🏵🏵☀☀🏵🏵☀☀🏵🏵
*☀WAYE MACUCI☀*
🏵🏵☀☀🏵🏵☀☀🏵🏵
'''Suhaib koh Suhail'''***********************************
® *REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS P.M.L*💭💭💭
_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_
# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
©
'''Marubuciyar Rayuwar Sumayyah'''*eedatou😍*
'''Follow and ✅ote me on Wattpad''': *eedatou*
*BESTORED TO MY LIL SIS* ''' SUMAYYAH MUSA DAUDA'''5⃣2⃣
Da isowan ta ta hau nocking ya fito ya bud'e mata tare da amsar trey d'in da ta d'ora fruit salat d'in a kai ya d'ura bisa table, kallon ta yayi ido cikin ido yace" baby na nasa ki aiki koh?,
Kallon shi tayi for some minutes ba tare da ta ce komai ba, ta zauna a d'aya daga cikin kujerun d'akin tana murza zoben hannun ta tana yin murmushi k'asa k'asa.
A sanyaye ya matso kusa da ita, ta yanda suke shakar numfashin juna ya rik'o hannun da take murza zoben cikin kasala yace" kin ga kuwa yanda zoben nan ta miki kyau kuwa baby na, anya ba wayo kika min kika kwace zoben nan a hannu na ba kuwa ?, ta galla mishi hararar wasa a shagwab'e ta turo bakin ta waje tace" ummm ummm Allah baby zamu yi fad'a da kai muddin kana tuna min da past d'ina, do you know how I felt kuwa ?, ka san wacce irin azaba ka d'and'ana min kuwa, baby gashi ban da wanda zai assisting d'ina dad time and kuma ban da idon gani, haka nayi ta b'oye wa azuciya ta day and night ina kwana da kunci, ta yi rau rau da fuska kamar zata yi kuka.
Cike da tausayin ta ya tallab'o hab'an ta yana kallon kwayan idon ta, shi kad'ai ya san irin abubuwan da yake ji idan yana tare da Aysha, so tarri yana loosing control d'in shi, sai ya dinga jin kwakwalwar kan shi na koma mishi kamar na karamin yaro, k'irjin shi ne ya hau beating da sauri da sauri, jin yake kamar ya rungumo ta dan ya samu relief d'in shauk'in k'aunar ta da ya dad'e da cika mishi zuciya, da kyar ya iya saita nutsuwar shi, ba tare da ya kawar da fuskan shi gare ta ba yace" i'm sorry baby na san na hurting d'in ki da yawa, and kuma na riding d'in ki roughly wish i was totally out of my senses but belief me, i promise idan muka yi aure sai kin ammince min kafin nayi abunnan you get me?,
Kunya ne sosai ya kamata kamar ta nitse a k'asa saboda kunyar shi, cike da tsananin kunya ta rufe fuskan ta da tafukan hannayen ta tace" ummm ummm baby ni dai koh mun yi aure ba tare zamu dinga kwana ba, ni dai ba za'a kuma wannan abun me bala'in zafin ba, saboda ni k'arfe ne koh ?, ya jefo mata tambaya tare da tsare ta da ido.
Kok'arin cire mata hannun da ta rufe fuskan ta da shi yake yi yana cewa" bud'e fuskar ki ki amsa min tambaya ta, ita koh sai dad'e manne hannun ta tayi a fuskan ta tana dariya k'asa k'asa,
ganin da gasken shi yake yi ta mik'e tsaye ta kwasa a guje tana maida numfashi, yana ganin ta fice ya cike lips d'in shi na k'asa lokaci guda yana shafo suman.
Aysha na fita yaci karo da Suhaib da dawowan shi daga Dengi kenan yana k'ok'arin haurowa matakalen benen za shi d'aki, trusss ta ja ta tsaya tana jiran ya wuce ta sauko main parlour, yana isowa wurin ta ya ja ya tsaya ya hau bin fatar jikin ta da wani irin mayataccen kallo yana lumshe ido kamar wani tsohon maye,,
"Mtswww" ta ja dogon tsaki tace" dallah mallam idan saka wuce ka wuce idan kuma baza ka wuce ba sai ka matsa ma mutane su wuce ka so ka wani tsayawa a hanya k'erere kamar wani tsohon munafuki,".
