to us cuz yanzu tana wurin hukuma and you know dad wasn't aware of all those things".
A tsorace mum ta zaro eyes ta dafe chest d'in ta da k'arfi tace" what hukuma fa kace shi kenan na banu he have killed me, i'm scared kar dad d'in ku yaji labarin nan cuz i'm going to die, ta kare maganar tare da d'ora hannun ta a ka lokaci guda tana facing Suhaib tace" wayyo ni Maryam yau yaya zan yi da mijina a gidan nan, ka kyauta kwarai da gaske da yau ka nuna min cewa ban isa da kai ba na maka aike and you took her some where else .
Suhaib ma k'iris ya rage ya fashe da kuka dan tsabar haushi saboda yanda gana y'an matan nan d'azu ran shi ya b'aci matuk'a da halin d'an uwan shi, duk mai hankali ba zai so ya ga y'ar uwar shi a mummunan wuri irin wannan ba talkless of shi da kan shi ya kai ta, what's a shameful thing is this chaiiii, yayin da a heart d'in shi yana imajini yanda bros d'in shi ke shirin jefa Aysha cikin kazantacciyar layuwa kenan so yake ta koma tamk'ar matan nan da ya gani a lodge d'azu nasu rayuwar dabbobi sai inda suka kai kan su kenan ?, idan ma ya fake da cewa ita y'ar zina ce fatan shiriya ya kamata yayi mata ba ya kai ta inda za'a tarwatsa rayuwar ta ba .
Haka dai suka yi ta tunanin yanda zasu kwato Aysha daga hannun sojojin nan su biyun ba tare da sanin dad ba gashi kuma ya matsa da k'iran wayan mum babu gaggautawa and rasa mai picking cikin su shi kuma bai fasa k'iran ba.***********************************
B'angaren dad ma hankalin shi a matuk'ar tashe yake dan tun da yake barin gida hakan bai tab'a faruwa da shi ba hakan yasa yayi ta k'iran wayan mum ya tabbatar da lafiyar su but abunda ya bashi mamaki da kuma tsoro lokaci guda shine almost 50 missed calls ya mata but no responds yaji kamar ya bi flight ya koma gida dan ya ji lafiyar su but dole dai sai yayi kwana biyun nan dai,,
haka dai ya hak'ura ya zauna a hotel d'in da ya kama rai babu dad'i, da ya gaji da tunani ya kamo tashar FM Jos dan ya d'ebe mishi kewa kun san dad gwanin jin news ne,,
a cikin labaran ne aka nuno wata mata ta kashe mijin ta sakamakon kishiya da yayi mata sojoji suka tusa k'eyan ta cikin motar su, bayan an gama labaran ne aka nuno y'an mata sun fi 30 an sa musu chain a hannu da k'afafuwan su nan hukumomin yad'a labarai saka yi baya ni kan cewa" sojoji ne suka shiga gidajen karuwai da ke garin Jos yin operations Allah ya basu sa'a suka kame kad'an daga ciki,,
sosai labarin ya tab'a zuciyan dad a take ya fara ganin sakacin iyayen na su da suka yi silan jefa y'ay'an su a hanyar halaka,,
yana k'ok'arin kashe TVn ne yaga an nuno wata yarinya da y'ar sandar ta a hannu hawaye na ambali a fuskan ta, sosai yaji gaban shi na fad'uwa ya kai hannu zai kashe kenan aka zooming face d'in yarinyar me zai gani ? fuskar Aysha ce b'arob'aro a jikin talabijin d'in tana fidda hawaye ga majina shab'e shab'e a fuskan ta,,
wani irin shock da jiri ne suka bala'in kama shi da kyar ya iya rage k'arar TVn ya d'au waya yana calling numbern d'in mum da zuwa yanzu suma suna gaban Tv suna kallon duk abubuwan da yake faruwa, ringing d'aya, biyu ta d'auka murya na hard'ewa.Please share
*Sa'eeda✍🏻*
~Y'ar mutanen Dengi~
YOU ARE READING
WAYE MACUCI
Historical FictionLabari ne a kan wata mak'auniyar Allah mai suna Aysha wacce take soyayya da yayan ta amma kwatsam sai wata tsautsayi ya afka mata har hakan ya saka ta cikin bakin ciki,ba tare da ta bayyana mishi ba sai daga baya ya fahimci halin da take ciki a tsan...