Page 38

812 48 0
                                    

🏵🏵☀☀🏵🏵☀☀🏵🏵
          *☀WAYE MACUCI☀*         
🏵🏵☀☀🏵🏵☀☀🏵🏵
        '''Suhaib koh Suhail'''

***********************************

® *REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS P.M.L*💭💭💭

_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_

# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
      
          
                       ©
'''Marubuciyar Rayuwar Sumayyah'''

    *SA'EEDA MUSA DAUDA😍*

'''Follow and ✅ote me on Wattpad''': *eedatou*


*BESTORED TO MY LIL SIS* ''' SUMAYYAH MUSA DAUDA'''

       ~Afwan fans kun jini shiru kwana biyu i have an emergency call from my IT supervisor ne shi yasa tafiyar dole ta kama ni zuwa Bauchi yanzu haka i'm totally out of time i just squeezed to typed this pages saboda I know I kept most of you waiting dan haka na muku typing da yawa asha karatu lafiya, Sa'eedar ku ce.~

                       3⃣8⃣   

*Note edited*

       *Washe gari birthdayn granny* 
    
      Mum ce ta shigo d'akin Aysha da sallama a bakin ta yayin da hannun ta yake rik'e da bluen laida thick, shigowan ta ke da wuya ta wuce inner room d'in Aysha tana magana tana cewa" daughter daughter wai ina kika shigane yau throughout koh lek'o  waje baki yi ba gashi yau birthdayn granny ya kamata ace mum halarci wannan wuri dan yaya celebrating day d'in, maganar da ta fad'a yayi dai dai da lokacin da ta idda shigewa d'akin ta tarar da Aysha a zaune a kan gadon ta tana wasa da zoben hannun ta,,
    Kallo sosai mum ta bi yatsan hannun da shi it looks like irin rings d'in hannun kids d'in ta ne kamar zata yi magana sai kuma ta yaja baki tayi shiru ba tare da ta d'auke eyes d'in ta a kan zoben ba, tambayoyi ta d'inga yi a k'asan zuciyan ta tana cewa" were did this girl got this ring ? ohhh it should be Suhail that gave her saboda suna da strong relationship da shi, but if I could remember tun tahowar shi gidan nan bayan ya gama services ban kuma ganin ring d'in nan a hand d'in shi ba, but for how long zoben yake wurin Aysha,  shia may be ma is something different eyes d'ina yana bani wrong k'ila ba ring d'in da nake tunani bane.
   Bata idda tunanin ba ta jiyo muryar Aysha tana cewa" mum ai tun d'azu nake d'aki yau ina fama da mura ne gabaki d'aya ya hana ni tsakat ina ma tunanin anya kuwa za'ayi taron nan da ni kuwa ?
    Me zai hana daughter, birthday mama ta guda ace baza ki ba ? oohh no you have to go please dan already mun gama arranging d'in komai, tana kawo nan ta d'ora laidan a cinyar Aysha ta d'ora da cewa" ga kaya nan dad d'in ku  ya taho muku da shi, wannan naki ne na kai ma brothers d'in ki so bari na hanzarta na had'a miki ruwan wanka yanzun nan ki shirya  da tare zamu.
    Duk da ran ta bai so ba amma babu yanda ta iya dole ta taso suka shige band'aki mum ta had'a mata ruwan wank'a a birthtub kana ta ja mata k'ofan tayi shigewar ta kitchen ta k'irawo Jummai ta je d'akin Aysha ta taimaka mata ta taya ta shiri.
   Bayan fitowan mum daga d'akin Aysha before Jummai ta shigo Suhaib ya shigo d'akin Aysha da sand'a, jin motsin saukowan ruwa ne yasa shi gane cewa Aysha na birthroom, murmushin mugunta naga yayi ya d'auko laidan kayan da mum ta shigo d'akin Aysha da sauri ya b'oye a cikin rigar shi ya fice daga d'akin, yana isowa palour zai haura site d'in su kenan mum ta fito daga kitchen ta hango shi sauri yana taka matalalar benen da zai sada mutum da site d'in su ta kwalla mai k'ira tace" son",,
