🏵🏵☀☀🏵🏵☀☀🏵🏵
*☀WAYE MACUCI☀*
🏵🏵☀☀🏵🏵☀☀🏵🏵
'''Suhaib koh Suhail'''***********************************
® *REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS P.M.L*💭💭💭
_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_
# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
©
'''Marubuciyar Rayuwar Sumayyah'''*SA'EEDA MUSA DAUDA😍*
'''Follow and ✅ote me on Wattpad''': *eedatou*
*BESTORED TO MY LIL SIS* ''' SUMAYYAH MUSA DAUDA'''
4⃣3⃣
yana kawo nan ya gyara kwanciya yace" baby na naji kin ce y'anci shine abu na farko da kike so ki fara d'ora idon ki a kai bayan eyes d'in ki sun bud'e it makes me confused dan na san y'anci ba abu bane da ake gani da ido please me kike nufi da abunda kika fad'a ?, kuma wani muhimmanci ne yake da shi a rayuwar ki har zaki zab'i ganin shi kai na".
Bata yi wani mamakin jin abunda ya fito daga bakin shi ba dan ta san dole ayi hakan, cije libs d'in ta tayi cikin dakiyar zuciya tace" tabasss na san dole tambayar nan ta fito daga bakin ka kasancewar na zab'i na fara d'ora ido na a kan shi fiye da masoyina kuma burin zuciya ta",,
"yaya na", ta fad'a a sanyaye, "uuummm" k'anwa ta ina sauraren ki, ya amsa mata yayin da yake ji a zuciyan shi tamk'ar an sa mishi dafi.
Shiru ta yi mishi dan ta rasa abunda zata fad'a mishi abun da ya faru tsakanin ta da macucin da ta tsinci zoben shi bayan ya k'eta mata haddi, a kullu yaumin bata da wani buri da ya wuce ta bud'e ido ta ga kalan zoben da ke sanye a hannun ta dan dole sai da taimakon zuben zata iya gano macucin though dai bata da tabbacin gano shi but mai nema baya fidda tsammanin samu.
"Hello !!! hello !!! baby na kina ji na kuwa, ya fad'a tare da gyara ma wayan zaman a kunnen shi"
"ummm yaya na ina jin ka",
Jefo mata tambaya ya kuma yi yace" ke nake sauraro baby na, me kike nufi da k'almar nan da kika fad'a ta y'anci".
wani irin miyau ta had'iye mai d'aci da ta tsinkayo maganar shi kana tace" afwan yaya na ban san irin k'almar da zan yi amfani da ita na bayyana maka ma'anar abun da nake nufi ba, amma kamar yanda na fad'a maka y'anci abu ne na farko da nake so na fara gani, na san cewa dole ka yi mamakin abunda na fad'a, amma idan na gano *macucin* na san kai ma baza ka bar shi ba".
Rasa gane inda maganar ta ya dosa yayi cike da mamaki da kuma neman k'arin bayani yace" *waye macucin* da kika nema har kika k'asa gano shi ?, kin sanya zuciya ta a cikin rud'ani please ki fito fili ki min magana ta yanda zan gane cuz tsakani na da ke babu wani b'oye b'oye dan ni mai taya ki nemo shi ne a duk inda yake sannan kuma wani irin hukunci kika tanadar mishi a duk sanda kika gano shi".
Tambayar ta shi ce ta zo mata a bazata, instead of ta amsa mishi sai ta hau murza zoben da ke sanye a hannun ta tare da gyara kwanciyan ta lokaci guda ta sauk'e sassanyar ajiyan zuciya tace" kafin na amsa maka tambayan ka ina so ka fad'a min a tunanin ka wani irin hukunci kake ganin na tanadar ma yaya na kuma *macucin* da ya kai ni gidan karuwai da sunan b'atan ci ? kana ganin zan iya kyale macucin ba tare da na d'and'ana mishi azab'a dai dai da laifin da ya aikata min koh dai zan gyale shi ne ya ci bulus?
Ban da amsar tambayan ki amma na sani a yanda zuciyan ki take cike da tsanar bros komai ma zai iya faruwa sannan duk irin hukuncin da kika d'auka a kan shi matuk'ar ba kisan kai kika yi ba zan iya ce ya c'anc'anci hakan saboda yanda nayi la'akari da irin girman laifin da ya aikata miki".
