🏵🏵☀☀🏵🏵☀☀🏵🏵
*☀WAYE MACUCI☀*
🏵🏵☀☀🏵🏵☀☀🏵🏵
'''Suhaif koh Suhail'''
©
'''Marubuciyar Rayuwar Sumayyah'''*eedatou😍*
'''Follow and ✅ote me on Wattpad''': *eedatou*
6⃣1⃣
'''Kullu nafsin zaikatul maut''' Dukkan mai rai zai zam mamaci, Allah ka jikan ya Abdallah ka karb'i bakuntan shi Ameen. Mutuwar tsaye iyayen nasu maza suka yi koh wanne hawaye na saukowa a fuskan shi kallo d'aya zaka musu ka tabbatar da cewa hankulan nasu a matukar tashe suke, domin kuwa babu alamar jarumta a tattare da su. Mum da mommyn tee kuwa suka fashe da matsananciyar kuka dan kuwa sosai mutuwar ya Abdallah ya tsaya musu a rai, barin ma mommyn tee da a d'an k'ank'anin lokaci ta shak'u da shi tamk'ar d'an cikin da ta haifa haka take jin shi a ran ta.
Mutum mutumi Ash da tee suka komo a d'akin sun kasa koh da kwakkwaran motsi, they can't believe cewa wai yau gawar ya Abdallah ne a gaban su, wai a waye gari sai dai su ga gangar jikin shi a gaban su a matsayin matacce. What's a sudden death?
Yunkurin tab'o jikin ya Abdallah Ash take yi tana magana kamar wacce ta zauce bisa dukkan alamu ita kan ta bata san ma me yake fitowa a bakin ta ba, kallon su Abba tayi cike da tarin rad'ad'i a zuciyan ta tace" Abba yaya na bai mutu ba ta yaya zaku ce min ya mutu bayan ina feeling breath d'in shi? saurin d'auke kan ta tayi ta maida kan gawar ya Abdallah da ke gaban ta yayin da idanuwan ta suke yi mata gizo da cewar yana numfashi kana ta d'ora da cewa" dad koh kun makance ne? shin bakwa ganin yanda heart d'in shi ke beating ne, oohhhh nooooo yaya na fa bai mutu ba, zai kasance da ni a matsayin rayayye har zuwa sufan mu".
Suhail da ke tsaye a kusa da Sadeeq wanda su kansu abun ya d'aga musu hankali matuk'a dan koh kad'an ba wanda ya fidda tsammanin cewa ya Abdallah zai ci mutu a wannan gabar da kowa bai cire mai tsammanin zai ci gaba da rayuwa ba".
Har cikin ran shi yake jin maganar Aysha na bugun shi a zuci, ga zaton shi sai ji yayi hawaye na tsiyayo mishi a hankali a fuska shi, cikin dakiyar zuciya ya sharo su da tafukan hannun shi kana ya tako a hankali zuwa gaban Ash da zuwa yanzu kuka ya kwace mata. Dukawa kad'an yayi a gaban ta yana fuskantar ta, ya tallab'o hab'ar ta ido cikin ido yana kallon ta yayin da tsananin shauk'in ta da kuma tausayin ta ke dad'a ratsa duk wani b'argo na jikin shi.
Duk da dai cewa ba wani shak'uwa sosai suka yi da ya Abdallah ba but yana ji a ran shi like he is missing some part of him, cuz he is a kind of person da suke da dad'in mu'amalar rayuwa.
Tsayawa yayi a hakan for some minutes shi ba magana yayi ba and kuma ya k'asa mik'ewa daga tsugunen da yake aikin kallon Ash yayin da wasu zafafan hawayen ke bin fuskar shi, cikin tsarkewar murya yace"cry no more durling me, Abdallah is no more yayi tafiyar da har abada baza mu tab'a ganin shi ba, domin kuwa ya amsa k'iran mahalliccin shi.