    duburburcewa yayi sosai da ya jiyo muryar mum, tsayawa yayi caakkk a wuri d'aya tare da juyowa da baya yayin da eyes d'in shi suka firfito suna bayyana alamar rashin gaskiya,,
     nufar wurin shi mum tayi tana cewa" saurin me kake ta yi haka sai kace wanda zai bar gidan gaba d'aya, so kake garin sauri k'afafuwan ka su gurd'e ka fad'i ?
    no mum ba haka bane kawai dai...., sai ya ja ya tsaya.
     Kawai dai me? you needs to be careful a kan hawa benen nan da muddin kaci gaba da irin wannan sauri haka tsautsayi zai iya afka maka so be careful and take this as a sign of warning given to you kana juna koh ?,
     Yeah mum thanks zan kula insha Allah, yana gama fad'a ya juyo da niyar barin wurin mum ta taro shi tace" wait, why are you in a hurry tun ban gama magana da kai ba you are about to go ?
     Kamar zai fasa ihu haka ya juyo zuciyan shi cike da fargaban kar asirin shi ya tonu dan idan mum ta gano kuddirin shi ya banu,,
     dak'ewa yayi yace" so sorry i taught kin gama ne dan sauri nake na shirya kin san this is a special day for both of us dan haka yakama mu looking so special yau".
     Ba tare da ta gano irin k'aryar da ya sharara mata ba tayi smile tace" owk shikenan maza kake ka shirya sama abunda nake son fad'a kenan cuz na san twice d'ina da African time, you guys too much like it. 
      Maida mata martanin murmushin yayi ya juyo tare da cigaba da tafiya ta bi bayan shi da kallo lokaci guda ta saki murmushi tana girgiza  head d'in ta ta koma kitchen dan dama abunda ya fito da ita kenan.
      Yana isowa cikin d'akin ya fiddo da kayan d'aya bayan d'aya yana dubawa, doguwar riga ce ash colour mai adon duwatsu a jiki, sai kuma golden takalmi wand baza a iya k'ira da flat koh hill ba wanda dai bazai ba ma mace marar ido wahalar tafiya ba with golden colour purse sannan kuma sai head da net duka ash colour,,
     ba k'aramin kyau da d'aukan hankali kayan suka yi ba idan nace zan tsaya na fad'a ma mai karatu  irin tsaruwar kayan ma b'ata lokaci ne dan sai na shafe kusan rabin littafi ba tare da na idda ba.
    K'arar foot steps Suhaib ya jiyo yana dosan site d'in su da sauri ya maida kayan a laida ya rufe, Suhail ne ya shigo yake  sauri dan tun d'azu yake so ya fad'a birthroom yayi wanka but ya tsaya decorations ne ya hana shi shirin da tuni yayi,,
    kallo d'aya yayi ma Suhaib ya d'auke kan shi daga gare shi ba tare da ya tanka mishi ba ya fara rage kayan jikin shi, shi kuwa Suhaib dan neman fitina tsaki ya ja ma Suhail yace" aikin banza mutum dai ya gama duk iskanci ya aure fanko, k'aruwa mai raba ma mutanen unguwa jikin ta, kaiiii hmmmmm ba dan kar nayi wata mummunar magana ba da sai nace wannan makauniyar da jaraba take ban da jaraba ta mata yawa ta rasa wanda zata bashi kan ta ya d'irka mata ciki sai kuturu ? tabbbb Allah ya tsare ni shiga gonar da kuturu ya amfana da abubuwan cikin ta mtwwwww, ya k'are maganar tare da jan tsuka mai k'arfi.
    Maganar da Suhaib ya fad'a sosai ya dake zuciyan Suhaib saboda sannin kan shi da shi yake yi, tunanin yarinyar da ya cuta ne ya fad'o mishi a rai saboda bai san koh a wani hali take ciki ba, koh ita ma tana fuskantar matsala similar to that of Aysha ? Allahu a'alamun.
