Page 59

608 34 0
                                    

🏵🏵☀☀🏵🏵☀☀🏵🏵
          *☀WAYE MACUCI☀*         
🏵🏵☀☀🏵🏵☀☀🏵🏵
        '''Suhaib koh Suhail'''

***********************************

® *REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS P.M.L*💭💭💭

_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_

# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
      
          
                       ©
'''Marubuciyar Rayuwar Sumayyah'''

                   *eedatou😍*

'''Follow and ✅ote me on Wattpad''': *eedatou*    

                            5⃣9⃣

    
Hakan ya fad'ar da gaban mutanen da ke wurin ciki kuwa har da mum, ummi Sumayyah da kuma zee da basu san halin da ake ciki ba suka ma juna signal da ido lokaci guda suka saki killer smile musamman tee da take jin wani dad'i ya ratsa ta har ta k'asa boye farin cikin da take ciki sai da mahaifiyar ta wato ummi Sumayyah ta ankarar da ita ta hanyar mata nuni da mutanen da ke wurin kana ta daidaita nutsuwar ta ta marairaice fuska ta shigo layin mutanen da suka rik'o Aysha.
      Ashe duk abunda suke yi abba na kallon su, murmushi mai ciwo yayi ya tunkare inda Aysha take tare da tsugunnawa gaban d'iyar shi ya riko hannun ta ya ja ta zuwa d'akin shi yace" Aysha na fiki jin ciwo a duk sanda wata matsala ta iske ki, na kan rasa sukuni a duk lokacin da na hango hawaye a kwayan cikin idon ki, a matsayi na na abban ki nayi miki zab'i da wanda na san koh bayan raina ba zai musguna miki ba, abu d'aya nake so ki min shine ki kasance mai biyayya a gare ni, matuk'ar kin yi haka a gare ni nayi miki alkhawarin cewa zaki samu ingantacciyar rayuwa.
     Yana gama fad'a ya k'ure ta da kallo yayin da tausayin ta ya gama ratsa mishi zuciya. Hawaye ne ya fara zarya a fuskan ta, bata san sanda ta fashe da kuka ba ta fad'a jikin abban ta ta fashe da matsananciyar kuka tana cewa" Nayi alkawari yi maka biyayya abba na koh da zan rasa farin ciki a rayuwa ta ne, zan kasance mai biyayya a zab'in da kayi min, a shirye nake da na k'arb'i zab'in k........, k'asa k'arasa maganar tayi saboda kukan da yaci k'arfin ta,  yana ganin hakan ya hugging d'in ta tide tare da zagaye hannun shi yana bubbuga bayan ta a hankali alamar lallashi sai da ta tsagaita kukan ya raba ta da jikin shi tare da sharo mata hawayen fuskan ta ya rik'o ta suka fito waje.
        Bayan barin su wurin ne dad da daddyn tee suka komo gefe nan daddyn tee ya fad'a ma dad abunda ke tsakanin tee da ya Abdallah da kuma kuddurin su na zuwa Dengi tare da rok'on alfarmar kar ya sake tee ta san abunda ya faru da ya Abdallah da soyayyar Aysha ya jefa shi a halin da yake ciki, bayan sun gama maganar ne suna k'ok'arin barin wurin suka yi kicib'is da tee a gaban su ta sark'e hannayen ta, fuskanta kuwa hawaye ne ke kwaranya, dad d'in ta na ganin haka ya ji wata iri matsananciyar fad'uwar gaba ta kama shi, bisa dukkan alamu tee ta ji kafffff abubuwan da yake fad'a ma dad, cakkkkkk ya tsaya yana kallon ta for some minutes kafin nan ya d'aga k'afa da kyar zai yi wuri ta,cikin muryar kuka tace" it that want you were hidding dad?, dama ya Abdallah ba ni yake k'auna ba wata ce can ta ban, tana gama fad'a ta rushe da gunjin kuka tare da barin wurin a guje ta shige masauk'in su tare da sa sakata ma door d'in ta jingina jikin ta da bango tare da tsugunna k'asa ta hau sakin kuka mai cin rai.
      Nocking dad d'in ta ke yi babu gaggautawa a kan ta bud'e, tana ji tayi birisssss ta kiya ta kwanta ragwaffffff a wurin tana fidda kwalan bak'in ciki, a take jikin da ya d'au zafi rad'auuuuuu.
     Wasa wasa sai da ta kwashe awa sama da awa d'aya a hakan da kyar aka samu ya b'alle k'ofan cikin rashin sa'a har ta jigata ta fita hayyacin ta, hankali a tashe ya sungumo ta waje yayi wurin mutani da ita dai dai nan Ash da abban ta suka fito me idon ta zai nuna mata inba tee ba, me ya kawo tee gidan su?, ta jefo ma kan ta tambaya.
      Cikin halin koh in kula ta gefer da kan ta gefe har suka iso wurin jama'ar wurin a tare nan kuwa ta ga mum d'in ta tayi wurin d'iyar ta tana kuka tana jijjiga ta a hankali.
      Tabasss tee ce idan haka ne me alakar ta da gidan su?, koh ita ma ta san da maganar auren ne ta boye mata kamar yanda su abban ta suka mata, da wannan tunanin ne ta tak'o zuwa wurin teee da zuwa yanzu bata iya gane inda kan ta yake tace" tee teee teeeee d'ita me yasa kema kika rufe min maganar kema, kin manta cewa mu friends ne and kuma we don't used to hide secrets to our selves?.
