🏵🏵☀☀🏵🏵☀☀🏵🏵
*☀WAYE MACUCI☀*
🏵🏵☀☀🏵🏵☀☀🏵🏵
'''Suhaib koh Suhail'''***********************************
® *REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS P.M.L*💭💭💭
_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_
# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
©
'''Marubuciyar Rayuwar Sumayyah'''*eedatou😍*
'''Follow and ✅ote me on Wattpad''': *eedatou*
*BESTORED TO MY LIL SIS* ''' SUMAYYAH MUSA DAUDA'''
5⃣1⃣
*Not edited*
Bayan sati biyu da faruwar hakan ummi Sumayyah ta shirya duk wata kisar ta ta nufi Dengi wurin abban Aysha ita da zee da kuma Suhaib tare da yi ma dad k'aryar cewa zata dubiyan surikar ta ce and she wants Suhaib to escort her, koh kad'an dad bai zarge wani abu game da tafiyan ba hakan yasa basu samu wata matsalar ba ya ammince musu suka d'auki hanya sai Dengi, gari mai cike da tarin albarka.
*Koh ya rayuwar su inna ta kasance bayan tafiyar Abdallah?*
Ba k'aramin tashin hankali su abban Aysha suka shiga ba na rashin ya Abdallah da suka yi ba, barin ma inna Larai da zabge ta rame ta fita hayyacin ta ta koma kalar tausayi, ga kuma Ilu da ya saka ta a gaba ya hana ta sakat da fitinar shi, in takaita muku ma kulle ya maida ta dan koh kad'an inna bata fita koh da waje ne, sanin kan ta ne muddin ta bari suka had'u da Ilu toh fa sai ya ci zarafin ta kamar yanda ya saba.
B'angaren Ilu kam har yanzu bai cire Aysha a zuciyan shi ba, kullum cikin zaman jiran ta yake ta dawo su yi aure su more rayuwar su, wannan kenan.
Yau ma kamar kullum malam na kwance a kan taburma yana shan Iska ya ga wata mota ta parking a k'usa da inda yake kwance, wanda suke motan suka firfito suka tunkaro shi, yana ganin si yayi saurin nad'e tabarmar yana murmushi tare da shigewa gida suka rufa mishi baya.
Bayan sun iso ne abban Aysha ya k'irawo inna Larai ta kawo musu ruwa suka sha, sai da suka natsa abba yace" ummin yara yau ku kad'ai kuka taho ne, ina kuka baro yaya?.
Tsotsa kai tayi cikin rashin gaskiya tace" eeeemmm yaya wallahi yanzu ma dole ce ta sa mu ka taho mu kad'ai, idan ba haka bai da tare zamu taho da yaya".
Hakane kam dan da farko na so na tambaye ki amma nace bari da ku huta tukunna".
Ummm yaya kenen dama wata muhimmiyar magana ce ta kawo mu", ta jimm tana tsotsa keya. "Cikin zak'uwa abba yace" toh toh toh Sumayyah fad'a mana yaya kika tsaya, ba dai wani abunne ya faru ba", inna kuwa sai cewa a zuciyan ta take Allah yasa ma shegiyar nan mutuwa ta yi na huta da azabar da Ilu yake d'and'ana min".
"Wallahi babu komai sai alkhairi", ta fad'a tana gyara d'aurin d'ankwalin ta tare da nuno inda Suhaib yake zaune da hannu ta d'ora da cewa" dama yaron nan ne d'an wurin yaya yake son Aysha shine nace bari na taho na fad'a maka".
Mamaki ne ya kama dad yace" ikoh Allah, toh shi yaya da yake babba ai zai iya yin komai akan maganar auren Aysha, tsaya ma tukunna, ka san fa duk abubuwan da suka faru da Aysha amma kuma kake son ta a hakan ?,
Sunkuyar da kai Suhaib yayi k'asa cike da kunya ya k'asa furta komai, ganin haka ummi Sumayyah ta gyara zama tana fuskantar dad tace" ai yaya ba sai ka tsaya tambaya ba, tunda ka ga mun tak'o k'afa takanas tun daga Jos har Dengi ka san ba wasa ce ta kawo mu ba, shi ya gani yace yana so".
