Part 14

724 54 2
                                    


🏵🏵☀☀🏵🏵☀☀🏵🏵
          *☀WAYE MACUCI☀*         
🏵🏵☀☀🏵🏵☀☀🏵🏵
        '''Suhaib koh Suhail'''

***********************************

® *REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS P.M.L*💭💭💭

_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_

# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
      
          
                       ©
'''Marubuciyar Rayuwar Sumayyah'''

    *SA'EEDA MUSA DAUDA😍*

'''Follow and ✅ote me on Wattpad''': *SaeedaMusaDauda*


*BESTORED TO MY LIL SIS* ''' SUMAYYAH MUSA DAUDA'''

       ~Woow Masha Allah wannan comments haka nagani kuma naji dadi Allah ya bar kauna, ina yinku over my fans wallahi yawan Ku ya sanya bana rubuta sunayen ku but before na gama novel d'innan zan ware muku pages na musamman domin nuna jin dadi na a gare ku. ~

                        1⃣4⃣

tambaya Suhaib ne ya d'oke dodon kunnen Suhail da yake cewa" where is the promised between both of us i mean the ring",,
    hantar cikin Suhail ne ya kad'a kululululuuuu fuskan shi na bayyana alamar gaskiya ya bud'e baki yace" uuhhmm uuhhmm", ya fad'a yana tsotsa keya.
      "uuhhmm what just say it out i'm all ears, Suhaib ya fad'a ba tare da ya d'auke idanuwan shi a kan d'an uwan nashi ba,,
     rasa abun fad'a Suhail yayi ya tsaya shiru kamar ruwa ya ci shi yana wuwwula ido, jin shirun yayi yawa ne Suhaib ya mik'e daga inda yake zaune ya koma cikin d'aki ba tare da sha fresh milk d'in ba,,
       yana tafiya ya sauke nannauyan ajiyan zuciya ya mik'e shima yabi bayan shi rai babu dad'i, daren ranar gabaki d'aya Suhail da tarin mafarkai ya kwana wai gashi nan yayi ido biyu da yarinyar da ya cuta.

      B'angaren Aysha kuwa tun ranar da Ilu ya ci zarafin ta bata kuma sanya shi a ido ba dan shima ba k'aramin tsorata yayi da ya Abdallah ba dan Allah ne ya kwace a hanun shi but amma har zuwa yanzu bai janye kudurin shi na mallakar Aysha a matsayin mata ba a sirrance ya bada sadakin Aysha a hannun inna Larai ba tare da sanin mahaifin ta ba.
     yammacin Asabar Aysha na zaune ita kad'ai tana tankad'e ma inna Larai, ya Abdallah ne ya shigo gidan da sallamar a bakin shi yayin da hannun shi ke rik'e da wata bak'ar laida,  ganin abunda take yi ne yasa ba shiri sallamar ta mak'ale a bakin shi da saurin shi ya nufo ta inda take yana cewa " a'a k'anwa ta yau ke ce kike tankad'e da kan ki, ina inna take ne kam ai da ta taimaka miki cuz rabin garin zubewa yake, dubi jikin ki fa fisabilillahi kaca–kaca da gari. "
      ba tare da ta ce mishi kala ba illah k'ak'alo murmushi da tayi kana ta ci gaba da aikin da take yi,,
     ganin ta k'i kula shi kuma har yanzu bata daina abunda take yi ba a dake yace" wai ni kam Aysha ba da ke nake yi ba kina ji na ina ta magana kin yi biris da ni kamar ba da ke nake yi ba ??
     "hmmm ya Abdallah me kake so na ce maka ne bayan kafi kowa sanin halin inna Larai babu ruwan ta da lalura ta ta fannin aiki idan ta tashi bata duba aiyukan da marar ido zata iy da wanda baza ta iya ba had'awa take yi ta bani kuma dole na nayi",,
     haka ne na fahimci ki amma ki dad'a k'ara hak'uri a kan wanda na san ki da shi, wata rana sai labari kin ji y'ar uwa ta"??
     insha Allah babu komai ai inna uwata ce dan haka tana da daman da zata sa nai mata duk abubuwan da ran ta yake so,,
     ba k'aramin dad'i yaji ba da jin kalaman ta dan ya tabbata cewa abunda ta fad'a ba a baki ya tsaya ba har zuciyn ta take fad'a, murnushi yayi kana yace" k'anwa ta bari na lek'a d'akin inna dan tun jiya ta aiko ayi k'ira na ban samu daman zuwa ba,,
      ba tare da ya kuma cewa komai ba yayi shigewar shi d'akin mahaifiyar shi, yana shigowa ya tarar da mahaifin Aysha na k'ok'arin fitowa daga d'akin,,
     matsawa yayi gefe guda ya bashi hanya tare da dukka wa har k'asa yace" ina yini Abba yayi kasuwa da fama da jama'a ?? "
    cikin sakin fuska Abba yace" a'a Abdullah taso mana me na wani dukkawa har k'asa sai kace wani bako taso abun ka", ya fad'a tare da rik'o hannun ya Abdallah yana k'ok'arin d'ago shi,,
       cikin nitsuwa ya Abdallahi yace" a'a Abba albarkar ku muke nema dan haka ba wani abu bane idan na duk'a na gaida da wanda matsayin uba a gare ni, sannan kuma duk d'an da bai ma mahaifan sa biyayya ba zai tab'a gamawa da duniya lafiya ba,,
     shiru Abba yayi yana yab'a nutsuwa irin ta ya Abdallah bugu da k'ari kuma yaro ne mai matuk'ar biyayya, da ace yana da lafiyayyiyar y'a da ya mallaka mishi ita amma kuma makantan Aysha shi ya kawo mishi cikaaasss,,
     

Share
Comment
Follow on wattpad

*Sa'eeda✍🏻*
~Y'ar mutanen Dengi~

WAYE MACUCIWhere stories live. Discover now