       Haka dai take ta magana babu alamar tee d'in na jin ta mum ce ta d'ago ta da yake dad ya fad'a mata komai game da abunda yake faruwa yasa tausayin da take mata yanzu ya ninka wanda take mata a baya, a haka aka d'auki tee sai hospital ita ma aka yi emergency da ita.
      Haka zuciyoyin bayin Allahn nan yake cikin kunci sun rasa mafita. Time d'in da ake shigo da tee time d'in ne aka tuk'o sickbay d'in ya Abdallah da Suhail zuwa waje aka shigo da su wani madaidaicin d'akuna guda biyu makofta juna, Ash na ganin sanda aka wuce da su Suhail ta gaban su kan ka ce me har ta riga su dad shigowa d'akin, d'akin da aka kwantar da Suhail ta ta fara shiga da isowan ta ta kifa kan ta a kan gadon sai ga hawaye sharrr sharrrrr a fuskan ta.
     Difffff ya fara fidda sautin numfashi ahankali bata sani ba har ya bud'e a hankali ya bud'e eyes d'in shi ya sauk'e shi fesss a kan ta tare da tallab'o fuskan ta suna had'a ido sai ga mak'alallen hawayen da yake shirin boye mata sun zubo, tana ganin haka ta fad'a cijin shi tana kuka tace" kaga ni koh an mana katanga da junanan mu, an haramta mana zama karkashin inuwa d'aya da junan mu.
     Tsiraren hawaye ne suka fara zarya a fuskan shi cikin k'unan rai yace" me nai musu ne da suka raba ni da ke, why !!! why !!!  why !!!, ya fad'a cikin d'agun murya.
      K'ok'arin d'ago ta yayi daga jikin shi yana mai jin wani irin bak'in ciki a zuciyar shi, ya had'iye miyau mai tsananin d'aci kana ya furta" sun haramta min ke, sun ruguza min farin ciki na da rayuwa ta tell me ta yaya zan iya rayuwa babu ke? You are my life and every thing.
      Su dad suna daga bak'in k'ofa da doctors suna kallon abunda ke faruwa sosai abun ya dake zuciyar su amma there is no way out dolle masoyan su d'au hak'uri tunda aikin gama ya riga ya gama.
      Cikin dak'iyar zuciya yace" sorry to say son tabbas d'an uwan ka ya biye ma son zuciya cutar da mu,, abba kuwa kawar da zuciyan shi yayi gefe ba tare da yace komai ba.
      Jiki a sanyaye ta bar jikin bed d'in tayi wurin doctor tace" kai ni naga halin da d'an uwana yake ciki pls doctor.
     Haka suke tafiya tana biye da su har suka kawo bakin k'ofar d'akin, a sanyaye ta murd'a handle d'in k'ofan ta shige ciki tare da nufar inda yake.
     Ba k'aramin tashin hankali ta shiga yi ba da ta tarar da halin da Abdallah yake ciki, koka ta kama yi har sai da doctors suka jata waje dan gudun kar ta lalata musu aikin da basu da tabbacin nasarar shi.
          A gida kuwa bayan barin su gidan jama'a aka hau watsewa da d'add'aya da d'add'aya koh waccen su na tofa albarkacin bakin ta, inna Laraice daga waje na gan ta tana nufo wurin su dan tun lokacin da ta iske su Aysha da Abdallah a tsakar gida ta bar gidan saboda gudun kar Ilu ya tarar da ita a halin da ake ciki ya bata kunya cikin mutane dan ta san cewa kad'an ne daga cikin aikin Ilu kenan.
       Tun daga inda take taji matan na k'ananan maganganu k'asa k'asa tana matsowa k'usa da su taji wata mata tace" ni koh Ramlatu lamarin nan ya d'aure min kai ashe ba da sanin wan mahaifin yarinyar da kuma ita kan ta yarinyar aka yi auren ba, hasali ma tuggun Sumayyah ce".
      D'ayar matar ta kwanco zani tare da gyara d'aurin zanin ta lokaci guda ta karkato wuya tana mai kallon wacce tayi magana tace" Allah Ladiyo?
      Kwarai kuwa Mari ashe wai Abdullahi d'an inna Larai yake ta dak'on son ta idan baki manta ba kwanakin baya akan son da yake ma yarinyar ne ya gudo daga gida cikin rashin sa'a kuwa bai sani ba ashe auren ta ake d'aurawa. Na takaita miki ma mutanin da suka halarci d'aurin auren sai cewa suka an kwashe shi rab'e rab'e zuwa babban asubiti koh yaya uwar zata yi idan taji maganar koh da yake bak'in halinta ne ya ja mata.
      D'ago indon da inna Mari zata yi ta ga Larai ta k'usa zuwa inda suke, da sauri ta hau fisgan hannun Ladiyo murya k'asa k'asa tace" shiru gata nan zuwa kar ta jiyo mu mu shiga uku da masifa ai kuwa Ladiyo tayi saurin yi ma bakin ta lizami.
      Koh kad'an inna bata kawo komai a zuciyan ta ba ta banka musu harara cike da masifa tace" munafukan banza duk na jiyo abunda kuke fad'a, aniyar ku ta bi ku dan bakin ku yayi kad'an ya kama Abdallah na, haka dai take ta yarfa ruwan masifa su koh suna ganin haka suka ja jiki sumi sumi suka b'ace a wurin.