     Shin wani hali ta shiga a tsanadiyar fad'en da ya mata, babban abunda ya fad'o mishi a rai shine da take cewa" kat kayi garkuwa da lalurata ka cutar da rayuwa ta, shin wata lalura ce gare ta?
     Ooohhh Allah forgive my sins ka sada ni da yarinyar na nemi yafiyar ta, idan rayuwar ta na cikin kunci ne ya Allah ka fidda ta daga cikin k'uncin rayuwa, ya Rabbi,  you known better than me cewa i was deceived by a bad friend, he uses alkaholic drink to give me which i wasn't aware that he put something that will drow my mind away, if not because of this i couldn't raped the innocent handicap girl,,
        uncontrollable hawaye ne suka fara sauk'o mishi from no way ba tare da ya wiping d'in su ba ya juyo ya kalle Suhaib a wulak'ance rai na mishi tsuya yace" no one knows what Allah destined to him,no matter what it might be one can change it, ina so ka sani duk abubuwan da kake fad'a baza su tab'a iya cire son Aysha a zuciya na ba, shawara d'aya zan iya baka shine ka addana munanan kalaman da kake sukin Aysha da su a gefe domin baza su yi tasiri a zuciyan Suhail ba, if you are jealous about my relationship with her ka fito fili ka ga min or else ka joining queue na maneman ta a san da zaman ka ya fi ace ka dinga beating around the bush.
      Dama ance idan ka fad'a magana mai zafi baka san amsar da zata biyo baya ba, tabbas hakan take dan maganar da Suhail ya yab'a ma Suhaib ya bala'in k'ona mishi rai but dan k'ar ya bada wata k'ofa da zata nuna alamar ran shi a b'ace yake yayi saurin sakin murmushin dole, ya mik'e tsaye ya taho wurin da Suhail yake tsaye ya tsaya a gaban shi tare da folding arms suka zuba ma juna ido na tsawon minti uku kana ya sauk'e hannayen shi ya soma zagaye Suhail yana magana cikin tak'ama time to time yana dafa shoulder d'in Suhail yana cewa" oohhh no God forbid na had'a tsahu da kuturu ai sai ku so hold your words.
    Tsayawa da maganar yayi for some minutes kana ya d'ora da cewa" infact da kake ce na joining queue ka ga na maka kama da wanda zai yi soyayya da karuwa, tantiri never it can't happen and....
      A tsawace Suhail ya dak'a mishi tsawa ba tare da ya bari ya k'are maganar ba yace" enough please i'm tired of hearing this from you wai yaushe ne zaka daina jifan Aysha da munanan kalamai ne idan kana da blood sister mistakenly tsautsayi ya fad'a kanta and u heard someone blackmailing her yaya zaka ji ? mtswww, yayi shigewar shi ban d'aki ba tsabar yanda ran shi yake a b'ace bai tsaya ya k'are cire kayan jikin shi ba haka ya fad'a bathroom yana huciiii. 
     Shigan Suhail band'aki ke da wuya Suhaib ya d'auko laidan kayan nan ya kuma bud'ewa koh mai yake yi ohooo ban samu na gani ba cuz jikin shi ya covering side view d'ina, nayi nayi na d'auko muku rohoto amma koh kad'an ban samu daman yi ba illah hango inuwar shi da nayi daga nesa koh me yake yi ohoooo.
     Sai da ya gama abunda yake yi kana ya maida kayan cikin laidan yana murmushin mugunta ya fice daga d'akin ya d'au hanyar d'akin Aysha.
     Isowan shi ke da wuya ya bud'e k'ofan ya shigo tare da maidawa a hankali rufe, a palour ya tarar da Jummai, magana yayi mata murya k'asa k'asa ta inda babu mai jiyo ta sai shi kad'ai yace" please Jummai had'o min Coffey ki kai min site d'in mu, not less than 20 minutes na baki so ki yi sauri ki gama dan so nake na sha kafin mu tafi wurin birthday d'in nan".
