🏵🏵☀☀🏵🏵☀☀🏵🏵
*☀WAYE MACUCI☀*
🏵🏵☀☀🏵🏵☀☀🏵🏵
'''Suhaib koh Suhail'''***********************************
® *REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS P.M.L*💭💭💭
_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_
# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
©
'''Marubuciyar Rayuwar Sumayyah'''*eedatou😍*
'''Follow and ✅ote me on Wattpad''': *eedatou*
*BESTORED TO MY LIL SIS* ''' SUMAYYAH MUSA DAUDA'''4⃣8⃣
Safiyar asabar ta kama dai dai da ranar da granny ta yi ma Suhaib alkhawari cewa zata zo har gida ta same su mum akan maganar da suka yi, cikin ikon Allah kuma sai gashi ta cika alk'awarin tana shigowa tun daga bakin k'ofa ta hau kwala sallama su mum da tun daga d'aki suka jito muryar ta aparlour suka firfito, suna ganin ta cikin had'in baki suka ce "sannu umma", kallo ta bisu da shi ta tab'e baki tace" ku rik'e gaisuwar taku bana bukata".
'''"Subahanalillah''' me yayi zafi umma", dad ya fad'a tare da maida kan shi k'asa.
A masifance granny tace" haba alhaji fisabilillah kun kyauta kenan"? ace har hanzu baku sauk'o daga fushin da kuke da yaron nan ba, koh gaisuwa yayi muku bakwa amsawa haba, so kuke sai ya mutu kana ku huta?, ta k'are maganar tare da zaro mayafin jikin ta ta wurgo a kan three seaters kana ta nemo wuri ta zauna.
Shi Suhaib d'in ne ya fad'a miki cewa bama kula shi, cewar mum kenan.
Kin ci gidan ku Maryam, granny ta fad'a tare da rike k'ugu kana ta d'ora da cewa" ni sa'ar ki ce da zaki tsare ni da tambaya?, yo sai wani ya fad'a min abun da ke tafiya a gidan nan ne bayan na san komai",?.
Masifa sosai granny ta hau yi musu ta inda take shiga ba ta nan take fita ba su mum kuwa sai bata baki suke yi, sai da ta musu tatas kafin ta aika Maryam ta k'irawo mata yaran, mum bata d'au lokaci da barin wurin ba sai gata ta shigo da su Suhaib biye da ita a baya, kana ta shige d'akin Aysha tayi k'iran ta ita ma ta fito ta zauna.
Sai da suka gama hallara kana granny ta bisu da kallo d'aya bayan d'aya ta maida fuskan kan dad tace" alhaji", "na'am umma".
Wannan karon alfarma nake nema a wurin ku, na san baku san da cewa Suhaib ya kamu da k'aunar Aysha ba, so nake a d'aura musu aure idan ba haka ba kuma muna dabbbb da rashi a gidan nan".
A razane su mum suka d'ago da kai suna kallon granny can kuma Suka maida fuskan su kan Suhaib da sauri ya sadda kanshi a k'asa kamar munafiki zuciyan shi cike da tsoron abunda zai biyo baya but a yanda yake jin kan shi he is ready to face any challenges matuk'ar a kan Aysha ne".
Suhaib kam gumi ne ya soma d'iga daga kan shi, kan kace wani abu sai gashi zufa ya wanke mishi jiki tasss saboda tsabar tashin hankalin da yaks ciki, b'angaren Aysha kuwa kana kallon fuskan ta hango tashin hankali ne tsantsa.
Kuuutttt Suhail ya had'iye miyau mai d'aci yana magana cikin sarkewar murya yace" haba granny ya zaki min haka why eehhee bayan kowa ya san Aysha tawa ce, da ni tafi dacewa, dan Allah kar ku raba ni da Aysha wallahi muna matuk'ar k'aunar junanan mum, she is mine, ita tawa ce idan kuka yi hakan baku mana adalci ba dan mun sasanta kan mu".
Shut up my friend, dad ya daka mishi tsawa a hasale yace" duk irin cutar da ka mata shine kake cewa ka dace da ita ?, ka sani Suhaib shi zai aure Aysha ba kai ba saboda duk tsanar da ya nuna mata bai kai abunda ka yi mata ba sakarai kawai".
Suhaib kuwa dad'i ne ya lullub'e shi, saboda bai tab'a tunanin su dad zasu yi saurin ammincewa da buk'atar shi ba.
