Part 15

933 60 1
                                    

🏵🏵☀☀🏵🏵☀☀🏵🏵
*☀WAYE MACUCI☀*
🏵🏵☀☀🏵🏵☀☀🏵🏵
'''Suhaib koh Suhail'''

***********************************

® *REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS P.M.L*💭💭💭

_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_

# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035


©
'''Marubuciyar Rayuwar Sumayyah'''

*SA'EEDA MUSA DAUDA😍*

'''Follow and ✅ote me on Wattpad''': *SaeedaMusaDauda*


*BESTORED TO MY LIL SIS* ''' SUMAYYAH MUSA DAUDA'''

Afwan jiya na mistaken page num er 14 yakamata na rubuta sai na sa 15 shi yasa zaku ga na maimata page number, but na gyara a doc, ana mugun tare.


1⃣5⃣

shiru Abba yayi yana yab'a nutsuwa irin ta ya Abdallah bugu da k'ari kuma yaro ne mai matuk'ar biyayya, da ace yana da lafiyayyiyar y'a da ya mallaka mishi ita amma kuma makantan Aysha shi ya kawo mishi cikaaasss,,
ba tare da kuma cewa komai ba ya juyo da baya da niyar barin gidan, har yayi 4 steps yaji muryar ya Abdallah cikin inda inda yana cewa" uuummm uuummm Abba dama wata magana
na zo maka da ita ban san koh zaka amince ba,,
saurin juyowa Abba yayi zuciyan shi cike da tunani kala kala dan jin cewa ya Abdallah na son yin magana da shi ba tare da ya same shi a d'akin shi ba kamar yanda yake yi a lokutan baya,,
"Shin lafiya dai koh Abdallah ai da ka bari mun keb'e saboda ban san wace irin magana ka zo min da ita, Abba ya fad'a yayin da yake maida fuskan shi kan ya Abdullahi"
a kunyace ya sauk'e kan shi k'asa yana tsotsa keya sannan yace" lafiya lao sai alkairi Abba, yana fad'a yayi shiru tare da maida fuskan shi kan Aysha da zuwa yanzu ta gama tankad'en ta d'auko sandar ta tana k'ok'arin dogarawa a ta tafi d'aki,,
cuz daga inda yake tsugunen yana iya hango duk abubuwan da take yi, sai da ya bari ta shige d'aki kana ya maida eyes d'in shi a kan Abba da tun d'azu shi yake kallo yana jira ya ji abunda d'an nashi zai fad'a,,
a kunyace ya Abdallah ya kuma mai da kan shi k'asa kana ya d'ora da cewa" dama magana ce akan Aysha, ba tare da ya gama fad'a ba Abba yayi sauri ya tare shi yace" wata Aysha kuma ba dai ta gidan nan ba wani abun ne ya faru ??,,
ba tare da ya daina tsotsa keyan shi ba cike da kunya ya fara cewa" uuummm uuummm dama dama, yana fad'a yayi shiru a sakamakon rasa abun fad'a da yayi,,
jin muryar Abba ya kuma yi yana cewa" fad'a mana Abdallah idan ma rashin kunya ta yi maka yanzun nan na d'au hukunci, Abba ya fad'a cikin k'aguwa,,
ka kwantar da hankalin ka Abba babu raini tsakanina da Aysha koh kad'an illa tarin mutunci da kuma girmamani a matsayin yayan ta datake yi, amma zan so ace inna na k'usa dan itama maganar ta shafe ta".
toh toh toh shike nan bari na k'ira ta, Larai !!! Larai fito mana kina ina ne kam, cewar Abba kenan yayin da yake gyara zaman hular shi,,
tun daga cikin uwar d'aka ta amsa tace" ganinan tahowa mai gida wannan k'ira haka kamar mai shirin bani kyautan sulalla,,
girgiza kai Abba yayi a zuciyan shi yana cewa" Larai kenan kullum maganar ta bata wuce ta kud'i, tun da nake ban tab'a ganin mace mai jarabar son kud'i kamar ta ba,,