Maimakon ya ji zafin maganar da ta hab'a mishi, sai ha tsinci kan shi da gyara tsayuwa a jingina a jikin matakalar benen ya hau jifan ta da murmushi, hakan ya dad'a hasala ta, a fusace ta tsirta mishi miyau a jiki ta rab'a ta jikin shi tace" mayye matar zuciya wahalalle".
Sai yanzu ya samu damar yin magana yace" ni kika watsa m miyau Aysha ?, koh dan kin ga ina son ki ne kika samu daman raina ni da yawa?, yana maganar ne yana bin inda miyau d'in ya b'ata da kallo.
"An fad'an ka yi duk abunda kaka ya dace ka yi, raini kuma yanzu ka fara shan ta a gidan nan mtswww tayi shigewan ta rai a b'ace, koh bi ta kan jummai bata yi ba haka ta wuce ta a kitchen ta shige d'akin ta,,
Suhaib na ganin ta bar wurin ya kissing miyau d'in ta yace" duk abunda zaki min i still love you Aysha koh da yanka naman jiki na zaki yi, uuuhhhmmm kin kusa ki shigo hannu na da zarar lokacin yayi dole ki cire tsana na a zuciyar ki ki rungume ni a matsayin masoyi ba *macuci* ba, yana gama fad'a yayi shigewar shi d'aki.
Nace" ooohhhh Suhaib soyayyar Aysha ya mai da kai ruwan k'ank'ara, da can baka daraja ta ba sai yanzu, hahahaaa kayi dai ka gama Shatu dai sai Ilu🤭🤭🤭 bari dai nayi shiru kar na ba ma mai karatu hint(satar amsa).
Yana isowa ya tarar da Suhail yana shan fruit salat d'in shi hankali kwance yana lumshe ido saboda tsabar dad'in abunda yake ci kamar yau ne ya fara testing a baki".
Samo wuri yayi ya zauna tare da ture try d'in a gaban shi yace" i need to talk to you bros", a hankali Suhail ya bud'e idon shi ya sauk'e a kan Suhail cike da takama yace" i'm all ears ba sai ka ture min abuna a gaba na ba kafin ka min magana ka gane koh?, yana gama maganar ya dawo da tray d'in a gaban shi, ya d'au spoon ya kai fruit salat d'in a haki yana tauna a hankali.
Sai da Suhaib ya gyara zaman shi da kau kana ya tattaro da hankalin shi grurin Suhail yana fuskantar shi yace" bros, idan har yanzu kana rik'e da alk'awarin da muka d'aukar ma juna in so ka hak'ura ka bar min Aysha ka koma ku sasanta da zee tunda tana matuk'ar k'aunar ka and ita ma d'in dangi ce".
Suhail bai san san da ya fuzar da abunda ke bakin shi a waje ba ya kama dariyar shekeyanci, sai da ya tsagaida ya dube Suhaib a shekeke yace" oohh ashe kana sane da alk'awarin da muka d'aukar ma juna kake neman rabani da murad'in rai na, why not ka koma ku sasanta da zee tunda Aysha ni take so ba kai ba?,
"Wait malam ba wai na fad'a hakan bane dan ka gaya min magana ba, ka gane koh?, maganar ka bata yi kama da ta masu hankali bane so idan ka shirya magana mai mutunci you can face me so bye for now, bai tsaya ya d'auki tray d'in ba ya fice daga parlourn ya nufi parlourn k'asa ya bar Suhaib da cizon yatsa.
Bayan kwana hud'u da faruwar hakan Sumayyah kullum cikin aiwatar da mugun nufin su suke ita da y'ar ta zee, yau ma kamar kullum ummi Sumayyah na zaune a kan kujerar three seaters yayin da zee ta filo da cinyar ta suna tattaunawa game da sharrin su, a cikin hirar ta su ce na jiyo zee tace" ummi na, yaushe zamu koma gurin mutumin nan ne ni fa i'm eager na ga na malleke Suhail fa tun kafin dad ya gano akwai abunda muke kullawa".