No dad hukuncin da kuka d'auka yayi sauri da yawa Suhail ba *macuci* bane, suka jiyo murya daga waje yana tunk'aro parlorn su duka suka jiyo suna kallon bakin k'ofan d'akin, Sadeeq ne ya shigo parlorn ba tare da ya zauna ba ya nufi gaban dad ya tsaya tare da cewa" yeesss dad na san na jefa zukatan ku cikin mamaki but first of all zan so na fad'a muku kad'an daga cikin abubuwan da suke faruwa".
Cike da takaici dad ya d'aga mishi hannu yace" dakata Sadeeq me zaka fad'a da zai gamsar da mu bayan abunda kunnuwan mu suka jiye mana ?
Yess dad ni kuwa nake da hujja mai k'arfi na san idan na fad'a muku you will believe me, zama yayi a kusa da Suhaib ya nad'e k'afafufan shi ya hau bama su dad labarin duk abunda ya faru from A to Z har ya gama.
Ba k'aramin mamaki suka yi ba da jin irin abubuwan da suka fito daga bakin Sadeeq, granny da bata san kwanar zancen ba sai zuwa yanzu ta doke salati tana tafa hannu kana ta buga uban tagumi kamar ruwa ya ci ta, dan ita kad'ai ta san irin abunda yake bugun ta a zuci.
Tun farkon fara labarin har aka k'are mum take ta aikin kuka saboda tausayin Aysha da taji, babban abunda ya tsaya mata a rai shine yanda har Suhail ya raping d'in ta a buge Allah ne kad'ai ya san irin wahalar da ta sha a hannun shi,bugu da k'ari kuma Aysha nakasashiya ce a lokacin how will she fell and who assisted her ya gyara mata jiki.
Sadeeq na gama rufe baki Suhaib yace" please dad kar ku yarda da abunda yace wannan wasan kwaikwayon an yi shi ne domin rusa had'in aure na da Aysha, kallon Aysha yayi yace" shin zuciyar ki zata iya amincewa da k'anina kuma *macuci* ?,ya girgiza lokaci guda ya d'ora da cewa" noooo you won't Suhail bai san darajar ki ba tunda ya keta miki haddi bai tausaya ma irin halin da kike ciki ba a matsayin ki na nakasasshiya, sanan kuma hai tausaya ma halin da zaki shiga a sanadiyan shi ba sai daga baya ne yake nuno miki shi mutum ne ya zo miki da wata fuskan.
Hawaye ne ya gangaro a fuskan Aysha ta sa hannu d'aya ta share ta wurgo ma Suhaib hararar tsana ta mik'e tsaye tace" *WAYE MACUCI*? '''Suhaib koh Suhail"''', su duka suka bi ta da kallo, ta saki murmushin takaici, wani irin rad'ad'in da take ji a zuciyan ta tamkar an sa mata dafi, Sadeeq yayi saurin k'arb'e zancen yace" Suhail shine cikakken masoyi wanda ya san martabar ki da k'imar ki, dare da rana yake zubar da hawayen nadama akan abunda ya faru a tsakanin ku, kin san dare nawa ya b'ata yana kunci a sanadiyan ki?, dad koh kun san cewa duk kuncin rayuwa da Suhail ya shiga a sanadiyan Aysha ce?, for how long ta dakon ki a zuciya ya gan ki ya nemi afuwar ki?".
Tabbas maganar ka gaskiya ne Sadeeq babu namijin da yafi dacewa ya aure Aysha kamar Suhail, abunda ya faru tsakanin su sharin aboki ne shi yasa ake cewa a guji mugun aboki dan wataran zai iya b'ata maka rayuwar ka, kenan da tun farko Suhail baya alaka da abokin nashi da hakan bata faru ba, na biyu kuma k'aryar da kuka shirga mana kuka je sarvice a Dengi ba tare da kun sanar da mu ba kun ga koh a nan hakkin mu zai iya bin d'ayan ku".
Haka ne alhaji Suhaib kuwa son zuciya ne tsantsa ya kai shi ga zaluntar Aysha, shi yasa ake so a koh da yaushe mutum ya fi k'arfin zuciyan shi dan wata ran zai iya kai mutum ga dana sani, sannan kuma kar ka kyamace wata halittar Allah tunda shi da yayi kayan shi bai kyamace su ba, kuskuren da kayi kenan Suhaib wanda zai iya jawo maka rasa Aysha a rayuwar ka.