    Tun kafin ya kai ayya Jummai tace"toh yallab'oi an gama yanzun nan ma kuwa zan had'a ma, tana maganar tana nufar k'ofan fita daga palourn.
    Sai da ya bari ta fice kana ya shige  inner room d'in Aysha tarar da ita yake tana a zaune a gaban dressing mirror tana shafa mai,,
     tsayawa yayi cakkkk a wuri d'aya yana bin santala santalan cinyoyin ta da kallo wanda towel bai gama rufewa ba, tsigar jikin shi ne ya tashi yarrrrr a take yaji wata irin muguwar kasala da sha'awar ta ta addabe shi lokaci guda k'afafuwan shi na neman k'asa d'aukan shi.
    Miyau ya had'iye mai d'aci k'uuuuttt jikin shi har suma yake tsabar sha'awar ta, da kyar ya iya controlling sha'awar shi ya maida kayan inda ya d'auko su yana d'aga k'afa da k'ar har ya fice daga d'akin ita kuwa uwar d'aki na bata san ma yana yi ba.
      A hanyar shi ta zuwa main parlour ya tarar da Jummai ta fito daga kitchen hannun ta d'auke da tray da madaidaicin jok an zubo coffeyn a ciki,,
       yallab'oi na gama had'a ma yanzu nake shiri na kai maka d'akin ku na fito kenan muka had'e da kai a nan ".
    Gabaki d'aya ya manta da cewa ya ba ma Jummai aikin coffey saboda abunda ya gani a d'akin Aysha da driving d'in shi crazy, karb'ar tray d'in a hannun ta yayi yana cewa" owk owk kawo ma kawai zan kai da kaina", yana k'arba ya haura saman bene sai site d'in su.
    K'arfe hud'u da rabi yayi dai dai da lokacin da su mum suka gama shiri suka fito suka shige cikin mota suna ta zuba uban k'amshi,,
     Da yake ba wani nisa bane da wurin, motoci biyu suka d'auka mota ta farko na hango Suhail a gaban mota yana driving jikin shi sanye da wata farar shirt da farar wando yayin da k'afan shi ke sanye da black canvass, dad na daga gefe shima sanye da black suit ya k'ame a gaban mota da ka gan shi ka san cewa naira na tare sa shi.
      A back seat kuwa Aysha ce da Jummai a zaune suna tab'a hira sama sama Jummai na bata labarin iri kyaun sabbin gina ginan da ta gani a hanya, ba laifi itama Jummai ta had'u ba laifi idan ba za ka tab'a d'auka servant bace saboda irin had'uwar da tayi.
    A d'aya matar kuwa Suhaib na hango sanye da kaya irin ta Suhaib komai iri d'aya babu wata banbanci, driving yake shima mum na zaune a gefen shi taci adon maron d'in kaya ka wani uban net shima maron takalmin ta kuwa white ta sanya with wite purse, yayin da da granny ke zaune a back sit  tana sanye da koriyar riga da sani mai adon duwatsu sai wani vail mai girmata rube jikin ta da shi, yayin da 
     ma k'aramin kyau su duka suka yi ba na tak'aita muku tsaya fad'an kyau da had'uwar kayan b'ata lokaci ne dan duk abunda ka kalla a jikin su tamk'ar da dala aka d'in ka. 
    Tun a hanya Aysha ta ji kamar wani abu ya mitsine ta zabora tayi saboda unexpected mitsinin yazo mata da sauri ta sa hannu tana tsotsawa can ya tsaya haka dai ta d'inga yi ita kad'an ta yayin da fuskan ta ya cicciko da hawaye,,
    ashe duk abubuwan da take yi idanuwan Suhail na kan ta yana kallon ta ta mirror  ya so ya mata magana but ganin dad na wurin yasa shi yin shiru har suka iso.
     Isowan su ke da wuya suka bud'e murafen k'ofa suka firfito kai tsaye suka nufi cikin hole d'in hannun Jummai rik'e da na Aysha.