        Sadeeq kam nashi b'angaren yana ganin an sako su Abdallah a mota kamar bawa za'a yi asubiti da su yayi saurin barin wurin dan bai da idon da zai had'a da su dad saboda kunyar abunda mahaifiyar su tayi musu, tun da ya had'a ido ya gan su a gidan bai yi wani mamaki ba dan yasan akwai abunda suke kullawa duk da dai cewa tunanin shi bai bashi hakan ba.
      Ya jima a b'oye a gindin bishi yana sharar kwallan takaici har motar da aka sako su Abdallah ta wuce a gaban idon shi, har fitowan Suhaib sannan ya fito daga lab'en da yake ya damk'o shi yace" munafuki marar mutunci, ya fad'a tare da kai mishi naushi a hanci sai ga hancin ta fashe jini na bin wurin.
      Rai na tafarfasa Suhaib ya ture shi daga jikin shi ya kai mishi bugu shima Sadeeq ya goce, da yake a galabaice yake zai kuma kai ma Sadeeq bugu da sauri ya goce ya rik'o hannun Suhail ya murd'a ta da k'arfi, da kyar mutane suka kwato shi a hannun Sadeeq aka raba su kana Suhail yayi hanyar Jos koh biya wa ta gidan su Aysha bai tsaya yi ba Allah ya taimaka da d'an caji a wurin shi yayi amfani da shi yayi kud'in mota cuz bai jin zai iya tuk'i a halin da yake ciki.
        Sadeeq kuwa gidan su Aysha ya nufa cike da tarin takaici yana isowa ya ga zee da ummi Sumayyah su biyun su dan inna Larai ma da ta shigo bata bi ta kan su ba ta shige d'aki, bai ce da su komai ba ya fisge hannun zee da k'arfi yayi hanyar waje da ita hakan ya bala'in d'aga ma mahaifiyar su hankali ta dama mishi tsawa cikin tsananin b'acin rai tace" Sadeeq ina kuma zaka da ita?, k'anwar taka kake ma haka?, koh sauraran ta bai yi ba ya k'arasa ficewa daga gidan hannun shi na rik'e da na zee, suna fitowa ya tusa k'eyar ta cikin mota nan ne kuwa idon zee ya raina fata, tana ganin sanda ummi Summayyah ta fito da uban gudu ta d'ora hannu a ka ta kurma uban ihu amma haka Sadeeq ya tada motar ya tafi da zee.


*eedatou✍🏻*
      ~Y'ar mutanen Dengi~

WAYE MACUCIWhere stories live. Discover now