Ciro hannu granny tayi a kuncin ta tace" Suhaib nayi nawa k'ok'arin na gama domin ba zan iya tilasta ma Aysha ta aureka ba yin hakan kamar na zalunce ta ne, ita take da daman da zata zab'a ma kan ta zab'in zuciyar ta tsakanin ku biyun kuma ina farin ciki da zabin da zata yi.
Ido ne ya koma kan Aysha kowa na son ji daga gare ta, cije libs d'in ta tayi cike da takaici kamar baza ta ce komai ba, sai da ta danne ran ta kafin tace" dad to me every thing has gone, zab'ina na da shine a raina bana canjawa saboda na yarda da k'addara.
Murmushin farin ciki ne ya bayyana a fuskokin su su duka banda Suhaib da hankalin shi yayi dubu ya tashi, ji yake kamar ya mutu dan huta da azaban bak'in cikin kalamanta masu k'ona mashi zuciya,,
haka dai suka watse a taron Suhail kamar ya goye friend d'in shi a baya saboda tsabar murna zuciyan Suhaib kuwa kamar an had'a gobara.
**********************************
B'angaren tee kuwa bata samu daman had'a yayan nata da friends d'in ta ba kasancewar ranar fashi makaranta ne, Monday nayi da safe bayan ta gama shiryawa ta fito a dinning ta tarar da family d'in ta suna breakfast ta ja kujera ta zauna tana fuskantar yayan nata tare da gaishe da iyayen nata tana gamawa ta turb'une fuska tana kallon yayan ta da ke ta aikin danne danne a phone d'in shi, ganin bai san ma tana yi ba cikin shagwab'a ta turo baki tace" uuhhmm uuhhmm bros, d'ogo kan shi yayi yace uuhhmm har kin fito ne k'anwata?, dad'a turo baki tayi tace" oohh baka ma san na fito ba koh ?,,
Yi hak'uri k'anwata wani abu ne nake gani ya d'auke min hankali a waya ta".
Wato abun ya fini muhimmanci kenan koh?
haba k'anwata yaya kike so nayi ne ? ba dai nace ki yi hak'uri ba?, ai babu abunda zan yi a waya ya fi min k'anwata muhimmanci come on ci abincin ki mu tafi tun kafin kiyi latti seniors su zane min ke", ya k'are maganar yana turo mata abincin gaban ta.
Shagwab'a ta kuma sakar mishi tana buga dinning table da hannu biyu tace" ni dai ban ci sai dai ka bani cuz jiya na yanke da knife a kitchen da mum take koya min girki".
Idan wannan ne mai sauk'i ne amma fa sai kin saki ran ki idan ba haka ba kuma na k'i, sake ran ta tayi yana feeding d'in ta suna tsokanar juna suna dariya suka mance da iyayen nasu, sai da suka gama kana suka ankara da su shi d'in ma dan sun ga suna musu dariya ne yasa, a kunyace suka bar wurin su suka fice daga gidan suka shige mota sai school.
Tun a mota tee take mishi tuni a kan maganar su na had'uwa da su hibb da Ash har suka iso school.
B'angaren Aysha kuwa a tare suka fito da Suhail cikin shirin ta na tafiya makaranta suna hirar su cikin nishad'i suna nufar parking space. A cikin hirar tasu ne naga Aysha tana sakar ma Suhaib shagwab'a wai sai lallai ya koya mata driving, shi kuwa cewa yayi" baby is too late fa you are going to school zaki yi late fa", eehh eehh d'in ni dai kawai ka koya min i want to be driving by my self", ta k'are maganar tare da yunkurin k'arb'o car key d'in a hannun shi.
Fatan jikin su na gogayya da juna suka ji yarrrrr a jikin su, tuni suka fara aika ma juna sakonnin kallo mai cike da tarin ma'ana har na tsawon mintuna, Aysha ce ta fara ankara da abunda suke yi da sauri ta d'auke idon ta daga kan shi ta maida gefe, karabbb eyes d'in ta ya sauk'a akan Suhaib da ke kallon su ta tagar parlor, koh a jikin ta dan ta k'ara mishi haushi ta huro ma Suhail iska a ido, lumshe eyes d'in shi yayi a k'asalace yana kallon ta, "wannan kallon fa", ta fad'a tana sura mishi na mujiya, murmushi yayi ya sarke hannayen shi tare da jingina bayan shi a jikin mota yace" ke kika zautani baby, a duk lokacin da nake tare da ke ina loosing control ban san me yasa ba".