Murmushi ummi Sumayyah tayi tana shafo baza bazan suman kanta tace" daughter kenan har kina tunanin wannan sakaran yayan namu zai iya gano komai ?, ai kawai ki kwantar da hankalin ki mu bi komai a sannu kar garin gaggawa abban yarinyar ya gano mu".
Uhmmm uhmmm ni dai ayi sauri a had'a abunnan idan ba so kike ku kawo k'arshen numfashina a doron k'asan nan ba", ta fad'a tana turo baki.
Lallashin ta ummi Sumayyah ta hau yi da dad'ad'an kalamai tare da kissima mata wasu abubuwan, haka dai suke ta maganar su ita da y'ar ta.
B'angaren Aysha kuwa da wuri ta shirya ta shiga mota Suhail ya kaita makaran ta, suna gama parking ta fito tare lek'o tagar mota ta blowing ma Suhail kiss "muahhh" a iska tace" baby zan shige class kar a zane ni".
Owk durling me ki kular min da kan ki, ban yarda malaman ku su kalle min ke ba".
Zaro dara daran idanuwan ta tayi tace" ohhh babyn nan ka cika kishi da yawa, abun naka har da malamai na ma"?
ohhh haka ma zaki ce dan na fad'a gaskiya ?, ai malaman yanzu ba kamar ta da suke ba, akwai su da neman mata so ni dai ki kular min da kan ki".
Attention tayi ta buga mishi salut tace" yess sir, your wish is my command",, better ya fad'a yana jifan ta da shu'umin murmushin shi masu tsayawa a ran ta.
Hibb ne suka doso inda suke suka hau tafi suna cewa" sarakan soyayya ranar auren ku da kallo?, wannan shagwab'a haka Ash ai sai ki zauta yayan namu da yawa ya kasa kollon mata a waje ya mak'ale miki ke kad'ai gashi mu mata uku mike so mu aura", cewar hibb kenan tana fad'a a lokacin da suke doso su, kare maganar ta yayi dai dai da lokacin da suka iso wurin su,,
"ummmm kenan ai duk wacce ta shigo sai dai ta zame min mai shara saboda na riga da na rik'e akala sai yanda naga daman yi da abuna koh masoyi, ta k'are maganar tare da yi ma Suhail signal da ido".
Ummm ummmm baby ban da cika baki faaaa,, ya fad'a yana murmushi.
Aikam gara da ka fad'a mata kar wata ran kun yi aure muzo mu ga other half ta zama housemaid, suka saki dari su ukun ban da Aysha da tayi kicin kicin da fuska wai ita tayi fushi.
Yana ganin haka yace" enough please kar ku saka min mata a gaba ku tsoratata ta k'i ni tun kafin ahi auren, ya k'are maganar tare da fakan idon Aysha ya kanne musu ido d'aya.
Da sauri suka gimtse dariyar su, ita kuwa ta sakar mishi kukan shagwab'a tace" I know wayyo kake min aradu ina watching d'in ka ka ma su teehibb signal you have forgotten cewa Ashteehee kan su a had'e suke, duk abunda ya faru da d'ayan su suna taya ta fighting da iya karfin k'arfin su, ta juyo tana kallon su teehibb tace" ku kuma koh ?, if I catch you ehhhmmm, ta ja kwafa.
Tee zata yi magana ta ji phone d'in ta na ringig tarrrr tarrrrr tarrrrrr da sauri ta b'alle zip d'in jakar ta d'au wayan ta manna a kunne tace" hello yaya na", daga d'aya b'angaren aka amsa da cewa"na'am k'anwata kina class ne ?, na ji wurin kamar da hayaniya".
Cike da tsantsar begen shi ta dad'a manna wayar a kunnen ta tace" ka ganni nan a waje muna hira ne da Ash da yayan ta kuma wanda zata aura".