Shi kuma yayan fa,? ai maganar aure bashi yihuwa ta hannun mace,".
Cike da makirci ta marairaice fuska tare da rage murya k'asa k'asa tace" ka san halin yayan namu da alkunya acewan shi ba zai iya tunkarar ka da maganar ba shi yasa yayi hakan, yanzu haka ma shi ya turo mu yace yana so ayi komai cikin kwanakin nan dan tafiyar gaggawa ce ta kama shi, ya fi son ayi komai kafin ya tafi".
Goron numfashi abba ya sauk'e tare da kallon inda inna Larai take kana ya maida kan Sumayyah yace" toh shikenan ki ce mishi duk abunda yayi dai dai ne, amma yanzu hakkin Aysha ya rataya a kan shi, a matsayin shi na uba a wurin ta ma'ana wan mahaifin ta da kuma marikin ta yana da ikon aurar da ita ma duk wanda ya so kai koh da ma ba a zuri'ar mu yake ba, balle kuma ace gudan jinin shi.
Suna jin abunda abba ya fad'a suka kanne ma juna ido tare da sakin murmushin mugunta suka hau jero ma mishi godiya.
Basu wani d'au lokaci a gidan ba suka musu sallama suka d'auki hanyar Dengi.
Bayan fitan shi ne labari ya iske Ilu game da zuwan su, tuni ya d'auki hanyar gidan malam Sa'eed, yana isowa ya ga malam na kok'arin fitowa da buta rike a hannun shi za shi masallaci.
Yana ganin Ilu ya ja burki ya tsaya tare da bin shi da kallo yana cewa" a'a Ilu yau kai ne a gidan?, lafiya koh ka taho haka gantsar gantsar da kai babu sallama, ai idan ban ci darajar mutunci ba zan ci darajar musulunci ka min sallama koh?
Shek'ewa da dariya Ilu yayi yana tafa dungun kutaren hannayen shi yace" a'a lallai ma Sa'eedu, har wani mutunci ne da koh da har za'a yi muku sallama ?,
"Ya salam" Ilu rashin kunyar taka har ta kai kazo har gabana ka k'ira ni da sunana kana min rashin kunya bayan b'ata min y'a da ka yi ? anya ka san da wanda kake magana kuwa?,
Rassss na sani da kai nake magana, ba dai Sa'idu uban Shatu ba?, munafukin da ya munafunce ni ya raba ni da Shatu indodo, toh labari ya iskoni kuma ka sani har hanzu ina kan bakata, a yanda nake jina jini a jika d'in nan koh maza dubu ne a gaba na sai na auro Indo".
Sosai ran abba ya b'ace, ba tare da ya furta komai ba ya kurb'i ruwan buta ya fetsar cike da takaici yana sauraran munanan kalaman Ilu.
"Wai hayaniyar ne nake ji a tsakar gida ?", cewar inna Larai kenan tana fad'a tare da d'aga labulen ta lek'o, tana ido hud'u da Ilu ta saki labulen da sauri ta dafe k'irjin ta tace" na shiga uku ni Larai !!!, ta fad'a tana maida numfashi, a tunanin ta cewa a zuci ta furta ashe a fili ta yi maganar dan sai da su abba suka jiyo ta,,
"Fito munafuka baki shiga uku ba tukunna sai kin jin rusa da wannan hannun mai kama da guduma a kan ki kafin ki dawo cikin hayyacin ki, ki gano cewa kin ci amanar Ilu".
Daga ciki idanun inna suka firfito saboda tsabar tsoro, ita kad'ai ta san irin azabar da take sha a wurin Ilu, bata ankara ba sai ji tafi fitsari na bin cinyoyin ta lokaci guda jikin ta ya d'au kyarma ta kama radar mazari.
