Page 28

665 51 0
                                    

🏵🏵☀☀🏵🏵☀☀🏵🏵
          *☀WAYE MACUCI☀*         
🏵🏵☀☀🏵🏵☀☀🏵🏵
        '''Suhaib koh Suhail'''

***********************************

® *REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS P.M.L*💭💭💭

_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_

# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
      
          
                       ©
'''Marubuciyar Rayuwar Sumayyah'''

    *SA'EEDA MUSA DAUDA😍*

'''Follow and ✅ote me on Wattpad''': *SaeedaMusaDauda*


*BESTORED TO MY LIL SIS* ''' SUMAYYAH MUSA DAUDA'''


                       2⃣8⃣

Ganin yanda Aysha ke rufa eyes d'in ta idanuwan ta ke neman k'afewa jiki na rawa Suhial ya shige site d'in driver ya ja motar zuwa hospital yana karanto addu'o'i a fili  yana juyowa ya tofa ma Aysha har suka iso bai daina karanto addu'o'in ba.
    Emergency direct aka nufa da ita saboda yanda jinin ke zubowa a jikin ta dan seat d'in da ta zauna a kai ma gabaki d'aya ya b'aci da jini.
     Oxygen doctors suka sa mata saboda numfashin ta da yake sama kamar zata amsa k'iran mahalicin ta kwararrun likitoci ne sun kai goma koh wannen su da irin tashi taimakon da yake bata tsabar hawala har suna had'a zufa da kyar Allah ya taimaka suka samu suka tsayar da jinin and thank Allah zuwa yanzu numfashin ta ya daidai ta ya koma nomal,,
     da yake private hospital ne na y'ay'an wane da wane d'aki guda suka ware mata sannan suka turo ta a sickbay zuwa d'akin kana doctor Munir ya fito ya sanar da su mum halin da ake ciki,,
    duk da dai hankalin su mum a tashe yake bai hana su hamdala sun nuna ma Allah godiyan su akan nasarar shawo kan matsalar Aysha da doctors suka yi ba,,
     da sauri suka bi bayan doctorn nan doctor Munir ya samu daman yi ma mum cikakken bayanin halin da ake ciki yace" we are sorry madam mun yi iya bakin k'ok'arin mu dan mu ga cewa cikin da ke jikin ta bai zube ba but unfortunately he failed to save the baby saboda wahalhalu ta patient d'in ta sha before aka kawo ta nan, sakamakon binciken mu ya nuna
mana cewa" anyi ta bugun cikin uwar ce sosai tare da tsananta mata horo hakan ya jawo unstable d'in babyn a ciki har ta kai zubewan cikin saboda cikin bai yi kwari sosai da zai iya d'aukar wahalhalu ba,,
       but Alhamdulillah mun yi nasarar ceto uwar yanzu haka alluran barci muka mata dan ta samu hutu, bayan haka kuma muna buk'atan jini laida biyu da za'a saka mata,,
    gwaron numfashi Suhaib ya sauk'e kana ya sauk'e eyes d'in shi a kan Aysha yana kallon yanda tayi shame shame a kan gado kamar wacce ta jima bata yi barci ba though dai ya san ba wani jin dad'in barcin take yi ba saboda yanda sautin numfashin ta ke fitowa da kyar saboda tsabar ta tasha a wurin sojojin nan.
     Saurin maida fuskan shi yayi a kan mum yaga hankalin ta ya tashi over a kan zubewan da cikin Aysha yayi, though shima i felt so much pain a kan hakan dan ji yake kamar some parts of him are missing saboda wani irin d'aci da zuciyan shi yake mishi, haka kawai yaji ran shi na mishi k'una mamaki sosai yayi dan shi kanshi  bai san dalili hakan ba, gefe guda tausayin yarinyar ce ya gama kama shi a take zufa ya fara k'aryo mishi babu iyaka, cikin k'arfin hali ya dube doctor Munir yace" muje ka d'ebi jini na doctor",,