Kan ya gama maganar tee ta fad'a karafffff a sume a k'asa abunda ya janyo hankulan mutanen wurin kenan ya koma kan ta, nan ne aka rufe gawar da wani farin kyalle, suka yi saurin zuwa gare ta aka d'auke ta cakkkkkk sai emergency domin ceto rayuwar ta.
cikin ikon Allah ba a d'au lokaci mai tsawo ba aka yi nasarar farfad'owan ta, a kai mata alurar barci domin. A lokacin ne Ashe itama ta fara fisge fisge tana jifa da duk wani abu da ta gani a gaban ta.
D'aki guda aka bata itama aka yi mata tata alurar saboda gudun kar ta samu matsala a kwakwalwar ta bayan y'an wasu gwaje gwaje da aka yi mata.
Daga nan aka d'au gawar mamacin zuwa gida don yi mishi sutura a kai shi gidan shi na gaskiya.B'angaren inna Larai bata san kalar wainar da ake toyawa ba, haka kurum taji gaban ta na tsananta fad'uwa, tayi iya juyin duniya ta gano silar faruwan hakan amma koh kad'an tunanin nata bai kawo mata kan gudan jinin nata ba.
Zaune take a a kan dakali ita kad'ai ta rafka uban tagumi kallo d'aya zaka mata ka gano cewa ta jima da lulawa a cikin kogin tunani, gefe kuwa buta ce a kusa da ita dan fitowan ta kenan daga band'aki ta zauna a kasalance a wurin kamar mai tsohon ciki.
Duk irin masifar inna Larai yau gabaki d'aya tayi laushi da ita da ka gan ta abun a tausaya mata, dan koh a cikin awanni k'alilan ta zafge ta rame like tayi shekara guda tana jinya. Gajiyan da tayi da zama a wurin ne yasa ta mik'ewa tsaye ta karkad'e zanin nata tare da gyara ma zanin d'aurin a kugun ta, ta d'au butar tayi hanyar d'akin ta da ita.
Har ta kai bak'in k'ofa ta jiyo da sauri a sakamakon sallamar da ta jiyo a bayan ta, abun mamaki tana jiyowa tayi ido hud'u da mutane suna shigowa da mutum an rufe jikin shi dafarar kyalle, dammmmm gaban ta ya buga, mall........m tafiya kayi ka barni"?, a tunanin ta cewa gawan abban Aysha ne, ai kuwa cakkkkk maganar ta makale mata a sakamakon ido hud'u da tayi da shi yana shigowa a bayan mutanen da suka riko gawan.
Cirko cirko kowa yayi yana kallon ta abban Aysha kuwa sai addu'a yakeyi a zuciyan shi yana Allah Allan kar ta gano gawar.
Duk da dai cewar inna bata san koh gawar na wanene ba haka kurum taji jikin ta ji jikin ta ya d'auki rawa, kiris ya rage ta fad'a a dumin ba k'aramin tsorata tayi ba,, daddyn tee na ganin haka yayi umurni da a wuce da gawan, a take suka cigaba da tafiya.
Ina na ganin suna neman wuce ta, ta yi saurin sakin butan fantsammmm a k'asa a haukace ta k'araso wurin su ba tare da jikin nata ya daina rawa ba, ba zato ba tsammani ta d'aga lullub'in da aka rufe gawar da shi karafffffff tayi ido hud'u da fuskan gudan jinin ta Abdallah.
Wani irin birkitaccen k'ara ta sake tare da saurin rufe gawar ta juyo da fuskan ta gefe cikin tsananin tashin hankalin da bata tab'a tsintar kan ta a ciki ba, yayin da a zuciyar ta sai cewa take "innalillahi wa'inna ilaihi raji'un". A hankali ta soma ja da baya ta kasa koh koh da kwakkwaran hawayr har illa lokacin bata d'auke idanuwan nata daga kan gawar ba.