Cakaall cakaal cakallll Ilu ya hau dungura k'afa zai shigo d'akin abban Aysha yace" dakata Ilu ba dai shiga d'akin matata zaka yi ba k'ato da kai ?
Tsayawa Ilu yayi ya cakkkk a wuri d'aya ya galla ma abba harara, kana ya ciro waya ya hau daddanna wa da dungun hannun shi, yana gamawa ya manna wayan a kunne ya hau yin magana, kan ya kashe wayan sai ga gardawa biyu da wasu yanmata uku da baza'a a gaza k'iran su da kadangarun bariki ba sun shigo gidan kai tsaya suka iso wurin Ilu.
Umurni ya ba ma matan yace" y'an duma duma na ku shiga d'akin nan maza ku fito min da wannan matar su cika min aiki a kan ta, ku kuma sangamaye idan kuka ga mutuminnan yana neman kawo mana cikasss ku sassare min shi gunduwa gunduwa a nan, hahahaaaaa suka saki dariyar mugunta y'an matan kuwa suka shige d'akin da aka nuno musu domin aiwatar da nufin su.
Suna shiga suka tarar da inna a halin da take ciki d'azu ga wani uban zufa da ya yanko mata, ba su yi wata wata ba suka hau jan ta da k'arfi tana turjewa, basu dire ta a koh ina ba sai a gaban Ilu.
Ilu na arba da ita ya kwashe da wani mahaukacin dariya tare lokaci guda ya mak'e murya yace" Larai me nake gani a jikin ki?
Cikin muryar kuka tace" Fitsari ne Ilu?, hahahaaa suka saki dariya su duka ban da abba da yake ji yakd gani ana wulakanta auren shi bai da halin kare ta, da kuma inna da tun ganin wannan k'artin samarin ta shiga tashin hankali mai tsanani".
Babu koh d'igon imani haka y'an matan suka kwantar da Inna Larai a k'asa, biyu suka danne ta a k'asa yayin da d'ayar ta fiddo almakaci sabuwa filll har shek'i take yi, koh tausayi babu a zuciyan tayi wurgi da d'ankwalin inna tare da finciko suman kan ta lokaci guda ta dasa almakacin ji kake kyatttttt ta datse,
Ai kuwa suka kuma b'arke da dariya wannan karon har da tafawa, inna kuma hawaye ne zub zubbb ya fara bin face d'in ta na ganin irin tozarcin da ake mata, sai da suka aske kan tasssss kana Ilu ya rusa mata uban rusa a kai wanda ta sanya Inna sakin uhu da k'arfi har sai da abba ya tsora ta amma su kam koh a jikin su, murmushin mugunta Ilu ya ma inna yace" ihu kuma surukata, ladar aski fa na ci, bari mu bar ki hakan nan sai mun kuma had'uwa wannan karon ki sani dole sai kin nemo shatu duk inda ta shiga kin kawo min ita na aura, dan haka kurum bazan zuba ido ki ci min kud'i a banza ba".
Yana gama fad'a ya wuce fuuuuuuu mutanen shi suka rufa mishi baya suna hura mishi kai.
B'angaren Aysha da masoyin nata kuwa sai soyewan su suke hankali a kwance ba tare da tunanin wani abu ba, a cikin kwanakin shi ke kai ta makaranta ya d'auko ta, wani sa'in ma idan bai da abun yi haka zai zauna ya jira ta a mota har su taso kafin ya maida ta gida.
Sosai ya saba da su tee saboda irin kusancin da suke da shi da Aysha, kuma ya yaba da halayen su matuk'a.
Duk zuwan da Suhail yake makarantar su Aysha basu tab'a had'uwa da d'an uwan tee Abdallah ba, koh yaushe cikin sab'a ni suke, shima dai Abdallan tun ganin da ya ma yarinyar da ta fama mishi mik'in da ke fame a cikin zuciyan shi bai kuma had'uwa da yarinyar ba, amma a koh da yaushe tunanin ta na mak'ale a k'asan zuciyar shi ya hana shi sakat.
