Page 21

726 56 0
                                    

🏵🏵☀☀🏵🏵☀☀🏵🏵
          *☀WAYE MACUCI☀*         
🏵🏵☀☀🏵🏵☀☀🏵🏵
        '''Suhaib koh Suhail'''

                       ©
'''Marubuciyar Rayuwar Sumayyah'''

    *SA'EEDA MUSA DAUDA😍*

'''Follow and ✅ote me on Wattpad''': *SaeedaMusaDauda*

*BESTORED TO MY LIL SIS* ''' SUMAYYAH MUSA DAUDA'''

     

                        2⃣1⃣

Ina waliyin ango da amarya, da sauri suka d'unguma cikin masallacin Ilu na cika yana batsewa kamar wani basarake har suka shigo cikin masallacin, bayan waliyin ango da na amarya sun fito aka fara gabatar da d'aurin aure ya Abdallah na gaba waje heart d'in shi na beating da sauri fattt fattt kamar zai fita.
      Ana k'ok'arin idda d'aurin auren ne dad ya shigo Suhaib da Suhail na bin shi a baya da sauri tun daga nesa yake magana dan ya dakatar da liman yana cewa" a matsayi na na waliyin amarya kuma yaya a wurin mahaifin amarya ban ammince da wannan auren ba",,
    gabaki d'aya hankalin kowa ya koma kan su kowa na bin su da kallon mamaki jin cewa dad yace shine waliyin amarya sannan kuma ga wanda mahaifin ta ya kawo a matsayin waliyin toh amaryar waliyai biyu gare ta ?? ,,
     Ilu ango ji yake kamar ya shak'o su dan haushi ta yaya ana d'aurin aure dad zai zo da wata magana ta da ban wai bai ammince da d'aurin auren ba bayan y'ar su ta gama raba jikin ta ma wasu a waje taimakon ta yayi niyan yi ??
     cike da tsananin mamaki liman ya dakata ya dube dad ya jefo mishi tambaya yace" malam lafiya kuwa zaka dakatar da mu me ke tafe da kai kuma menene dalilin da yasa ka dakatar da mu ??
     sai da su dad suka samo wuri suka zauna kana yayi gyaran murya ya dubi liman cike a nutse yace" shin an tab'a auren mace da ciki a jikin ta?? ,,
     Jama'a aka amsa da cewa" a'a kana dad yace" dalilin da yasa nayi wannan tambayar shine aure ya haramta ga mace da ciki muddin bata haihu ba, kuma wannan aure babu shi saboda ammaryar da ciki a jikin ta,,
     kallon mamaki liman ya bi dad da shi kana ya dubi abba yace" toh malam shin da gaske ne y'ar ka da ciki a jikin ta kake k'ok'arin yi mata aure ba tare da kun bi yanda addinin islama ta koyar mana da shi ba ??,
     Cike da kunya abba ya sauk'e fuskan shi k'asa yayi shiru ya k'asa furta komai, sai yanzu ya ga rashin dacewan d'anyen aikin da yake shirin aikata ma d'iyar shi, Ilu ne yayi k'arafff ya  k'arb'e zancen yace" eeehh Allah ya taimake ka liman da ciki a jikin ta kuma nine nan nayi mata dan haka a d'aura mana aure kawai tund na ammince na k'arb'i abun,,
     wata uwar harara Suhaib ya sak'ar ma Ilu rai a b'ace yace" dallah malam rufe ma mutane baki ana magana ta hankali kana kawo ma mutane maganar marasa hankali gaka a dunk'ule kamar wani tsohon munafuki ana magana kana wani sako baki toh baza a d'aura auren ba,,
      " dunk'ulallun hannun shi ya kai a hanci yana magana yana buga k'irji da nad'add'en hannun shi yace" eeeyyyeee yau da bala'i a nan ni zaka kalla kace dunk'ulalle dube ni da kauka gani ka gani d'an samari ba wani fina kayi ba eehheenn, kuma aure na da shatu na nan daram babu fashi idan ma bak'in ciki kake da kishi sai dai ka mutu dan ba mai raba ni da Shatu,,
      harar up and down Suhail yayi mishi ya tab'e taki a heart d'in shi yace" wannan kuturu anyi jarababbe wallahi koh da yake laifin yarinyar ce wakila tana son shi ne ta bashi kan ta ya d'ura mata ciki, Suhaib kam k'asa hakuri yayi ya maida mishi martani a tunzure yace" taabbb na rasa wanda zan yi kishi da shi sai kuturu ai wallahi anci baya dube ka fa sai kace wani biri ga wani uban takalmi ka dank'ara ma k'afan ka sai kace fulani zashi kiwo idan in an barka wai kayi kwalliyan angwaye abun bak'in ciki ma koh kunya babu a gaban iyayen yarinya kana cewa kai ma y'ar su ciki mtssswww" tirrrrrr da halin dabbobi.
