🏵🏵☀☀🏵🏵☀☀🏵🏵
*☀WAYE MACUCI☀*
🏵🏵☀☀🏵🏵☀☀🏵🏵
'''Suhaib koh Suhail'''***********************************
® *REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS P.M.L*💭💭💭
_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_
# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
©
'''Marubuciyar Rayuwar Sumayyah'''*SA'EEDA MUSA DAUDA😍*
'''Follow and ✅ote me on Wattpad''': *eedatou*
*BESTORED TO MY LIL SIS* ''' SUMAYYAH MUSA DAUDA'''3⃣9⃣
Ganin Aysha a jikin Suhail tana ihu tana kuka da kuma yanda su mum suke bin hawaye ke ta ambaliya a fuskokin su mum ya dad'a fusata dad, gadan gadan yayi kan Suhail ba tare da ya duba halin da ake ciki ba ya shak'o wuyan shi da k'arfi yana cewa" i was disappointed in you, ashe dama kai ne macucin da ya zalunci wannan yarinyar ? kai ta nemi cin zarafin ta ka kai ta gidan karuwai domin ka bata mata suna ? you deceived me da kake nuna ma Aysha fake love bayan dawowa na not nowing that are a monster that is hidding himself under my unbrella, so i prefer na kashe ka wallahi kowa ma ya mutu tunda zuciyar k'afurai ne da kai".
K'iris ya rage Suhail ya yarda Aysha a k'asa saboda ba k'aramin shak'o wuyan shi dad yayi ba da sauri ya fara tari yana gwalalo ido, dad kusa saurin sakin sa yayi ya taro Aysha da zuwa yanzu ta fara tsagaita kukan,,
hankali a matuk'ar tashe ya raba ta da jikin Suhail tare da watso ma mum uwar harara ya nufi motar shi da sauri ya bud'e back seat ya turo Aysha a ciki tare da rufo k'ofan ya zagayo ta d'aya site d'in ya shige tare da jan motar a guje yabar wurin yana bad'a ma su mum k'ura.
Ganin haka yasa su mum bin bayan su a mota da guda kowa a cikin motan zuciyan shi cike yake da tashin hakali.
Gudu suke sosai a hanya kamar zasu tashi sama musamman dad da yake tuk'i ba acikin hayyacin shi ba burin shi ya ceto matainiyar Allah daga halin da *macucin* d'an shi ya jefa ta a ciki, a zaton dad Suhail ne *macucin* da ake cutar da Aysha not knowing that is his twin brother, basu wani b'ata nokaci ba sai gasu sin iso gida da taimakon Allah kuwa zuwa yanzu Aysha ta daina kuka,,
Fitowa dad yayi daga motan tsabar b'acin rai har eyes d'in shi sun turning red dan idan baka lura da kyau ba baza ka ga farin kwayan cikin idanuwan shi ba,,
inda Aysha take zaune a back seat ya nufa ya rik'o handle d'in motan hannun shi kuwa sai shaking yake yi da kyar ya iya murd'awa ya bud'e tare da rik'o hannun Aysha zuwa cikin gidan.
Kai tsaye d'akin Aysha ya nufa ya shige ban d'aki ya had'u mata ruwan wanka ya fice a band'akin ya bata wuri ya koma palour dan ta watsa ruwa dan ya tabbata zuwa hanzu k'aik'ayin ya lafa saboda tun a mota yake lura da ita.
Fitan shi ke da wuya Aysha ta soma rage kayan jikin ta, ita kad'ai ta san irin azabar rad'ad'in da ta d'and'ana a wurin yayan ta, anya bawan Allan nan ba so yake yaga bayan ta ba ?, tambayar da tayi ma kan ta kenan har ta gama cire kayan tana dafa wuri cikin sa'a hannun ta ya sauka a birthtub, shigewa ciki tayi ta zauna tare fashewa da matsananciyar kuka.
B'angaren dad kuwa yana isowa parlour zagaye parlourn ya hau yi yayin da zagaye hannayen shi biyu ta baya ya d'ora a mazaunen shi,,
tunda yake bai tab'a jin b'acin rai kamar ta yau ba k'arin abun bak'in ciki ma wai ace a gidan shi *macucin* yake amma ya kasa ganowa tabbbbbb dole da had'in bakin Maryam aciki yana kyautata zaton da goyon bayan ta macucin ke zaluntar Aysha ba tare da sanin shi ba, in koh haka ne tabbas Maryam taci ammanar shi, ta tarwatsa dukkan yardar da ya bata kuma ba zai bar ta ba dole ita da d'an ta su fuskanci hukunci gwargwadon laifin da suka aikata.