"Uummm" ta fad'a tare da waino eyes balls d'in ta tace" kar ka cika min kunne da dad'ad'an kalaman ka ka haddasa na rasa sukuni ya zamto koh darasi ake a aji na kasa fahimta nayi ta tunanin ka masoyi na".
Ashe dama bakya tunani na ni koh hatta kwarrun numfashi zan yi sai na tunano ki, rashin ki tamk'ar bankwana da farin ciki a rayuwa ta",
Blowing mishi wind ta kuma yi tare da waino eyes d'in tace" really sahibil qalbi".
Oh yess"heartbeat, fakon shi ta yi ta zaro car key d'in a hannun shi ta ruga a guje yana bin ta a baya har suka shige cikin wata mota ash colour, Suhaib na ganin haka ya dafe kan shi da sauri yace" Ohhh shhhiiittt, Aysha why !!! why !!! the hatred !!! baby don't turn your back on me cuz i really deserved you, wallahi son da nake miki ne da kuma kishin ki yaja na miki abubuwan da suka faru a baya, zuciyata baza ta jure rashin ki ba, haka dai yake ta fad'a yayin da hawaye suka fara kwaranya a fuskan shi.
B'angaren su Aysha kuwa jan motar suke yi hannayen su na had'e da na juna a kan steering motar, tana zaune a driving seat yana zaune a d'aya b'angaren har suka iso makarantar.
Da yake ba da wuri ta fito daga gida ba bata wani b'ata lokaci a gurin Suhail ba ta yi shigewar, tana barin wurin ya tada motar shi sai gida.
Tafiya take tana sauri ta shige aji saboda yau maths teacher ne da darasi, tana cikin tafiya ne bata sani ba ta bangaje wani matashin bawayan Allah, ya juyo kenan yana waya ita kuma garin sauri bata gan shi ba suka had'e da juna jakan ta ya fad'i k'asa, da yake garin sauri ta fito daga gida ta maida takardar da tayi assignment d'in da mai English ta basu bata tsaya ta maida zib d'in jakar ta ta rufe da kyau ba takardun ta da ke ciki suka watse a k'asa. '''Subahanalillah''' ta furta da d'an k'arfi lokaci guda ta bi mutumin da kallo, ba tare da ya dube ta ba ya tsugunna yana picking books d'in da suka zube d'aya bayan d'aya tare da ci gaba da wayan da yake yi, yana gamawa ya mik'a mata a hasale ta k'arb'a ta shige tana jero uban tsaki abunda ya d'auke hankalin shi kenan yayi saurin katse wayan yana bin bayan ta da kallo yana mamakin halin ta ai koh ba komai ita ta bige shi bai damu da hakan ba ya tsugunna ya tattaro mata takardun ta".
A take fad'uwar gaba ta kama shi lokaci guda ya hau tunanin inda ya tab'a ganin mai suffa irin ta ta, yayi yayi ya tuna ya k'asa ya ja guntun tsaki sai ga tee da hibb sun zo wurin shi, ohhh sorry yaya na nayi ta neman Ash ban ganta ba k'ila sai zuwa gobe zata shigo ga k'awata hibb ku gaisa, ta k'are maganar tare da nuno mishi hibb da hannu.
Shine kika shanya ni koh da na k'ira wayan ki kike ce min k'ar na tafi da tuni na bar harabar makarantar ku dan dai bana son ganin ki cikin fushi ne yasa na tsaya".
Afwan yayan mu kar kayi fushi da mu please, cewar hibb kenan ta fad'a tana marairaice fuska.
Kin ci sa'a k'anwata ta bani hak'uri da na d'au hukunci, sai da suka gaisa da tee sannan ya yi musu sallama ya data motar shi suna waving d'in shi har ya b'ace musu da gani.*eedatou✍🏻*
~Y'ar mutanen Dengi~
YOU ARE READING
WAYE MACUCI
Historical FictionLabari ne a kan wata mak'auniyar Allah mai suna Aysha wacce take soyayya da yayan ta amma kwatsam sai wata tsautsayi ya afka mata har hakan ya saka ta cikin bakin ciki,ba tare da ta bayyana mishi ba sai daga baya ya fahimci halin da take ciki a tsan...