Page 30

802 54 5
                                    

🏵🏵☀☀🏵🏵☀☀🏵🏵
          *☀WAYE MACUCI☀*         
🏵🏵☀☀🏵🏵☀☀🏵🏵
        '''Suhaib koh Suhail'''

***********************************

® *REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS P.M.L*💭💭💭

_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_

# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
      
          
                       ©
'''Marubuciyar Rayuwar Sumayyah'''

    *SA'EEDA MUSA DAUDA😍*

'''Follow and ✅ote me on Wattpad''': *SaeedaMusaDauda*


*BESTORED TO MY LIL SIS* ''' SUMAYYAH MUSA DAUDA'''


                       3⃣0⃣

Around 4:30 ya samu daman isowa asubitin saboda go slow da ya rik'e shi a hanya da kuma saye sayen kayan motsa baki da ya tsaya ya saya a hanya, yana isowa harabar asubitin ya dai daita parking motar shi a inda aka tanadar ma motoci,,
     fitowa yayi ya d'auko laidan kulan abinci a right hand d'in shi kana ya d'auko sauran laidodin da d'aya hannun ya ma motar key kana ya fara taku a hankali cike da jan class har zuwa d'akin da Aysha take.
     Sallama yayi daga waje time d'in Aysha na kan sallaya ta idar da salla kenan, mum daga ciki ta jiyo muryar shi ta amsa mishi sannan ya bud'e ya shigo a natse yake tafiya mum ta zubo mishi ido ita kad'ai ta san abubuwan da take tunani a zuciyan ta har ya shigo ya janyo wata plastic chair da ke opposite da mum ya zauna tare da dire tarkacen laidodin da ke hannun shi ba tare da ta sani ba,, 
     "mum" taji ya fad'a da k'arfi, abunda kenan ya dawo da ita hayyacin ta tace"uuummm son are back ? ", ta fad'a tare da d'auke idanuwan ta daga gare shi ta sauke kan laidodin da yazo da su".  
     dogon numfashi ya sauk'e kana yace" yeah mum traffic ya tsaida ni a hanya da i coudn't stay long dan kin ga kuwa yanda aka had'a go slow a hanya ?  like Buhari is gonna give us a visit ".
    Guntun smile mum tayi tace" you are two funny dear kawai d'an go slow d'in da aka had'a kake wani magana I know ba wani na azo a gani bane".
    "Hmmmm mum you will not understand", ya fad'a yayin da yake turb'une fuska.
    "And will never", k'arar bud'e k'ofa suka jiyo Aysha ce ta doctor ne ya shigo da murmushi a fuskan shi suka shaking hands da Suhaib yace" a'a mutuniya har ka dawo ne i taught sai gobe ka dawo koh da yake a yanda kake ta rawar k'afan nan na san baza ka iya barci ba matuk'ar baka duba lafiyan madam ba".
     Madam su duka ukun suka maimaita k'almar a zuciyan su ba kamar Aysha da take ta maimaita k'almar dan ta bala'in d'aure mata kai,,
     Suhaib ne ya k'ak'alo murmushin yake yana washe baki yace" ahh haba dai daga dubiya kuma sai ka min sharri ? toh shikenan daga yau baza ka kuma gani na ba tunda ka ce haka kar kazo kana cewa d'ankwali ya ja hula dan ni bana yarda da wannan a wuri na d'ankwali baya tab'a jan hula", cuz tsaffff ya gane meaning d'in doctor Munir wato a tunanin shi Aysha matar shi ce shi kuma Suhaib ya biye mishi ne dan ya rufa mata asiri dan kar ya zarge wani abu.
    Rage tsawo doctor yayi ya gaida mum kana ya dubi Aysha da zuwa yanzu ta taso daga kan sallaya tana k'ok'arin linke sallaya yana magana yana facing d'in ta yace" toh sha kurumin ka d'an uwa madam kam insha Allah kwana sai gida dan naga yanayin jikin ta akwai kyau da wuya ku kai four days a nan any ways bari na fice i have a lot of work to do in the office see you next".
    "Owk babu case" Suhail ya fad'a tare da mik'ewa tsaye ya raka doctor bakin k'ofa kana ya koma cikin d'akin.