     tun daga nesa suka hango dandazon mutane mak'il a wani babba hole da only classic mutane ne suke iya kama hole d'in talaka ba sai iya kamawa ba, duk wanda ka kalla a wurin zaka hango farin ciki ne tsantsa a zuciyan shi, kallo d'aya zaka ma mutanen da ke wurin ka gano cewa kud'i ya zauna sosai dan duk wana ka kalla cikin su kayan da ya sanya is not less than 500k kowa cika yake yi yana batsewa irin basa son raini.
     Su mum suna isowa mc ya sanar da zuwan su tuni aka sake wakar bithday party mutane suka hau sowa suna tafi saboda yanda abun ya kayatar da jama'a har su mum suka k'araso tsakiyan hole d'in suka rounding cake d'in da aka tanadar a wurin kana mc ya dakatar da mutane daga sowa da tafin da suke yi, sai da komai ya lafa kana ya welcoming celebrant ya d'an yi jawabi kad'an kana ya bada umurni da a yanka cake.
    Su duka suka d'ora hannu a kan cake zasu yanka yayin da phone d'in dad yayi ringing hakan ya dakatar da su daga abunda suke yi suka tsaya jiran shi.
     Dad na barin wurin Aysha ta ji wani uban k'aik'ayi a bayan ta da k'arfi ta buga ihun da ya jawo hankalin dukkan jama'ar da ke wurin suka juyo suna kallon ta, mum,  Suhail da su granny kuwa rasa abun yi suka yi da sauri suka sake nife d'in cake d'in da ke hannun su a rud'e suka yi kan Aysha,,
    ita kuwa babu abunda take yi sai ihu ta tsotsa nan ta tsotsa can, ganin tana neman gwab'e kayan jikin ta da sauri Suhail ya rik'o hannun ta zai d'aga ta sama mistakenly hannun shi ya ja net d'in ta ya yaye hakan ya bayyana shattin iron ajikin kayan da ya d'aya k'ona rigar har ya bayyana gadon bayan ta da site d'in cikin ta ta hammatar ta a waje dan har ana ganin bra d'in ta, so disgraceful da yawa mutanen wurin suka manta da ihun k'aik'ayin da take yi suka tuntsure da dariya suna nuno ta yayin da wasu suka fiddo da waya suna k'ok'arin d'aukawa a tsatus da sauri Suhail ya rufa mata jiki da net ya d'auke ta caaak yana ruwan hawaye yayi hanyar fita daga hole su mum suka rufa mishi baya, Suhaib kuwa tsabar cin dariya har yana fidda kwalla.
    B'angaren dad kuwa yana barin wurin gefe samo ta wurin da ba hayaniya da yawa ya ciro phone d'in a aljihun wandon shi, sunan wanda ya gani a kan screen ne yasa shi saurin d'agawa yace" hello Officer Ja'afar".
     Daga d'ayan b'angaren Officer Ja'afar yace" yess Alhaji Kabir yaya family ?
       Alhamdulillah Officer kowa k'alau, dad ya maida mishi amsa, sai da suka gama gaisawa kana Officer yace" i just called to tell you that mun yi nasarar gano suspect d'in kuma.......
      Bai idda maganar ba dad ya taro shi da sauri yace" what officer, fad'a min wanene shi wanene uban shi a fad'in garin nan ? me yake takama da shi da har zai nema b'ata ma family na suna ?, yana kawo nan yayi shiru yana sauraran Officer Ja'afar domin yaji ta bakin shi.
     Dogon numfashi  Officer Ja'afar ya sauk'e kana ya fara mana yana cewa" i'm sorry to say the suspect is among your family, mun yi dogon bincike mum gano cewa d'aya daga cikin tagwayen ka n........., kittttttt wayar ta katse.
     Wani irin gumi ne ya fara bin fuskan dad, a cikin k'ank'anin lokaci sai da ya jik'e tafffffff da zufa, a fusace ya koma hole zuciyan shi sai turirin bak'in ciki da kuwa tsabar tashin hankalin jin cewa d'aya daga cikin y'ay'an shi ne ya aikata laifin.   
        K'araffffff suka had'e had'e da dad a hanya.


Please share

*eedatou✍🏻*
    ~Y'ar mutanen Dengi~

WAYE MACUCIWhere stories live. Discover now