Girjin shi ne ya buga dammmm kamar ana bugun kalan gudu, a take ya ji zufa na wank'e mishi fuska, da murya mai kama da wanda yake cikin tashin hankali yace" what !!!, me kika ce k'anwata kunnuwana basu jiye min dai dai ba", kan ya gama rufe baki ta tare shi tace" cewa fa nayi muna tare da su Asha da wanda zata aura, hope lafiya dai koh naga kamar kana cikin tashin hankali ne".
Sassauta murya k'asa k'asa yayi ya hau kame kame yace" no , no, a'a babu komai dama ina son nazo na gan ki ne saboda nayi kewan ki dayawa.
Fad'ad'a fara'ar fuskan ta tayi tace" woow yayana har ka sa naji dad'i dama koh so nake na had'a ka da Ash ku gaisa tunda kun gaisa da hibb".
Owk toh yanzun nan ma kuwa zaki ganni, kittttttt ya k'ashe wayan.
Yana gama wayan yaji muyar mum tace" son lafiya kuwa na gan ka haka ?,
Murmushin dole ya k'irk'iro yace" k'alau mum so nake na duba k'anwata a makaranta, ba wani yarda da maganar shi tayi ba amma sai ta tsinci kan ta da farincikin maganar saboda yanda ta ga ya damu da gudan jinin ta, "owk toh, amma kuma sai naga ka had'a uban zufa, anya ba wani abu kake b'oye min ba kuwa Abdallah".
Haba mum ta yaya zan iya b'oye miki abu bayan abubuwan da kuka min ke da dad a gidan nan?, ai d'an halas baya manta alkhairi".
Dogon numfashi mumyn tee ta sauk'e tace" tohhh shikenan Abdallah bye sai ka dawo, idan ka dawo ka sanar da ni akwai maganar da dad d'in ku yace yana so ya muku game da alakar ku da daughter".
Ba tare da ya fahimci inda maganar tata ta dosa ba yace" toh mum", ya mik'e suka fice daga d'ankin tare tana dad'a jaddada mishi maganar da doctor ya fad'a kan maganar lafiyar shi, suna isowa bakin k'ofa suka rabu, Abdallah ya nufi parking space yayi ma motar shi key ya fice daga gidan da uban gudu.
B'angaren tee kuwa yana k'are wayan ta ciro wayan a kunnen ta tama mance da su Ashtee da kuma Suhail a wurin ta bama wayan hot kiss tana sakin murmushin, a fili ta furta" *I LUV YOU YAYA ABDALLAH NA, YOU OWNS MY HEART AND MY LIFE"*, ta fad'a manyan harufa.
Suhail kuwa tsare Aysha yayi da ido yana binta da kallon tuhumar da ita ta kad'ai ta san amsar shi, yayin da a zuciyan shi yake cewa" me had'in Aysha da yayan tee ?, bisa dukkan alamu akwai abunda wannan yayan tee yake nema a wurin Aysha idan ba haka ba me zai saka ya biye ma shirmen tee su gaisa da Aysha ?, bisa dukan alamu so yake ya ga Aysha ya gana da ita".
Aysha kam jikin ta ne ya mutu lakwassss saboda sunan *YA ABDALLAH* da ta jiyo a bakin tee, a take zuciyan ta ta fara tunano mata da yayan nata, garkuwan ta, kuma masoyin ta".Nace" *ALLAH* sarki Aysha ana kawo muku harri sosai a kan soyayyar ku, why not ki jarraba kiaure Ilu kawai koh zuciyan ki zai huta?.
*eedatou✍🏻*
~Y'ar mutanen Dengi~
YOU ARE READING
WAYE MACUCI
Historical FictionLabari ne a kan wata mak'auniyar Allah mai suna Aysha wacce take soyayya da yayan ta amma kwatsam sai wata tsautsayi ya afka mata har hakan ya saka ta cikin bakin ciki,ba tare da ta bayyana mishi ba sai daga baya ya fahimci halin da take ciki a tsan...