          *lna labarin mutanen Dengi su ya Abdallah da Ilu ?*   

      Tun lokacin da Inna taci kyawawan rankwashi a wurin Ilu wasan tsere suka shiga yi dan koh a hanya ta gan shi sai ta canja hanya,,
     Idan kuwa ya shigo neman ta a gida mak'ewa a d'akin ta take yi bata tab'a yarda ta fito a cewan ta bata ga banun ba nanun baza ta ganta ba lol 😂.
     Shi kuwa Ilu koh kad'an baya gajiya da bibiyan inna take dan tun lokacin da yaga kud'in shi ya b'ace a aljihun shi ya d'ora zargin shi kan inna kun san kuturu da musu da naci akan abu.
    Yau ma kamar kullum inna na tafe a kan hanya tana doka uban masifa ita kad'ai tana tafiya saboda uban rana da ya doke ta a hanya gashi wacce zata k'arb'a bashin kud'i a wurin ta jari ya k'arye mata, haka dai ta dinga masifa har ta biya ta k'ofar gidan su Ilu bata sani ba.
      Tana shawo kan kwana Ilu daga nesa ya hango ta dan mugunta har da dak'a tsallen murna dama da wani d'an hannun shi suke zaune,,
    magana yayi mishi kan ya samo mai gwafa da yake samarin unguwan rab'an Ilu suke yi su more aziki shiyasa a duk sanda ya sanya d'aya daga cikin su yin abu da rawar jini zaku ga ya taso ya yi, hakan kuwa ya faru da yaron dan kafin Ilu ya rufe bakin shi tuni ya taso da rawar jini ya sama ma Ilu aiken shi,,
     Ilu da yake ya lakanci mugun ta da dabaru iri iri da kan shi ya saita mazaunan inna ya harba gwafan tasssssss a kan d'uwawun Inna,,
     wata uwar tsalle ina da dak'a ta rik'e mazaunan ta tana Ilu tana karanto addu'o'in da tun tana y'an mata ta koyo a rud'e tana kuma zazzaro ido, a zaton ta koh Aljanu ne,,
     sai da ta waiwaya bayan ta taga babu mai kallon ta kana ta fara d'aga k'afa da kyar tana matso hawayen azaba tana tafiya,,
    habawa Ilu ya da shek'e da dariyar k'eta yace" shegen kaya ta ji baiwan da Allah ya ma kuturu ta rud'e hahahaaaa hannun kuturu zafi gare shi zaki san kin saci kud'in Ilu angon Shatu Indodo dan kuwa baya yafiya kud'in cijo gare shi".
    da kyau oga aikin ka na kyau ka min dai dai dan wanan mata da jaraba take kamar tsohuwar Allah kwan kwan hahahaaaa suka tafa da Ilu har k'ara ya sake saboda yanda dungun hannun Ilu ya doki kashin hannun shi yace"washhhhh oga gobara a hanuna".
    Kwal kwal kwaaal Ilu ya kuma sakin dariya yace" shegen kaya kai ma ka ji maza kenan ? "
    Ba tare da ya kuma bi ta kan shi ba ya kuma saita d'uwawun inna wanna k'aron da k'arfi ya sake ji kake taasssssssssss dan har sai da dutsen ya yaga zanin Inna,,
     A rud'e ta rik'e wurin ta hau sallen azaba tana gudu zani na fad'uwa haka ta ruga Allah y taimake ta da fatari a jikin ta da kuwa an yi abun kunya a gaban suruki Ilu🤭🤭🤭, shi kuwa tsabar dariya fad'uwa har k'asa yayi har ta b'ace mai da gani ba tare da ya daina dariyar ba.
     Saboda gudun abun kunya kar malam su ji abunda ya faru da ita ta ja baki ta tsuke, haka ta ja jiki da kyar ta had'a tafashashen ruwan zafi tana ta samo yashin ta ta zuba a wani light head tie tana tsoma d'ankwalin a ruwan zafin tana dannawa a mazaunan ta tare dad'e tsine ma aljanun,,
   Idan ta danna ya mata zafi sai ta saki y'ar k'ara tace" Ashhhhh wayyo wayyo",  da k'arfi sai kuma tayi saurin toshe bakin ta da wani tsumman zanin ta.
    Kafin ta gama sai ga idanuwan ta sun zazzago sun kad'a sun yi jazur da su ga hawaye shab'e shab'e a fuskan ta da kyar ta iya runtsawa ranar dan tsabar wahala ma kwanciyan rufff da ciki ta yi.

    B'angaren ya Abdallah kuwa abubuwa sai dad'a gaba suke yi ba dare ba rana kuka ne k'ad'ai aikin shi,,
    a y'an kwanakin gabaki d'aya ya tsafge ya rame kamar ba ya Abdllan da na sani ba,,
     some times idan yana abu kamar mahaukaci yake komowa dan ya kama maganganu irin ta marasa hankali kenan,,
    addu'a sosai abba ya dage da shi inna kuwa sai dai tayi kuka ta share hawayen ta gefe guda kuma tsinuwa take ma Aysha a zuciyan ta bila adadi a cewan ta duk ita ce ta jawo mata halin da d'an ta yake ciki.
    Yau da abun duniya suka taru suka mishi yawa kasa jurewa yayi ya had'a kayan shi cikin dare ya bar garin tare da dire ma malam takarda a gindin filo a d'akin shi dan bai jin a ran shi zai jure zama a gidan ba tare da Aysha ba,,
    a duk lokacin da ya kalle k'ofan d'akin ta yana tunawa da ita hakan kuma na tama mishi mik'in da ke zuciyan shi,,
     koh waiwayen inna bai tsaya yayi ba ya fice  daga gidan hannun shi rik'e da jakan shi  yayin da ambaliyan hawaye ke kwaranya a face d'in shi.



Please share

*Sa'eeda✍🏻*
     ~Y'ar mutnen Dengi~

WAYE MACUCIWhere stories live. Discover now