    son are you sure kana da ishasshen jini da za'a d'eba a jikin ka ?, i don't want any trouble fa kar ka b'ato min wata matsalar bayan wanda nake cikin ta cuz this time around zuciya ta baza ta iya d'aukawa ba idan baza ka iya ba gara mu sai jinin nan a asubiti a sa mata kawai", mum ta fad'a dan har ga Allah she seriously mean what she said.
     Cikin taurin rai ya sakar mata murmushin da bai kai zuciya ba yace" mum kenan ta yaya hankali na zai iya kwanciya bayan na san cewa k'anwa ta na bukatar jini balle kuma ace na gaza taimakon ta ?, da kike cewa a saya jini a saka mata shin mutanen da suke bada tasu jinin da sunan taimako ake sayarwa basa son kan su ne ?, i have to give a try cuz ba zan bari k'anwata na buk'atan taimako na ba na k'i taimaka mata bayan na san da yardar Allah zan iya taimaka mata, me amfanin na kyale ta without giving a help ?, put it at the back of your mind that your son will surely make it by Allah's grace dan haka ban ga wani abun d'aga hanlali a nan ba mum. 
    Sai zuwa yanzu dotor ya samu daman yin magana yace" madam tunda yayi niyan taimaka kamata yayi bar shi, kar ki damu ai kafin ma mu d'iba jinin shi sai mun gwada blood group d'in shi  mun gani sannan mu duba idan yana da ishasshen jini before sai mu d'eba ".
    dogon numfashi mum ta sauk'e tace" its owk doctor Allah yasa ayi dace,,
    su biyun suka amsa kana suka fice daga d'akin.
    Blood lab suka tafi aka gwada jinin Suhail thank Allah babu wata matsalar da aka samu anyi aiki sucessfully an gam babu b'ata lokaci aka d'iba aka kai fridge aka replacing da wani cuz a ka'idan d'iba jini idan aka d'iba a jikin mutum ba'a sama wani directly a jikin shi dole sai an saka a fridge har sai ya kai adadin lokacin da za'a iya amfani da shi.
    A lab d'in doctor yaso ya bar shi saboda ya samu hutu amma fafur Suhail ya k'i ya bi maganar doctor, babu yanda doctor ya iya haka ya hak'ura suka nufi d'akin da aka kwantar da Aysha a hanya kuwa jiri ne ke ta d'iban Suhail yana tangal tangal kamar zai fad'i doctor yayi saurin taro shi har Allah ya taimaka suka iso.
     Isowan su ke da wuya suka tarar da mum ta gama waya da dad kenan ta shaida mishi halin da ake ciki tana katse wayan ta sai ga su sun shigo.
    Gurin da Aysha take doctor Munir nufa ya d'auko jini laida d'aya ya saka mata kana yayi sallama da su mum cikin gaggawa ya fita kan cewa zuwa anjima zai lek'o saboda he have lots of patients da suka musu operations zai musu check up.
    Bayan fitan doctor da kamar akwa uku Aysha ta fara bud'e eyes d'in ta a hankali mum ce ta fara lura da hakan da sauri tayi kan ta Suhail ma ya bi bayan ta a tare suka iso.
     Bakin ta suka gani yana motsi yana mosti tana magana ciki ciki tana cewa" bawan Allah kar ka cuce ni....... kar kayi dogaro da lalurata ka cutar da rayuwa ta..... ya Ab.........., tuni Suhaib ya ya manna bakin shi a saiting kunnen ta dan ya jiyo maganganun da take fad'a saboda daga inda yake kawai dai ya jiyo bakin ta na motsin ne yayin da yaji heart d'in shi na bugawa da k'arfi da k'arfi fatt fattt fatty kamar zai fita gefe guda b'ari na zuciyan shi ke gargad'in shi da ya koma ya zauna kar garin jiye jiye ya b'aro ma kan shi abunda zuciyan shi ba zai iya d'aukawa ba.



Please share

*Sa'eeda✍🏻*
     ~Y'ar mutanen Dengi~·

WAYE MACUCIWhere stories live. Discover now