bai idda gama zancen zucin ba Larai ta fito tana turo baki tana hamutse fuska tana isowa kagan malam ta rik'e k'ugu tace" me ya faru mai gida da kake min irin wannan uban k'iran".
idan da sabo Abba ya saba da halin matar tashi, kallo ya jefo mata cike da takaici ya dubi ya Abdallah yace" toh bismillah yi magana tunda ga mahaifiyar ka nan ta taho,,
dad'e k'asa da kan shi yayi kana yace" Abba dama so nake a d'aura mana aure da Aysha dan mun riga da mun daidai ta tsakanin mu shine na tuntub'e ku da maganar domin muji daga bakin ku".
dafe k'irji inna tayi ta saki salati tare da doka uwar ashar kana tace" anya kuwa kan ka k'alau kuwa ??, da dai shaye shaye kake yi da sai nace garin shaye shayen naka ka samu matsala a kwakwalwar ka, ban da abun ka ma ina kai ina wannan nakasashiyar yarinyar ga mata birjikkkk a garin kamar gwanjo, ta d'ora hannun ta biyu a ka da k'arfi tace" ooohhh yau na shiga uku da jarabar d'a namiji"
maganar ta ba k'aramin k'ona ma Abba rai yayi ba jin yanda a gaban shi take kyamatan y'ar shi amma sai yayi ta maza ya dake,,
ya Abdallah kam hankalin shi ne yayi bala'in tashi da jin kalaman mahaifiyar shi, a zaton shi koh idan yayi maganar a gaban Abba zata danne tsanar da take ma Aysha a gaban mahaifin ta dan tun farko dabaran da yayi kenan ya k'ara mishi kwarin gwiwa akan soyayyar da yake mata sai kuma ya akasin haka wato babu kunya babu tsoron Allah balle kuma tausayin marainiyar Allah inna Larai ta takarkare tana ta ci mata fuska,,
gumi ne ya fara k'aryo mishi, cikin tashin hankali ya kwantar da murya yace" dan Allah inna ki taimaken Aysha ita ce cikon farin cikina, rayuwa ta bata da wata amfani matuk'ar babu Aysha a tare da ni",,
" a hasale inna tace" toh sannu romiyo da juliyet sarakan soyayyah" toh ka sani babu kai babu wannan shegiyar nakasasshiyar yarinyar nan kenan har abada ka dai ji na fad'a maka, koh da wasa kar ka sake ka sake tunkara ta da maganar ka dai ji na fad'a maka dan Aysha nayi mata miji kuma har na karb'a sadaki eeehhheeenn,
mutuwar tsaye Abba yayi dan jin k'arfin hali irin na inna Larai ganin yanda shi da y'ar shi take nema ta nuna mishi fin k'arfi, a zuciyan shi kuwa sai maimaita kalmar da take cewa" nayi ta ma Aysha miji kuma na k'arb'a sadakin ta" yake yi, kamar dama ita ce ke da right d'in aurar da Aysha bayan bata san wahalar ta ba, abun da ya k'ara b'ata mishi rai shine dan tsabar tsanan da take nuna ma Aysha wai Ilu zata aura mata wannan tambad'add'en yaro marar tarbiya ",,
bai k'ara cika da mamaki ba sai da ya ga inna Lari ta ja tsaki"mttssww " tayi shigewar ta d'aki tare da bank'e k'ofa cikin zafin nama dan sai da suka d'an tsorata cuz of unexpected k'aran da suka jiyo,,
tausayin ya Abdallahi ne ya bala'in kama Abba, a take ya hau mishi da hankali ta hanyar lallashin da kalamai masu kwantar da hankali kana daga baya ya bashi shawara a kan cewa ya bi umurnin mahaifiyar shi dan shi kan shi Abban wataran shakkar ta yake ji most especially idan ta fara ta da jijiyar wuya ,,
sai da hankalin ya Abdallah ya d'an kwanta kana Abba yayi ficewar shi shago rai a matuk'ar b'ace,,
Duk irin zage zagen da inna Larai ke yi ashe tamk'ar a kunnen Aysha take yi dan duk ta ji abubuwan da ta fad'a kaaafff,,