Abba ne yayi saurin kamo ta yayi hanyar d'akin ta da ita kana ya fice daga d'akin ya tarar har su dad sun shige da gawar domin yi mishi sutura, aka bar iyaye mata nata yi ma mamacin addu'a.
Bayan fitowan abban Aysha daga d'akin da kamar minti biyu inna ta fito kamar wata zararriya sai cewa take" kun kashe min Abdallah koh? d'ana guda d'aya? tilon d'ana kenan na shiga uku ni Larai mutuwa me na miki kika raba ni da d'ana Abdall"........., kan ta k'arasa maganar mum tayi saurin toshe bakin ta tace" inna Allah ya fi mu bukatar Abdallah shi yasa ya d'auke abun shi, ki kasance mai tawassali da Allah ki rungumi k'addara addu'ar ki kad'ai yake bukata".
Suna cikin hakan ne aka fito da gawar domin kai shi makwancin shi nan ne fa hankalin inna Larai da sauran mutanen wurin yayi matuk'ar tashi, sai yanzu hawaye suka samu daman ambaliya a fuskan inna Larai, babu abinda take tunawa kamar yanda take ta shige da fice wurin ganin ta raba alakar Abdallah da Aysha duk da dai cewar sau tari ya sha gaya mata cewa bazai iya rayuwa babu ita ba.
A iya rayuwar ta bata tab'a jin tsantsar nadamar abunda ta aikata ba kamar yau duk da dai bata san abubuwan da suka faru ba dangane da rashin lafiyar ya Abdallah ba, amma ta d'ora alhakin akan ta.
Abunda ya fargar da ita shine ganin fa tabbas tabbas za'a fice da gawar ya Abdallah tana ji tana gani, tafiyar da har abada baza ta kuma ganin gangar jikin shi ba, baza ta kuma jin amon muryar shi ba, ita data gan shi sai a koh idan a mafarki, ai kuwa bata san sanda ta fashe da gunjin kuka bs tana riko makarar tana fad'in shikenan ka min nisa kenan Abdallah? dama bankwana ka zo yi min ba kazo zama da ni ban.........kasa k'arasar maganar tayi a sakamakon wani sabon kukan da yaci k'arfin ta.
Sosai zukatan mutanen wurin suka cika da tsantsar tausayin ta, da kyar su abba suka iya danne zuciyoyin su ba tare da sun kuma bi ta kan ta ba suka wuce da gawar zuwa mota daga nan suka wuce makabarta suka binne shi tare da yi mishi addu'ar samun rahawa kana suka barshi daga shi sai halin shi, suka fara zaman makoki.
A asubiti kuwa Alhamdulillah an samu an shawo kan matsalar Ash bayan anyi mata allurar barci mai nauyi ya d'auke ta tana farka sunan
ya Abdallah ta k'ira k'arfi Suhail da ya fito daga nashi d'akin yana tafiya jiri na d'iban shi dan k'arfin hali koh a jikin shi burin shi dai ya san wani hali sahibar tashi take ciki, cikin sa'a yayi dai dai da lokacin da ta kwalla ihu da sauri ya komo da baya ya nufi wurin doctors ya shaida musu halin da ake ciki.
Kamar had'in baki a tare suka bar ofishin suka shige d'akin Ayshar suka tarar tayi buzu buzu da suma tana bubuga hannun ta a jikin k'arfen gadon, tuni Suhail ya ji sabon k'arfi na zuwan mishi, kafin doctors d'in suyi wani yunkuri har ya rige su isowa wurin ta ya riko hannayen ta he is trying to stop her so thats she didn't hurt herself, amma abunda bai sani ba tuni jini ya fara zubowa a hannun nata.
Janta yake yana famar haki yace" me yasa kike neman illata kan ki, you know hakan ba shine zai dawo mana da shi ba, you have to accept this as a destiny, and you have to be strong", yana maganar ne yayin da yayi nasarar jawo ta jikin shi ta lafe a lafiyayyiyar kirjin shi, a hankali yake bubbuga bayan ta da sigar lallashi.