     Maganar Suhaib ba k'aramin k'ona ma Ilu rai yayi ba a harzuke ya taso yana tangal tangal da k'afa yana cillawa cikin tafiyar su ta kutare yayi kan Suhaib wai zai  kai mishi bugu Liman yayi saurin dakatar da shi yace" kai Ilu ina kuma zaka koma ka zauna muyi magana ta fahimta ka san a masallaci kake bai kamata aji kuna sa'insa koh hayaniya ba kasancewar masallaci tsaftataccen wuri ne da aka kebe dan bautar ubangiji, dan haka bama son hayaniya a cikin nan idan baka zama toh kayi tafiyar ka,,
     rai a matuk'ar b'ace Ilu ya fara magana magana yana kai hannu hanci yace" ai da ka bari na bashi kashi wallahi da ya san ya tab'o maza angon Indo mai tagwayen suna,,
      Sai zuwa yanzu waliyin ango ya samu daman magana dan ba k'aramin mamaki yayi ba dan shi koh kad'an bai san cewa yarinyar na d'auke da ciki ba da yasan da hakan da bai d'ebo jiki ya zo masallacin a matsayin waliyin ango ba, "wannan abun kunya da jahilci da mai yayi kama, abunda kenan ya fad'a a zuciyan shi, a fili kuwa ya dak'a ma Ilu tsawa a kunyace yace" kai Ilu ba magana ake maka ba ka tsaya ma mutane k'erere a sama ??, ba dan Ilu ya so ba ya juyowa da baya ya koma wurin zaman shi mutane na bin shi da ido kamar wani sun ga sabon mahaukaci shi kuwa koh a jikin shi".
     sai da liman ya tabbatar da kowa ya natsa kafin yace" gaskiya bai dace ace. a matsayin mu na musulmai muna aiki da jahilci ba, abun da nake nufi da jahilci a nan shine bai dace muna take hakkin shari'ar musulunci dan b'oye ma duniya abun kunya ba shin idan ka b'oye ma mutane ka b'oye ma mahaliccin ka ne ??, sanin kan ku ne cewa ba'a aure idan mace na d'auke da ciki har sai ta haihu kana ta tsarkake jikin ta kafin tayi aure, saboda wannan dalilin mun fasa d'aurin auren idan da rabo a gaba sai mu bari idan yarinyar ta sauk'a lafiya sai a d'aura auren a gaba dan haka kowa ya watse, kai kuma Ilu kayi hak'uri ka jira zuwa gaba wannan hukunci ba mu muka tsara ba hukuncin Allah ne kuma duk wanda ya nemi ya taka hukuncin Allah Allah ba zai tab'a barin shi ba, dan haka ina dad'a baka hak'uri hakuri idan dai kana son yarinyar toh ka zuwa gaba,,
    Haba Ilu ya taso a haukace yana masifa yace" wallahi ban yarda ba aure dai sai an d'aura eehheenn babu ruwana da wani munafuki da ke shirin tarwatsa auren nan, babu wanda ya sake bi ta kan shi sai ma watsewa da aka dinga yi da d'add'aya da d'add'aya aka bar massalacin su dad suka fito suma aka bar Ilu shi kad'ai yana ta surfa masifa,,
     suna fitowa daga nesa suka hango ya Abdallah ya k'ifa kai da jikin bishiya yana rusa kuka dan daga inda suke suna iya jiyo sautin shesshekar kukanshi,,
     da sauri suka yi wurin shi a hankali a tashe, a rud'e dad ya janyo shi jikin shi yace" lafiya dai Abdallah kake kuka me ya faru ne mutuwa aka yi ne please tell me ",,
     ba tare da ya daina kukan ba ya dad'a shigewa jikin dad yayin da sautin kukan nashi na ke dad'a tashi at the same time numfashin shi na tashi sama sama kamar zai fita dad yasa hannun shi a bayan a bayan ya Abdallah yana bubbugawa a hankali da tsigar lallashi yace" calm down son explain to me ka daure ka fad'a min damuwar ka nayi alkawarin share maka hawayen ka,,
     d'ago da kai ya Abdallah yayi cikin muryar kuka yace" dad na rasa ta !!!, na rasa farin ciki na !!!, na rasata har abada dad,
     kallon shi dad yayi da alamar mamaki yace" wani irin farin ciki ka nema ka rasa Abdallah daure ka sanar da ni ka ji d'ana",,
     da murya mai kama da ta wanda yake stammering yana magana murya na sarkewa yace" Aysha ita ce jigon rayuwa ta,  nayi rashin da bazan tab'a samo kwatankwacin shi a rayuwa ta ba dan rashin ta garen tamk'ar an zare ruhi na aka bar min gangan jiki ne saboda muhimmancin ta da datajar ta gare ni,,