hawaye ne gabaki d'aya ya gama wanke mata fuska, motsin shigowan mutum taji tayi saurin share hawayen ta but abunda bata sani ba it was two late dan already ya gani before ta wiping,,
wani irin tausayin ta da kuma tsananin son ta ne yake tsirgar shi lokaci guda tamk'ar son ta zai fatso k'irjin shi, jiki a mace ya tsugunna a gaban ta suna shak'ar numfashin juna cike da tausayin ta da kuma kan shi ya bud'e baki murya na rawa yace" bana k'aunar ganin hawaye a fuskan ki k'anwa ta, cuz suna k'ona na min zuciya, ina da tabbacin cewa kin ji duk abubuwan da suke faruwa tsakanina da inna amma insha Allah muddin ina raye sai na mallake ki cuz jikina yana bani ke tawa ce, kuma duk rintsi ba zan daina k'aunar ki ba Aysha",,
hawayen da take k'ok'arin mak'alewa ne suka samu daman saukowa, ba tare da ta share su ba ta jiyo da fuskan ta inda kunnuwan ta ke jiyo mata muryar ya Abdallah tace" tun farko abunda nake guje ma ka da kuma kaina kenan tozarci, tabbas nakasassu irina na fuskantar rayuwa mai matsanancin wahala, me yasa lafiyayyu ke d'aukan duniya da fad'i har suke manta cewa ubangijin da yayi su shi yayi mu kuma babu bawan da yafi wani a wurin Allah face wanda ya fi wani k'arfin imani , dan haka mu da yayi mu nakasassu ba wai dan yana kin mu bane ya maida mu hakan illa dai hakan ya ga damu ya gan mu, shin a kwai ran da tafi k'arfin fad'awa kaddarar Allah ?? toh me yasa ake mai da mu abun kyama a cikin al'umma bayan duk matsayin mu guda ne ??, ta k'are maganar tare da rusa kuka mai cin rai cin rai,,
jikin ya Abdallah ya matuk'ar yin weak dan shima ba dan ya lalashe kan shi ba da tuni ya taya ta rusa kukan but ganin kukan nashi zai dad'a ingiza ta ne yasa yayi ta maza ya danne, ya matso hawayen bakin ciki zuciyan shi na mishi d'aci ya shiga bata baki da dad'ad'an kalamai masu sanyaya rai da kuma tunasar da bawa abunda ya manta dangane da abunda ta shafe kusanci da addini Islama yana cewa" bana so ki saka damu a ranki kanwa ta ina tare da ke da'iman duk da dai cewa har zuwa yanzu baki furta min cewa kina sona ba amma bazan tab'a bari a aurar da ke ga Ilu ba dan yin hakan tamk'ar kaskanci ne a gare ki dan kin fi k'arfin sa saaammm baku dace da shi ba, ina so daga yau ki sa a ranki cewa nakasa wata baiwa ce da Allah ne kad'ai yasan irin baiwar da tattare da shi, ita ido da kike gani tamkar bala'i ne ga duk bawan da bai amfana da ita ta hanyar da ta dace ba dan yana kusanto d'aya daga cikin abunda ke nisantar da bawa daga shiga aljanna sannan ya kusanto da bawa daga shiga jahannama, idan kin duba yawancin mutane suna sarrafa idanuwan su ta hanyar kallon batsa, luwad'i da kuma mad'igo most especially a zamanin nan namu sai kiga budurwa ta raba dare tana chatting d'in batsa da saurayin ta mai makun alokacin ya dace ki yi nafilar ki tare da kai kukan ki gaban Allah amma sai ki kwana kina aikata aikin da babu riba sai tarin nadama da sab'o a ciki , zaki ga sun tub'e zindir da su haihuwar uwar su suna turo ma junan su hoton private part din jikin su hankalin su kwance dan tsabar rashin tsoron da yayi musu karanci har ana dariya ana cewa" nice pick, wow baby kin had'u ashe dama haka kike/ kake ai da ba bar ka/ki da nayi sakaci,, "uuhhmm tabasss ta