Dariya tayi mai cin rai na tsawon lokaci kana ta had'e ran ta kamar tana gaban shi lokaci guda hawaye na wanke mata fuska tace" ka ga yanda nake jin tsanar yaya Suhaib a raina to wallahi koh kwatankwacin yanda nake jin tsanar *macucin* bai kamo ba dan a handa nake jin tsanar shi wallahi koh kisan kai zan iya yi".
Gaban shi ne ya yanke ya fad'i but sai ya dake yace" subahanalillah daina fad'an haka kin san hukuncin wanda yayi kisan kai kuwa", ya k'are maganar tare da sauke dogon numfashi yayin da gaban shi ke tsananta fad'uwa.
"Hmmmm ka san wani irin laifi yayi min ? Wallahi da ka san lafin da ya aikata min na san kai da kan ka zaka taya ni d'aukan fansar budurci............, wayar ce ta katse a sakamakon rashin charji a phone d'in dad ita kuwa Aysha sai magana take yi tana bashi labarin macucin, tana yi tana kuka har ba tare da sanin katsewan wayan ba har barci b'arawo ya save ta.
Kafin ta kwanta sai da ta cire zoben hannun ta ta lalimo jakan kayan ta ta jefa zoben tare da lafewa kan gado.
B'angaren Suhail kuwa k'iran na katsewa ya bugo ya ji wayan a kashe, guntun tsaki ya ja dan ya so yaji k'arshen maganar ta da kuma labarin *macucin*, tsaki ya kuma ja tare da kallon inda d'anuwan shi ke kwance shane shane bisa ga dukkan alamu barcin wahala yake yi dan yana lura da shi a y'an kwanakin baya samun ishasshen barci, wani iyin tausayin shi ne ya kama Suhail na ganin irin yanda Aysha ta tsane shi uwa uba su mum da basa bashi fuskan da zai yi magana da su balle ya nema yafiyan su.
A haka dai barci b'arawo yayi awon gaba da shi tare da mafarkan yarinyar da ya raping d'in ta wai gata nan tana bin shi da wuka zata kashe shi.
A mak'are ya taso daga barci saboda rashin samun isasshen barci daren jiya, a gaggauce ya fad'a band'aki ya sakar ma kan shi shower yana tunanin maganganun da Aysha ta fad'a mishi a daren jiya dan sosai maganar ta tsaya mishi a rai.
Yana gamawa ya fito yana tsane ruwan jikin shi har ya gama ya shafe jikin shi da mai tare da fetsa turaruka daga nan kuma ya fice daga d'akin babu wata walwala a tattare da fuskan shi.
Yana saukowa main parlour daga nesa ya hange Suhaib a zaune a kan kujera ya hard'e k'afafufan shi yana karkad'awa a hankali yayin da ya d'ora idon shi a gaban Tv ya zubo ma Tv ido yana kallon dramar da ake yi.
Kallo d'aya Suhaib ya mishi ya d'auke kai tare da k'arasowa inda ya ke ya zauna a gefen shi ya mik'a hannu ya d'au remote d'in da ke bisa centre table tare da rage k'arar Tv,,
saurin d'auke eyes d'in shi yayi a kan Tv ya maida a kan d'an uwan nashi da sai yanzu ya san da shigowan shi lokaci guda yana sakin ajiyan zuciya yace* har ka taso daga barci ?
"Uuummm" i just woke up and even took my bath, Suhail ya fad'a a daidai lokacin da yake k'ok'arin gyara zaman shi.
Owk wooo i see, any ways tun d'azu nake zaune a nan ina jira ka taso daga barci muje gidan granny ka taya ni ba ta hak'uri ka san ita kad'ai ce zata iya tausasa zuciyar su dad su hak'ura daga fushin da suke yi da ni, Aysha kuma da kaina zan ta bata baki har ta hak'ura kuma ina da tabbacin insha Allah da sannu zata yafe min kurakurai na".
Hmmmmm aya bros i pety you gaskiya i don't thing yarinyar nan zata iya s'auko da wuri saboda maganganun da ta fad'a daren jiya, shia just give try, Suhail ya fad'a a k'asan zuciyan shi yayin da a fili yace" owk let's get going dama so nake na gaida ta".
