Page 16

764 53 0
                                    

🏵🏵☀☀🏵🏵☀☀🏵🏵
          *☀WAYE MACUCI☀*         
🏵🏵☀☀🏵🏵☀☀🏵🏵
        '''Suhaib koh Suhail'''
      
          
                       ©
'''Marubuciyar Rayuwar Sumayyah'''

    *SA'EEDA MUSA DAUDA😍*

'''Follow and ✅ote me on Wattpad''': *SaeedaMusaDauda*


*BESTORED TO MY LIL SIS* ''' SUMAYYAH MUSA DAUDA''' 

Not edited

       Managed fans nasan na keeping din ku waiting but ba laifi na bane rashin time ne ga uzuri sun min yawa

                        1⃣6⃣

"Ya Ilahi" ya Abdallah ya furta da k'arfi yana dad'a rik'ota da k'arfi lokaci guda ya mai da fuskan shi a kan Aysha yana ganin yanda take ta amai tamk'ar wacce zata amayo hanjin cikin ta, bugu da k'ari kuma yanda jini ke ta b'ulb'uwa a k'afan Aysha like a kwata haka yake gani,,
      Humayrah kuwa bata san sanda ta ture laidan awaran ba da sauri ta d'ora hannu a ka tayi kan Aysha da gudu hawaye na wanke mata fuska tace" wayyo ya Abdallah shikenan na kusa kashe aunty Aysha, duk nice sila da ban sayo awaran nan ba da hakan bata taso ba,,
      mai da fuskan shi yayi kan Humayrah da ta daddage take rusa kuka dan har ga Allah ta d'ora alhakin a kan ta ne kamar yanda ta fad'a.
      sai da Aysha ta gama amayo kaffff abincin da ke cikin ta kana ya Abdallah ya umurci Humayrah da ta samu mass ruwa ai kuwa da sauri ta nufi randar inna hankali a tashe ta d'ebo ruwan ta kawo mishi, d'ebo ruwan yayi a hannun shi tare da kauwa bakin Aysha alamar ta kuskure bakin shi,,
      jin alamar hannun shi a lib d'in ta ya sa ta bud'e baki a hankali dan ta gane abun da yake nufi gefe guda kuma hawayen radad'i ne ke ta tsiyayo mata, turo mata ruwan a baki yayi ba shiri ta fara kuskure bakin ta, sai da ta gama kana ya taimaka mata ta tashi tsaye, ya tsuguno gaban ta yana kallon yanayin kumburin kafan, zuwa yanzu zuciyan shi ta gama karaya sai sosai, wani tsiririn hawaye ne ya zubo mishi ba tare da ya sharo su ba cikin sarkewar murya yace" sannu k'anwa ta jin ji" ??
     d'ago mishi kai tayi alamar "eh", a sanyaye yace" Humayrah maza hanzar ta ki shiga d'akin auntyn taki ki d'auko mata abunda zata rufe jikin ta na kai ta chemist a duba k'afan, da kuma a bata maganin tsare amai wata k'ila zazzab'in cizon sauri ne ke damun ta,,
     kafin ya k'are maganar shi har ta fara tafiya tana cewa" toh yanzun nan ma kuwa ya Abdallah ai tare zamu dan hankali na ba zai tab'a kwanciya ba muddin ban bi ku ba, maganar ta yayi daidai da lokacin da ta kai bakin k'ofan Aysha ai kuwa sai ga ta ta d'awo hannun ta d'auke da wani madaidaicin jan hijabi wanda tsawon shi iya gwiwa,, 
      tana isowa ta taimaka mata ta zira mata ya Abdallah ya rik'o hannun ta yace" ooyyaa mu tafi k'anwata",,
     d'ago da k'afan ta tafi da niyar tafiya ai kuwa da sauri ta kwalla k'ara tace" wwaashh k'afa ta ciro ya Abdallah ban iyawa Aradu",,
       sausauta murya yayi yace" daure dai k'anwa ta idan muka fita k'ofar gida na samo mai adai daita ya kaimu kin ga ban da halin taimakon ki a yanzu",,
     da yake ta fahimci inda maganar shi ya dosa wato yana nufin ido gub'a ne, zai iya taimakon ta but ba wani ne zai fahimci da niyar taimako ya had'a jikin shi da nata ba, hankan kuwa ya kawo mata rasa k'ima da mutunci a idon mutane kowa yayi mata kallin ballagaza kamar yanda inna Larai take mata sharri dan dai ganin ta b'ata mata suna, cikin jarum ta ta d'aga k'afan ta tana  takawa a hankali tare da runtse idanuwan ta da duka firfito da su har Allah ya taimaka suka fito,,
     fitan su kenan suka tarar da mai adaidai ta ya sauke wasu mata guda uku yana k'ok'arin reverse ya fita daga unguwar da sauri ya Abdallah ya dakatar da shi a hannu ya tsaya,,
      har gaban su Aysha ya k'araso, Humayrah ce ta taimaka mata tayi mata jagora da mazaunin baya ita ma ta shiga,,
      shi kuwa ya Abdallah a gaba ya zauna gefen driver daga nan mai adaidai ta ya ta da abar shi sai zuwa chemist d'in da aka directing d'in shi,,
       suna isowa ya Abdallah ya biya shi kud'in Humayrah na rik'e da Aysha suka shiga chemist d'in, treating d'in k'afan aka mata sosai kana ya Abdallah ya saya maganin malaria suka koma gida.
     da isowan su suka tarar da inna Larai da wasu mata guda 8 akwatunan kaya ne birjik a gaban su, inna na ganin su Aysha ta rangad'a gud'a tace" yuririiii ga amaryar ma nan k'araso nan ki gaida dangin Ilu kar mutane suce ban miki tarbiya ba,,
     wani irin muguwar fad'uwar gaba ya ziyarci ya Abdallah ba tare da ya tabbatar da abunda kunnuwan shi suka jiye mishi ba yace"Inna bak'i muka yi ne ??
    uwar harara ta sakar mishi tace" rufe min baki ja'irin yaro kawai me ya kaika fita da wancan makauniyar tana nuno Aysha da hannu, koh ka manta na maka iyaka da ita ne toh ka sha kurumin ka nan da sati biyu masu zuwa baza ka ga Aysha a gidan nan ba dan aurar da ita ma Ilu zan yi koh kana so koh baka so,,
      mutuwar tsaye Aysha abubu da yawa sun tsaya mata a rai ga uban zogin da k'afar ta ke mata gashi wata sabuwar k'addarar da ta tunkaro ta, wasu sabbin hawaye ne suka sake bin fuskan ta,,
     bata san lokacin da kuka ya kwace mata ba fuskan ta na kallon inda kunnuwan ta suka jiye mata muryar inna Larai tace" ki min rai inna, ki tausaya ma lalura ta da maraicina ki janye wannan k'addararren auren da kike shirin min, duk da dai cewa ni nakasashiya ce amma saamm Ilu bai dace da ni ba, kasa k'arasa maganar tayi saboda wani sabon kuka da ya kwace mata, da sauri ta toshe bakin ta ta fashe da gunjin kuka mai tsuma zuciya mai sauraro,,
     duk da hakan bai saka inna tausayin ta ba sai ma cewa tayi" ki yi kukan jini ma matsalar ki ce ban da abun ki taimakon juna zaku yi ke da shi, yanzu idan ba Ilu ba wani asararren ne zai aje ki a gidan shi a matsayin mata,??
     haba inna ai zalinci ne wannan Aysha fa tana da y'anci a gidan nan da za'a matsa mata kan maganar Ilu, sanin kan ki ne cewa ba ke ce kike da daman aurar da Aysha ba matsayin ki a wurin ta shine kishiyar mahaifiya toh mai yasa ba zaka ki bar y'ar mutane a gidan uban ta ba ??, ya Abdallah ne ya furta hakan ba a cikin hayyacin shi ba,,
     mari inna ta sakar mishi tace" ni kake furta wa wad'annan munanan kalamai Abdallah kan ka d'aya kuwa ??, shin ka man ta ni mahaifiyar ka ce ??
    dafe kuncin shi yayi ya surawa mahaifiyar shi ido yana kallon yanda ta daddage ta tana masifa, ba tare da ya idda jin abubuwan da take fad'a ba ya sa kai yayi hanyar majalisa ran shi na k'una,,
    ganin haka Humayrah ta yi jagora ma Aysha zuwa d'akin ta,,
       d'aya daga cikin matan tace" ai ni da Ilu zai aure y'ata da kaka na ya yank'e saka dan zama zan yi na dangwali arzi ki son rai na,,
     murmushin takaici Aysha tayi dan ita kad'ai ta san mai yake bugun ta a zuci.