Da farko tee ta fahimci kamar yayan nata na cikin damuwa amma ta yi juyin duniya ya fad'a mata matsalar shi ya k'iya.
Yammacin ranar talata Aysha na hango a kitchen ita da jummai suna shirya abincin dan mum da kan ta ta sa jummai ta kowa mata girki but na gargajiya da na zamani,,
Suna cikin girkin ne Suhaib ya lek'o kitchen d'in dan bama jummai aikin fruit salat da yake so ta had'a mishi, yana ganin Aysha a ciki ya jingina a jikin k'ofan d'akin ya hau bin ta da mayatattun kallo, jiyowan ta kenan idon ta ya sauk'a a kan nashi, fitinannen murmushi ya sakar mata yace" my one ashe kina kitchen"?
Waino mishi eyes balls d'in ta tayi tare da kashe mishi ido d'aya tace" Yeah babyna gara na koya girki tun kafin kazo kana cewa ban iya girki ba".
lumshe mayatattun shanyayyun idanuwan shi yayi yace" woow babyna keep trying one day you are gonna be a good cook, ummm you know what?, ya jefo mata tambaya.
Nop i'm all ears, ta fad'a a lokacin da take d'ora ruwan zafi gas cooker,
I'm eager a yi abunnan, i don't why those days gabana na yawaita fad'uwa, ji nake like something else is gonna happen".
Maganar shi yayi daidai da lokacin da ta gama d'ora pot d'in a kan gas ta juyo tana fuskantar shi, tare da nodding head d'in ta lokaci guda tace" ooohhh no, it couldn't happen by the will of Allah, I pray that Allah stop all bad thing that will depart us".
Lumshe ido yayi yace" hope so dear, ki preparing min fruit salat ki kawo min site d'in mu", Owk durling me, tana amsa mishi yayi saurin barin wurin ta bi bayan shi da kallo, tana ganin ya b'ace mata da gani ta sauk'e nannauyan ajiyan zuciya kana taci gaba da abunda take yi.
Bayan tafiyar shi ne jummai ta tsaya da abunda take yi tace" gaskiya Aysha kun dace sosai da Suhail, wani sa'in idan na gan ku a tare ji nake da ma nice na samu saurayi mai hali kamar na Suhail da naji dad'i.
Murmushi Aysha ta sakar mata tare da d'auko fruits d'in ta fara sliding d'in su kana tace" Jummai kenan you are so funny, tabbas abubuwa sun faru tsakanina da Suhail har ya d'arsa min tsanar shi a zuciya ta, amma zuwa yanzu na zauna nayi tunani na gano *Waye Macuci*, na mance da duk wani abunda ya faru da ni a baya na rungumi abuna, cuz k'addara ce da ta riga da ta afku, koh da ace tana tunkaro mu ne, babu wanda ya isa ya canja face Allah (SWA)·
Ban fahimce ki ba Aysha, wata irin k'addarar kike nufi ?, bayan na san Suhail bai tab'a cutar da ke ba sai dai Suhaib?,
Uhhhmmm Jummai ba za ki gane ba mu bar maganan haka nan, kin ga tunda na gama had'a fruit salat d'in nan bari nayi maza maza na kai mishi idan mum ta lek'o kice mata ina site d'in su Suhail, tana gama fad'a ta fice daga kitchen d'in da sauri ta nufi site d'in su Suhail.*eedatou✍🏻*
~Y'ar mutanen Dengi~
YOU ARE READING
WAYE MACUCI
Historical FictionLabari ne a kan wata mak'auniyar Allah mai suna Aysha wacce take soyayya da yayan ta amma kwatsam sai wata tsautsayi ya afka mata har hakan ya saka ta cikin bakin ciki,ba tare da ta bayyana mishi ba sai daga baya ya fahimci halin da take ciki a tsan...