Cike da kulawa Suhaib yace" but u have not eaten koh sai mun je gidan granny ne ka ci abinci a wurin ?"
maida mishi da martanin maganan Suhaib yayi yana magana lokaci guda ya mik'e tsaye yace" no need gaskiya ban jin zan iya cin wani abu saboda yanda nake ji like my heart is itching me".
Mik'ewa Suhaib yayi shima cikin muryar tausayi yace" take heart okay, a tare suka fice daga gidan park suka nufa suka shige cikin wata ash d'in mota suka fice daga gidan. Suhail ne ke driving yayin da Suhaib ke daga gefen shi sun yi shiru da su baka jin komai sai sautin k'ida da ke tashi a hankali,
a hanyar su ta zuwa gidan granny ne Suhail ya ga wani babban Shagon zobuna wanda duk fad'in garin Jos da wuya mutum ya samu babban shago kamar sa.
Killer smile Suhail ya sake kana ya nemo gefen hanya ya parking ba tare da ya ce ma bros d'in shi komai ba, Suhail ya d'ago da fuska da mamaki yana bin shi da kallon ta Suhail na ganin haka ya bud'e mota ya fito da sauri yace" give me some minutes please, yana gama fad'a bai tsaya ya jira abunda Suhaib zai fad'a ba yayi saurin barin wurin ya shige shagon Suhaib kuwa guntun tsaki ya ja lokaci guda yana duba watch d'in hannun shi tare da kwantar da kan shi akan seat na motar.
Yana shigowa cikin shagon direct kanta ya wuce inda ake biyan kud'i ya ciro phone d'in shi a aljihun shi tare da mika ma mai shagon wayan yace" you get this ?, mutum ya amsa yana duba sample d'in da aka nuna mishi.
Sai da ya gama dubawa kana ya girgiza kan shi yace" no sir dama d'aya ya rage kuma an saye ta but idan ba cikin gaggawa kake bukatan ta ba ending of this week sai a ma ordern ta".
Suhaib ya tab'e baki ya karb'a wayan daga hannun mutumin yace" ba matsala but are you sure za'a samo exactly irin wannan kuwa".
Eh toh banda tabbas but i have to check da yardar Allah za'a samu".
Exchanging contact suka yi daga nan kuma suka shaking hands Suhail ya fice tare da yi ma mutumin sallama yayi wurin da motar su take.
Da isowan shi ya tarar da har Suhaib ya gaji da jira ya fara barci, murmushi yayi tate da ba ma motar key sai gidan granny zuciyan shi falll farin ciki he is gonna solve half of his problem muddin yayi dace da abunda yake nema.
*Madina specialized hospital* shine asubitin da su dad suka kawo Aysha, hospital ne wanda yake da manyan kwararrun likitoci sannan kuma akwai kwararrun kayan aiki sosai a asubitin,,
bayan an sa ta a na'ura an duba matsalar da idon ta ke da shi nan suka ba su rana akan nan da three days su dawo a yi mata aiki,
ranar da aka basu na cika sai ga su dad sun dawo nan aka shiga da ita inda ake aikin ido likitoci makilll a kan ta kowa na bada tashi gudumar sai da suka share tsawon awanni uku currrrr a kan ta kafin suka gama, suna gama aikin suka saka mata cottons a eyes d'in ta aka rounding head d'in ta da bandage kowani doctor da abunda yake sakawa a ranshi game da aikin da suka yo.
Haka suka fito suna sharar zufa suka tunkaro su mum da tsoro ya gama kama zuciyoyin saboda. ganin yanda gabaki d'aya jikin doctors d'in yayi sanyi.
D'aya daga cikin doctors d'in ne yayi k'arfin hali yace" we are sorry sir.........Sorry for the errors
Pls share*eedatou*
~Y'ar mutanen Dengi~
YOU ARE READING
WAYE MACUCI
Historical FictionLabari ne a kan wata mak'auniyar Allah mai suna Aysha wacce take soyayya da yayan ta amma kwatsam sai wata tsautsayi ya afka mata har hakan ya saka ta cikin bakin ciki,ba tare da ta bayyana mishi ba sai daga baya ya fahimci halin da take ciki a tsan...