Suna wannan yanayin ne sai ga su mum sun shigo d'ankwali a hannu ta nufe wurin dad ta kneeling a gaban shi ta rushe da kuka tace" forgive me dear wallahi ban da hannu a cikin laifin da kake tunanin na aikata hasali ma da na san hakan zata faru da ba zan bari ba".
Dad bai yi wata wata ba ya ture ta gefe granny ta taro tana buga bayan ta a hankali, rasa abun cewa granny tayi sai bin kowa da kallo take yi dan sun bala'in kulle mata kai, wai ace ranar da aka d'auki tsawon watanni ana shirya ma zuwan ta sai yanzu da Allah ya kawo su ranar amma tazo musu da tashin hankali ?, wannan wacce irin bak'ar rana ce haka?, granny ta fad'a a k'asan zuciyar ta.
Zuciyar Suhail ya karaya sosai da ganin irin yanda dad ya d'au zafi da yawa but da yayi la'akari da irin tozarcin da Suhaib yake ma Aysha sai yaga ai dole ne dad yayi fushi da yawa, but abun da ya bashi mamaki shine yanda dad ya shak'o shi ba tare da ya tsaya yayi bincike ya gano macucin ba, infact ma ta yaya aka yi dad ya san yana da alaka da macucin ?
Jikin a sanyaye Suhail ya taso za shi gun dad wani irin mugun kallo da dad ya watso mishi ne yasa ba shiri ya ja burki ya tsaya a wuri d'aya, a take yaji legs d'in shi sun mishi nauyi ya kasa komowa da baya,,
granny ce tayi k'arfin halin magana tace" haba Alhaji idan rai ya b'ace hankali ba zai gushe ba, duk da dai ban san irin gurman laifin da y'ar nan(mum) ta aikata maka ba bai kamata kana d'aga hankalin ka har haka ba,,
ya kamata ka bi komai da sannu sannan sai a samo mafita.
Tsayawa caakk dad yayi a wuri d'aya yace" granny Maryam ta cutar da ni dayawa bisa dukkan alamu so take ta ga bayana".
Haba Alhaji da girman ka kake fad'an wannan maganar abunda da tun k'uriciya sab'ani bai tab'a shiga tsakanin ka da iyalen ka ba shine kake ik'irarin cewa matar ka tana son ganin bayan ka ?, toh in koh haka ne me dalilin da ya sanya kake fad'an haka, cewar granny kenan dan zuwa yanzu ran ta ya fara b'aci da irin munanan zafafan kalaman da dad yake gaya ma y'ar ta dan cin fuska ma in her presence.
A yanda granny tayi maganar dad ya gano da alamar b'acin rai a ciki amma a yanda yake jin zuciyan shi na zafi baya jin zai iya yin rangwame ma mum da d'an ta.
Ba tare da yace komai ba ya barsu a parlourn yayi shigewan shi d'akin Aysha dan dubowa koh ta gama yayin da mum ta dad'a k'ara sautin kukan nata Suhail da granny na bata baki Jummai kuwa na rakub'e a wuri d'aya ta k'asa kwakkwaran mosti dan ita ma kanta bata da masaniya a kan abunda yake faruwa da uwargijiyar ta.
Dad na shigowa d'akin Aysha ya lek'a inner room d'in ta bai gan ta ba, har ya juya kenan yaji k'arar sauk'owan ruwa a ban d'akin ta,,
sosai yaji mamakin ganin har yanzu bata fito daga band'aki ba toh me ta tsaya yi ?, "kuka", amsar da ta fad'o mishi a rai kenan.
Nufar k'ofan yayi da isowan shi ya manna kunnen shi a bakin k'ofan band'akin, abunda kunnuwan shi suka jiyo mishi shine sautin sheshek'ar kukan Aysha da ke tashi a hankali, bai san sanda hawayen tausayin ta ya kwace mishi ba ya hau nocking.Pls share
*eedatou✍🏻*
~Yar mutanen Dengi~
YOU ARE READING
WAYE MACUCI
Historical FictionLabari ne a kan wata mak'auniyar Allah mai suna Aysha wacce take soyayya da yayan ta amma kwatsam sai wata tsautsayi ya afka mata har hakan ya saka ta cikin bakin ciki,ba tare da ta bayyana mishi ba sai daga baya ya fahimci halin da take ciki a tsan...