had'u but saura had'uwan ta da Allah ranar da rai yake zama tamkar hoto, ranar da zaka/ki girb'e dukkan sharrin da kika/ka shuka a duniya, ranar da babu yafiya tsakanin bayi, ranar da za'a sauk'o da azaba kowa na neman mafaka, shin me kika tanadar koh ka tanadar ma wannan rana ?? basa koh tunanin Allah yan iya zare ran su yayin da suke aika ta barna hankalin su kwance burin su su biya ma junan su bukatu na duniya, shin sun manta tamkar gyara gaba da kuma b'ata b'aya suka sun manta cewa akwai hisabi a tsakanin su gab'ob'in jikin su. '''Wa'iyazubillah Allah mun tuba ka tsarkake mana zukatan mu''' me yasa muke kusan to kan mu daga shiga wuta dan karancin imani ma a lokacin da sarkin sarakuna yake saukowa yana cewa a tashi a roke shi zai amsa mana bukatun mu amma ke kina can koh kana can kun daddage ku ga masu raya soyayya kin manta matsayin ki na uwa koh ka manta matsayin ka na uba wata ran, ka manta cewa idan ka b'ata yar wani za'a b'ata naka fiye da yanda kayi ma wata toh wai ma shin haka addini ya koyar mana a b'angaren soyayyah, koh dai kawai mu mun samu addinin ta hanyar sauk'i muke watsi da shi mu kama rayuwar yahudu, bayan mun san irin gwagwarmayan da Annabawa da sahabbai suka sha wajen kafa mana musulunci ?? toh wallahi duniya makaranta ce a ranar da ka shige ta a ranar ka fara darasi da ka barta kuma kayi jarabawar ta wanda babu mai tsallakewa sai mumini,,
"Hmmmm" wallahi Aysha ki dad'a gode ma Allah (SWA) da bakya d'aukar zunubai da idanuwan ki, baki tab'a ganin jikin wata ba balle Allah ya kama ki da laifin hakan,, Aysha baza ki tabbatar da cewa ido gub'a bane sai jinki labarin yanda mace take neman mace, namiji ya nemi namji wato lesbianism da homosexual dan yawan ci abunda ke addaban al'umma kenan, sun manta cewa al'arshin Allah suke girgizawa yayin yin wannan bad'ala kuma ubangiji Allah yana tsananin fushi da su, da lafin mai yin les koh homo wallahi gara laifin mai aikata zina so tari duk da cewar shi d'in ma Allah ya haramta mana yin shi dan hakan ne yace mu kasance masu tsare farjin yayin da sha'awa ta taso mana sannan ya halatta mana aure saboda gujewa fad'awa halaka, dan haka ki kwantar da hankalin ki lalura dai ta Allah ne sai yanda yaga daman yi da bawa sa kuma tsakanin Allah da bayan sa naka ido.
sosai nasihan shi yake ratsa mata zuciya har take jin zata iya jure duk wata jarabawar da ta tunkaro ta a gaba, sai da ya tabbatar da ya rage mata damuwa da ke ran ta kana ya bar ta yai mata sai da safe cuz ya fara jin kiraye kirayen sallar magrib, yana fita yayi alwala yai shigewar shi masallaci.
Bayan ya fita ne ta d'auko sandar ta ta hau dogara har ta fice daga d'akin ta d'auro Alwala ta gabatar da tata sallar, sai da ta jima tana kwararu addu'a kana ta shafe jikin ta, nan ne ta fara cin tsanyin ni'ima na ratsa mata gab'ob'in jikin ta, a zuciyan ta handala take ta yi tana cewa" Allah mun gode maka da kayi musulmai, hak'ik'a musulunci ni'ima ne a duk lokacin da kayi sallah koh ka karanta Qur'an sai kaga duk farin ciki ta maye maka gurbin farin ciki, ba tare da ta idda zacen zucin ba nace" matsalolin ki yawa gare ta uwar d'akina kin ga tafiya ta, nan muka yi sallama na fece abuna.