    Sai yanzu dad ya gano abunda yake nufi idan hasashen shi ya zamto gaskiya kenan Abdallah yana son Aysha ne, dogon ajiyar zuciya dad ya sauk'e kana yace" ka kwantar da hankalin ka son baka rasa ta ba kuma insha Allah idan ina  raye baza ka rasa ta ba har abada,,
    Saurin d'ago da kai yayi fuska shab'e shab'e da yawaye ba tare da ya gaskata kalaman dad ba yace" aikin gama ya riga ya gama dad an riga da an daura mata aure da wani, kalla ka gani dad yanda mutane suka zo shaida d'aurin auren yayi mishi nuni da mutanen da ke k'ok'arin barin wurin",,
    Cike da tausayin shi dad ya raba jikin shi da na ya Abdallah ba tare da yace komai ba yayi wurin motar su ya bud'e mishi back seat ya zauna yayi mishi nuni da ya zauna dan ya fahimci ba a hayyacin shi yake ba,, 
    umurni dad ya ba ma su Suhaib da su shige suma, kamar dama jira suke dan sun k'osa da tsayusan suka shige suka zauna a k'usa da ya, dad ma sit din baya ya zauna yayin da abba ya zauna a gaba driver ya tada car d'in sai gidan dad.
    Suna shigowa da sallama Aysha da ke cikin d'aki taji gaban ta ya fad'i rasss a zaton ta koh an d'aura ne take gumi ya fara k'aryo mata ga wani irin tuk'ukin bak'in da ya tok'are mata makogoro, lokaci guda hawaye masu d'ami suka shiga bin kumatun ta,,
     Inna kuwa na ganin su ba tare da ta lura da yanayin da suke ciki ta shiga rangad'a gud'a mutane na taya ta,,
     abba ne ya watso mata uwar harara da ya sa ta shan jinin jikin ta ya daka ma mutanen da ke wurin tsawa yace" koh waccen ku ta fita" ai kuwa jiki na kyarma suka watse,,
     bayan fitan mutanen ne dad ya aika Sumayyah ta taho da Aysha, da isowan ta d'akin Aysha ta tarar da ita sai aikin kuka take yi,,
    tausayin ta ne ya kama Sumayyah jiki a mace ta rik'o hannun ta alamar ta taso, duk da dai cewa Aysha bata gane koh wacece ba bata mutsa mata ba ta mik'e tsare Sumayyah tayi mata jagora ita koh tana bin ta abaya,,
      suna isowa Sumayyah ta nima mata wuri ta zauna kana ta jawo kujera ta zauna ita ma tare da maida hankalin ta kan babban yayan nasu,,
    rai a b'ace dad ya fara fad'a ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba yana cewa" ka bani kunya sosai Sa'eedu wai ace da girman ka kana abu kaman k'aramin yaron har kake shirin aikata d'anyen aiki ?? idan ma ciki ne da ita for God sake haka ya kamata ka yi ??,  ka d'auko yarinya kana had'a ta da kuturu wallahi da ban da alaka da kai babu koh kaffara zan rantse da Allah cewa ba kai ne mahaifin Aysha ba, saboda yan da kake shirin banzatar da rayuwar ta indan an barka wai gudun abun kunya kake yi kan ta aka fara yin ciki babu aure ??
      hak'uri abba ya fara ba ma dad yace" kayi hak'uri yaya na san nayi kuskure wallahi zuciya ce da sharrin shaid'an ya ingizani, Insha Allahu hakan baza ta kuma faruwa ba,,
     saurin dakatar da shi dad yayi yace" ban nema haka daga gare ka ba and ka sani sai na kwato ma Aysha y'ancin ta na maida ita macce wacce sai  mijin da ta zab'a ta aura, yana gama fad'a ya juyo yana kallon ya Abdallah yace" Abdullahi zan tafi da Aysha na samo mata rayuwa mai inganci nayi Alk'awarin mallaka maka Aysha zuwa gaba, ku taso mu tafi, ya fad'a tare da mik'ewa tsaye, inna kamar ta kwala ihu dan bak'in ciki haka take ji ,,
      Tun tahowan Aysha kan Suhaib na duke a k'asa bai d'ago ba sai da dad ya bada umurnin su taso kana ya d'ago kan shi, d'agowan da yayi kenan eyes d'in shi ya sauk'a akan Aysha bin ta yayi da kallo yana tunanin ina ya tab'a sanin fuskan nan lokaci guda yaji matsananciyar fad'uwar gaba ta kama shi..........


Pls Share
       Vote
        Comment and follow me on wattopad

*Sa'eeda ✍🏻*
      ~Y'ar mutanen Dengi~

WAYE MACUCIWhere stories live. Discover now