Sannu a hankali ta fara dawowa hayyacin ta nan ne Suhail ya ba ma doctors damar duba lafiyar ta, hakan koh ta kasance domin kuwa babu wata alamar lalura a tattare da ita illa tsananin firgici da take ciki.
B'angaren tee kuwa Alhamdulillah domin kuwa normal ta farka ta had'e kan ta da jikin sickbay tana rusar kukan babban rashin da tayi wato rashin yayan nata kuma masoyin ta. Sai da taci kukan ta mai isar ta kana ta saurara ta hakura da kukan ba dan ta so ba sai dai jin yanda zazzab'i ke neman rufe ta.Wasa wasa sai da su Ash suka d'auki tsawon sati d'aya a asubitin kana aka sallamo su suka koma gida, d'akin ta na da ta fara shiga babu abunda take tunanowa illah a lokutan baya da ya Abdallan ta yake shigowa d'akin ya d'ebe mata kewa, ya rage mata kuncin rayuwa, yau an waye gari babu shi.
A lokacin da lafiyayyun idanuwan nata suke mararin ganin wanda yayi d'awainiya da ita tun tana jaririyar ta, me yasa sai daffff da zai amshi k'iran mahallincin shi zai bayyana gare ta a matsayin Abdallan ta?.
Haka dai ta wuni jiguffffff a wurin ita kad'ai tak'i cin abinci ban da aikin kuka babu abunda take yi.
Tun daga lokacin Aysha ta fakaice ikon mutane ta shige d'aki tayi ta rusar kuka tun su abba basa ganewa har daga baya suka gane nan ne suka yanke shawarar su koma Jos kawai, muddin bata yi nisa da gidan ba dole ne rashin Abdallah ya kasance mata sabon miki a zuciyan ta.
Hakan koh aka yi suka shirya washe gari da sassafe suka d'auki hanyar Jos tare da su.
Tafiyar awa biyu da rabi zuwa uku sai gashi sun iso cikin garin Jos gari mai tarin albarka, daga nan dukkanin su suka d'auki hanyar gidajen su.
A gidan su dad kam suna shigowa cikin gida suka tarar da Suhaib a parlour ya zafge ya rame kamar mai cutar kanjamau cuz tun bayan barin shi Dengi ya kaurace ma cin abbinci, ba komai ya haifar da hakan ba illah tarin dana sani da nadamar biye ma su ummi Sumayyah da ya dinga yi, sai yamzu ya hango illar abinda ya aikata a baya.
Kallo d'aya biyu mum and dad suka mishi suka d'auke kawunan su, shi koh yana ganin su yayi sumi sumi da ido tare maida kan shi k'asa cike da tarin nadama da borin kunya, gabaki d'aya ya kasa d'aga ido ya kalle iyayen nashi, k'anin shi da kuma Aysha.
Tsinkayo muryar dad yayi yana cewa"
"Ba zan iya maka baki ka k'ara lalacewa ba Suhaib, Allah ya gani ni da mahaifiyar ku mun yi iya k'ok'arin mu mu ga mun d'ora ku akan turbar gaskiya amma kai ka bijire mana ka biye wa ummin ku yau wa gari ya waya?, yau gashi a sanadiyar ka munyi rashin Abdallah", yana gama fad'ar haka yayi umurni ma su mum su shige d'aki hakan koh aka yi suka bar Suhaib a zauna yana ta rusar kukan nadama.*eedatou✍🏻*
YOU ARE READING
WAYE MACUCI
Historical FictionLabari ne a kan wata mak'auniyar Allah mai suna Aysha wacce take soyayya da yayan ta amma kwatsam sai wata tsautsayi ya afka mata har hakan ya saka ta cikin bakin ciki,ba tare da ta bayyana mishi ba sai daga baya ya fahimci halin da take ciki a tsan...