     Suhail kam tun komowan shi Jos bai da cikakken walwala kullum tunanin Aysha ce ke addaban shi dan har dad yaso ya gano shi but yayi iya k'ok'arin ganin cewa ya danne damuwan a ran shi kuma har zuwa yanzu bai fad'a ma kowannen su halin da ake ciki ba daga shi sai Sadeeq sannan kuma wacce tsautsayin ya faru da ita,,
      shirye shirye sosai su dad suka yi kamar yanda suka saba dan saura sati biyu ya rage zu kai ziyara ma d'an uwan su,,
      Suhaib ma ba'a bar shi a baya ba dan sosai yake shirin shi duk da dai cewa rabin hankalin shi na kan d'an uwan shi da gaba ki d'aya ya sauya mishi ya koma tamkar ba shine d'an uwa kuma abokin sirrin shi ba,,
     Zaune dad yake a  parlour shi da mum suna tattaunawa game da tafiyan da zasu yi, bayan sun gama maganar ne dad ya dubi mum so curious yace" uuummm mum d'in kids na tambaye ki mana , shin kin lura da changes d'in a gidan nan kuwa ??, i felt like something was going wrong, my Suhail was not like the one i knew before due to some changes that i considered "
      dogon numfashi mum ta sauk'e,  zuciyan ta babu dad'i tace" wallahi is all what i was thinking, I tried to find out the main source of the problem in other to know how to tackle it but i failed, have it been ma na san matsalar da it could not go far da mun samu hanyar warware ta but all i know shi ne matsalar came up from Suhail,,
     cike da damuwa dad yace"why didn't you tell me since da i could find solutions now,,
     ba naki fad'a maka bane bana so ka sanya damuwa ne a ran ka shi yasa wallahi babu yanda ban yi ba na gano main abunda ke faruwa but su biyun basu bani dama na karance su ba and kuma na tambaye su replied d'in su shi ne" babu komai mum, ta k'are maganar cike da damuwa kana ta dafe kuncin ta ta d'ora da cewa" huhhh i got tired of  all those things,,
    a sanyaye tsaye dad ya mik'e tsaye yana zagaye parlourn, can kuma ya zubo ma agogon bangon d'akin ido kamar mai nazari mum ta bin shi da kallo, sai da suka kai 5 minute a hakan sannan yace" go and call them all Maryam"
     jin sunan ta da ya k'ira kai tsaye ta san mijin nata yau babu sauk'i, babu musu ta mik'e a sanyaye ta yi hanyar part d'in su Suhaib da tunani kala kala a zuciyan ta,,




Pls share
       Comment
         Follow and vote on wattpad



*Sa'eeda✍🏻*
      ~Y'ar mutanen Dengi~

WAYE MACUCIWhere stories live. Discover now