Page 50

657 40 0
                                    

🏵🏵☀☀🏵🏵☀☀🏵🏵
          *☀WAYE MACUCI☀*         
🏵🏵☀☀🏵🏵☀☀🏵🏵
        '''Suhaib koh Suhail'''

***********************************

® *REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS P.M.L*💭💭💭

_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_

# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
      
          
                       ©
'''Marubuciyar Rayuwar Sumayyah'''

                   *eedatou😍*

'''Follow and ✅ote me on Wattpad''': *eedatou*


*BESTORED TO MY LIL SIS* ''' SUMAYYAH MUSA DAUDA'''

      My fan my every thing, ku ci gaba da hakkuri da ni da sannu zamu iso wurin, wani abun ma sai auren Aysha da Ilu. INA mugun yin ku littafi yanzu na fara ba gudu ba ja da baya insha Allah, azumi ne kadai zai dakatar da ni da typing shi d'in ma dan ta kama ne. 

                        5⃣0⃣

  
        "Kwantar da hankalin ki hajiya matuk'ar kuka sayi maganin nan kuka yi amfani da shi yanda na prescribing muku ina tabbatar miki da cewa insha Allah yaron nan zai rabu da lalurar, amma fa ga shawara dole ne ya rage yawon tunina dan na tabbata akwai abunda ke addaban shi a cikin zuciya", cewar doctor kenan.
    Dafe kan ta tayi cike da damuwa tace" oohhh Allah !!!  ban san wata irin damuwa yaron nan ya d'ora ma kan shi ba, bari na k'irawo driver ya sayo min gaganin a chemist, a tare suka fice daga gidan yayin da doctor ya hau nuna mata hanyoyin da zata dinga bi dan a samo nasarar magance matsalar ya Abdallah, sai da ta raka shi har mota kana suka yi sallama da juna, ta k'irawo driver ta mik'o mishi takardar sallama ya amsa da sauri ya d'au mota fice daga gidan ya tafi aiken mum.
     Mum na ganin driver ya b'ace mata da gani ta k'aryo kwana ta shigo cikin gida, d'akin ya Abdallah ta nufi ta tarar yana waya, samo wuri tayi ta zauna tare da k'ure shi da ido a take yayi saurin katse wayan yace" mum har kin shigo ne"?
    Eh son ba dole ba,  ai dole ka ga na kuma dawowa dan walahi hankalina baya jikina, son ?
   Ummm mum ya fad'a yana gyara zaman shi".
   Me nene matsalar ka ?, me yake haddasa maka yawan tunani koh dai mun maka wani abun ne koh kuma sister d'in ka ka b'oye baka sanar da mu ba ?
     Jimmm yayi ya amsa yace" a'a mum, a iya zamana da ku baku tab'a b'ata min ba, kun rik'e ni da gaskiya, kun maida ni tamk'ar d'an cikin ku da kuka haifa".
    Toh me ya haddasa maka ciwon zuciya?, ta jefo mishi tambaya.
    Runtse idon shi yayi sannan ya bud'e a hankali, zuwa yanzu ya k'asa zure abunda yake ji a zuciyan shi, bata ankara ba sai gan tayi hawaye na bin fuskan shi".
      "Ya salam" ta furta da k'arfi tare da dafe k'irji tace" hawaye kuma Abdallah, please ban shirya ganin saukowan su ba please ka tsagaita zubb da su, ta k'are maganar murya a raunane kamar mai shirin yin kuka.
      Magana yake yi da murya irin ta masu stammering yace" mu......m ki min afuwa har zuwa ran.... ar da zaki san sir... rin zuciya ta, ranar da za......n da ku ko...... mai game da ni Abdal........lah".
     Ba tare da ta furta komai ba hau share mishi hawayen shi tare da lallashin shi har tayi nasarar saida hawayen dake zubowa a fuskan shi.
      A tsanyaye ta mik'e zata fice daga d'akin, har ta kai bakin k'ofa Abdallah ya dakatar da ita yace" "mu.....m", ya fad'a tare da jan maganar.
     Cakkk ta tsaya a wuri d'aya tare da jiyowa da fuska tana kallon shi, ya had'e tafukan hannayen shi biyu yace" dan Allah kar ki sanar da dad, ina so ya zama sirri tsakanina da ke".
    Nodding head d'in ta tayi lokaci guda tace" yeah, amma kuma da sharad'in zaka saki ran ka kaci gaba da walwalar ka kamar kowa".
     "Insha Allah zan yi hakan". "Good" ta fad'a tare da sakar mishi murmushi ya maida mata da martani kana ta fice daga d'akin tare da jawo mishi k'ofa.
    Yana ganin ta fice daga d'akin yaja dogon numfashi ya sauke, kana ya bi lafiyar gado ya kwanta.

         B'an garen Suhaib kuwa yana ganin Aysha da Suhail sun bar gidan,  ficewa yayi ya nufi site d'in su ya had'a kan shi da jikin bango yana ta rusa kuka, sai da yayi mai isar shi kana ya lallashi zuciyar shi ya hak'ura da kukan ya d'au car key d'in shi ya fice daga gida.
      Gidan su zee ya nufa yana sharar kwalla har ya iso cikin sa'a ya tarar da  Sumayya da zee a parlorn, tun daga bakin k'ofa ya hau rusa kuka yana cewa" ummi su mum zasu kashe ni, they will kill me ummi", kallon shi suka tsaye yi galala baki a bud'e, Sumayyah ce tayi k'arfin hali ta dafa kafadar shi tace" what's going on son ? sanar da ni komai".
     Cikin sheshshek'ar kuka ya hau bata labarin kafff abunda ya faru wanda bata sani ba, yana idda labarin ta saki killer smile tare da ciro hannun ta ta bashi baya tace" wannan k'aron ba kai kad'ai abun ta shafa ba, mu ma ya shafa tunda zee ake neman a rabata da masoyin ta k'arfi da yaji, dole mu tashi tsaye mu had'a k'arfi da k'arfe mu yake wannan fitana da take tunk'aro mu, dole ne mu raba tsakanin Aysha da Suhail matuk'ar kuna son burin ku ya cika a kan su ku mallake zab'in zuciyar ku, tana gama fad'a ta juyo da fuskan ta tana facing d'in su idon ta yayi arba da zee da idanuwan ta suka cicciko da hawaye suna neman zubewa, girgiza mata kai tayi tana cewa" zee kuka ba naki bane daga yau kin bar yin ta, kai kuma Suhaib ina so ka danne komai da ke cikin zuciyar ka, ka d'auka cewa ka samu Aysha a matsayin matar ka".
     Ba tare da ya gane inda maganar ta ya dosa ba yace" ban fahimce ki ba ummi, kina tunanin akwai wata hanya da zan bi na mallak'e Aysha?, ya jefo mata tambaya.
    Kwarai kuwa shi yafi komai sauk'i, ni na san abun yi ku zuba min ido kawai".
    "Hmmm mum ki try please, zee ta fad'a tana marairaice fuska.
     Haka suka ci gaba da maida zance tsakanin su, sun d'auk'e awanni a hakan daga bisani Suhaib ya bar gida.
    Bayan barin shi gidan ne mum tace" hanya ta zo mana cikin sauk'i da zamu rusa duk wani shirrin su Marya, Alhaji Kabeer kayi kuskure sosai da ka juya min baya amma mu jure zuwa rafi....., tana gama fad'a ta ma zee rad'a a kunne suka buga shewa tare da tafawa da junan su kamar sa'annin juna.



*eedatou ✍🏻*
      ~Y'ar mutanen Dengi~

WAYE MACUCIWhere stories live. Discover now