bayan kwana biyar da faruwan hakan ya Abdallah bai kuma tunkaran inna Larai da maganar Aysha ba hakan ya sa ta tunanin koh yayi amfani da gargad'in da ta mishi ne akan Aysha, but a wurin shi koh kad'an gargad'in ta bai yi wani tasiri a zuciyan shi ba illah dad'a k'ara mishi k'aunar Aysha a zuciya da yayi, but he is trying to avoid it ne saboda gudun fitinar mahaifiyar shi before ya finding out solutions.
Humaimai na hango tafi to aike ma Aysha tana tafiya da y'ar laidar awara a hannun ta tana cillawa sama tana cafkewa, tana isowa daidai layin su Ilu ta hango shi a zaune a kan kujerar roba shi kad'ai ga bakin nan ya wani suntum suntum abun ma dariya ya so ya bata amma sai ta matse dariyar tayi kamar bata gan shi ba,,
yana ganin ta da sauri yayi mata nuni da kutaren hannayen shi cewa yayi ta zo, ba tare da ta biye shi ba ta ci gaba da tafiyan ta,,
saurin k'arasowa yayi gare ta yana isowa yace" ke Humayrah ba da ke nake magana ba kam kin yi biris da ni tamk'ar ba da ke nake yi ba, ina Shatu amarya ta take koh yau baki lek'a gidan su ba ne ??, ya fad'a tare da kai hannun shi kan ledar awarar tab'a tab'awa,,
saurin b'ata rai Humairah tayi tace" haba Ilu wannan wani irin abu ne hakan fisabilillahi ka kyauta kenan kana tab'a min kayan aike da wannan hannayen ka ??, ta k'are maganar tana turb'une fuska.
jan k'ak'i yayi ya fetsar kana ya fara maganar su na kutare yace" toh jaarrr uban nan dangin matsiya ta yooo ni zaki gwada ma iskan ci nawa kayan cikin laidar take ??, toh ta Allah ba taku ba na gane bakin ku d'aya da Audu bakwa son alakata da Shatu kwanan nan zan d'auke abuna kuma koh kin zo gidan bayan zamu kore ki".
wai ni kam na shiga uku dan Allah ka bar ni haka nan wannan kuturu da fitana kake ban da abunka ni ina ruwana da auren ka balle alaka ta shiga tsakanina da matarka har na zo gidan ku ??, Humayrah ta fad'a dan koh kad'an bata kawo a ranta cewa da Aysha makauniya yake nufi ba,,
tana gama fad'a tayi shigewar ta gidan su Aysha tana guni guni, tana isowa ta iske Aysha a zaune gefen ta kuwa ya Abdallah ne yana taya ta hira sama sama, duk da dai cewar Aysha d'in bata wani saki jikin ta da sh ba sosai saboda gabaki d'aya yau da zazzab'i ta taso but sai ta danne take biye shi,,
Humayrah na isowa wurin ta ta saki k'ara tace" wash Allah na yau da nayi wahala sosai gidaje biyar na shiga ban samu ba sai da na shiga gidan matar buba kana na samu",,
"Lallai kam kin yi k'ok'ari gaskiya k'anwata dubi ranar nan da ake yi amma sai da kika nemo ma auntyn ki awara", cewar ya Abdallah kenan lokacin da yake maida fuskan shi kan Humayrah,,
murmushi ta sakar mishi tace" ai dole na na nemo mata wallahi baka ga yanda ta matsa na nemo mata bane ya Abdallah shi yasa bari ma na bud'e laidar koh zaka ci kaima, ta fad'a yayin da take k'ok'arin bud'e laidar,,
a'a ni ban ci gaskiya tunda ba auntyn taki bace ta tayi min tayi da na ci, ya fad'a tare da maida mata da martanin murmushi,,
duk abubuwan da suke fad'a Aysha bata tanka musu ba illah Allah Allah da take yi humayrah ta kunce laidan awaran taci,,
Humayrah na gama kuncewa k'amshin awaran ya doke hancin Aysha da sauri ta mik'e tana k'ak'arin amai, a take kuwa amai ya fara k'ok'arin kubce mata garin lalib'o wurin da zata yi amman ne gudun kar ta shek'a musu a jiki k'usa ta cake ta zata fad'a kenan cikin zafin nama ya Abdallah ya tare ta da sauri zata kwalla k'arar azaba kenan sai ga amai ya taso mata shuuuuu kamar da bakin kwarya, lokaci guda wani irin azabebben rad'ad'i ne kafar ta ke mata,,


Ba'a fara komai ba just keep following

Share
Vote
Comment

*Sa'eeda ✍🏻*
~Y'ar mutanen Dengi~

WAYE MACUCIWhere stories live. Discover now